Gwamnoni bakwai da suka faɗi zaɓen sanata a jihohinsu

Zaɓen Najeriya na shekarar 2023 ya zo da abubuwa na ban mamaki, musamman nasarar da wasu 'yan takarar majalisun dokoki na tarayya suka samu.
Tuni dai sakamakon kusan duka kujerun majalisun dokokin ya bayyana inda ya zo wa wasu gwamnoni da sammatsi
Gwamnonin wasu jihohi musamman waɗanda suke kammala wa'adin mulkinsu na biyu, inda da yawa suka nemi kujerun majalisun dattawan ƙasar.
Sai dai yayin da wasu daga cikinsu suka samu nasara, wasu faɗuwa zaɓen suka yi.
Ga jerin wasu daga cikin gwamnonin ƙasar bakwai da suka sha kaye a jihohinsu.
Atiku Bagudu

Gwamnan jihar Kebbi da ke arewa maso yammacin Najeriya, kuma shugaban ƙungiyar gwamnonin jam'iyyar APC mai mulkin ƙasar, ya sha kaye a hannun tsohon gwamnan jihar Sanata Adamu Aliero na jam'iyyar PDP.
Wannan ne wa'adin gwamnan na biyu kuma na ƙarshe a matsayin gwamnan jihar da ya hau mulki a 2015, inda ya tsaya takarar kujerar sanata mai wakiltar Kebbi ta tsakiya.
INEC ta ayyana Sanata Adamu Aliero a matsayin wanda ya yi nasara da ƙuri'u 126,588, inda shi kuwa Bagudu ya samu ƙuri'a 92,389.
Simon Lalong

Asalin hoton, MAKUT SIMON MACHAM
Gwamnan Jihar Plateau da ke arewa ta tsakiya ya gaza samun nasara a yunƙurinsa na zama sanatan Plateau ta Kudu.
Mista Lalong na APC, ya yi rashin nasara ne a hannun abokin takararsa AVM Bali Ninkap Napoleon mai ritaya na jam'iyyar PDP.
Gwamnan Lalong wanda ya riƙe muƙamin gwamnan jihar har sau biyu shi ne babban daraktan yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam'iyyar APC.
Samuel Ortom

Asalin hoton, FACEBOOK/SAMUEL ORTOM
Gwamnan Jihar Benue da ke arewa ta tsakiyar Najeriya ya tsaya takarar kujerar sanatan Benue ta Arewa maso yamma.
Gwamnan na daga cikin gwamnoni biyar na jam'iyyar PDP da ke nuna hamayya mai tsanani ga shugabancin jam'iyyar tasu, inda suka kafa ƙungiyar gwamnonin PDP biyar da suka yi wa laƙabi da 'G-5 Governors'.
Mista Ortom ya yi rashin nasara a hannun abokin takararsa na jam'iyyar APC Titus Zam, wanda tsohon jami'in gwamnatin Ortom ɗin ne.
Darius Ishaku

Asalin hoton, DARIUS ISHAKU
Gwamnan jihar Taraba da ke arewa maso gabashin Najeriya, Darius Ishaku, ya sha kaye a takarar kujerar sanatan Taraba ta Kudu.
Darius Ishaku ya shafe shekara takwas yana kan kujerar gwamnan jihar a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar PDP.
Ɗan takarar jam'iyyar APC David Jimkuta ne ya yi nasara bayan samun kuri'u 85,415 kamar yadda INEC ta bayyana.
Ben Ayade

Asalin hoton, BEN AYADE/FACEBOOK
Gwamnan Jihar Cross River da ke kudu maso kudancin Najeriya Ben Ayade ya yi rashin nasara a ƙoƙarinsu na zama sanatan Cross River ta arewa.
Mista Ayade wanda ke kammala wa'adin mulkinsa na biyu na gwamnan jihar ya taɓa zama sanata tsakanin shekarar 2011 zuwa 2015.
Gwamna Ayade - wanda a shekarar 2011 ya ci kujerar sanata a jam'iyyar PDP, sannan ya ci kujerar gwamna har sau biyu a jam'iyyar ta PDP - ya koma jam'iyyar APC a shekarar 2021, inda ya yi takarar sanatan a yanzu.
To sai dai ya sha kaye a hannun abokin takatarsa na jam'iyyar PDP Agom-Jarigbe.
Ifeanyi Ugwuanyi

Asalin hoton, ENUGU STATE GOVERNMENT
Gwamna Ifeanyi Ugwuanyi na Jihar Enugu da ke kudu maso gabashin Najeriya ya yi rashin nasara a ƙoƙarinsa na zama sanatan Enugu ta Arewa a majalisar dattawan ƙasar.
Mista Ugwuanyi wanda ke shekararsa ta takwas kuma a wa'adinsa na ƙarshe a matsayin gwamnan jihar a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar PDP, ya sha kaye a hannun abokin takararsa na jam'iyyar LP.
INEC ta bayyana Okechukwu Ezea na jam'iyyar LP a matsayin wanda ya ci takarar kujerar.
Okezie Ikpeazu

Asalin hoton, OKEZIE IKPEZU
Shi ma gwamnan Jihar Abia ta yankin kudu maso gabashin Najeriya, Okezie Ikpeazu na jam'iyyar PDP, wanda ke kammala wa'adin mulkin jihar karo na biyu, kuma ya nemi tafiya majalisar dattawa, ya sha ƙasa.
Gwamnan ya nemi wakiltar mazaɓar kujerar ɗan Majalisar Dattawa ta Abia ta Kudu amma ya sha kaye a wannan buri nasa a hannun Enyinnaya Abaribe na jam'iyyar APGA.










