Abin da ke janyo rashin haihuwa ga maza da kuma yadda za a magance shi

Rashin haihuwa na wasu maza babban abin damuwa ne tsakanin ma’aurata kuma wannan na daya daga cikin abubuwa da ke janyo rabuwar aure.

Matsalar rashin lafiya da wasu maza ke fuskanta na daga cikin ababe da ke sanya su kasa yi wa matansu ciki bayan an yi aure.

Matsalar rashin haihuwa ga maza ce ke sanya wasu matan aure fita waje domin yin mu’amala da wasu mazajen har ciki ya shiga, inda kamar yadda masana ke cewa a wasu lokuta za su iya daukar yaron wani su kawo wa mazasu a matsayin shi ya haifa domin tseratar da aurensu.

Daukar ‘ya’yan wasu da mata ke yi domin kakaba wa mazansu a matsayin ‘ya’yansu na daga cikin abubuwa da ake yawan tattaunawa a Najeriya a baya bayan-nan, inda mutane da dama da suka fadawa ibtila’in ke kare rayuwarsu cikin kunci.

BBC ta jiyo ta bakin wasu masana kiwon lafiya don sanin abin da ke janyo rashin haihuwa tsakanin wasu maza da kuma hanyar magance matsalar.

Mene ne rashin haihuwa na maza?

Rashin haihuwa na maza cuta ce ta haihuwa da ke sanya namijin kasa yi wa matarsa ciki.

A cewar Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO, rashin haihuwa matsala ce da ke shafar miliyoyin mutane a duniya da suka kai shekarun haihuwa, hakan kuma na da tasiri ga iyalai da kuma al’ummomi.

WHO ta ce an kiyasta cewa ma’aurata tsakanin miliyan 48 zuwa 186 na fama da rashin haihuwa a fadin duniya.

Hukumar Lafiya ta Duniya ta kuma ce na da matakai, inda akwai karamin mataki da kuma babba.

Karamin matakin na rashin haihuwa shi ne mutumin da bai taba bawa mace ciki ba sannan babban matakin kuma shi ne mutumin da ya taba bawa mace ciki.

Me ke janyo rashin haihuwa ga maza?

Wani likitan al’aurar maza a Najeriya, Dr Adebayo Bamisebi ya fada wa BBC Pidgin cewa manyan abubuwan da ke janyo rashin haihuwa na wasu mazaje shi ne ƙarancin fitar maniyyi da maniyyi da ya lalace da kuma idan maniyyin namiji ya yi ƙaranci da ba zai kai gamsar da mace ba.

Likitan ya ce idan ma’aurata suka kasance suna saduwa sannan har bayan wata shida ko shekara daya babu ciki, to akwai alamun cewa daya daga cikinsu na da mastala.

Dr Bamisebi ya ce idan gwajin haihuwa ya nuna cewa adadin maniyyi ya yi kasa miliyan 15, hakan ke nuna cewa mijin na da matsala.

Likitan na Najeriyaya kuma ce akwai wasu abubuwa da ke janyo rashin haihuwan tsakanin maza kuma sun hada da sauye-sauyen salon rayuwa da cututtuka da sauransu.

Ya ce daya cikin bakwai na ma’aurata na basa haihuwa kuma rabin su maza ne ke da matsalar.

Idan aka zo batun sauye-sauyen salon rayuwa, Dr Bamisebi ya ce yawan amfani da kwayoyi ba bisa ka’ida ba na cikin ababe da ke haifar da rashin haihuwa ga maza.

Likitan ya kuma ce zama na tsawon sa’o’i ko sanya matsassun kamfai na haifar da rashin haihuwa ga maza, ya kuma shawarci mazan da su rika tabbatar da cewa sun guji irin wannan salon rayuwa.

Dr Bamisebi ya ce shan taba da kuma barasa fiye da kima shi ma yana janyo rashin haihuwa tsakanin maza.

Likitan ya kara da cewa cin abinci da ba ta dace ba na daga cikin matsalolin, inda ya shawarci maza da su rika cin lafiyayyen abinci mai gina jiki.

‘Duk abin da za mu ci, mu ci lafiyayyen abinci,’’ in ji likitan.

WHO ta ce abin da ya fi haifar da rashin haihuwa na maza shi ne rashin fita da kuma maniyyi mai kyau da kwayoyin halitta da sauransu.

Wani likita dan Najeriya, Dr Seraph Obasohan ya ce yawan shan barasa da kuma shan sigari da tabar wiwi su ne abubuwa da suka fi janyo rashin haihuwa tsakanin ga maza da mutane ba su sani ba.

Ya kuma ce saka matsassun tufafi wani dalili ne da ke janyo rashin haihuwa saboda yana kara zafin jiki a al’aurar maza wanda ke shafar maniyyi.

Dr Obasohan ya ce wasu magunguna da ake amfani da su don ciwon ciki da ciwon zuciya suna da illa da kuma ke shafar rashin haihuwa ga maza.

‘Akwai wasu mutane da aka haifa da kwayoyin halitta wadanda ba za su iya samar da maniyyi ba.

Akwai wani yanayi da namiji zai girma amma sai a samu gwaje-gwaje da ake masa basa aiki yadda ya kamata, wanda hakan kan janyo rashin haihuwa ga namiji,’’ in ji likitan.

Dr Obasohan ya kuma ce mutane da aka haifa da wasu kwayoyin halitta kamar karamin mazakuta da rashin girma da wuri na daga cikin abubuwa da ke sanya wasu maza basa haihuwa.

Ya ce mazan da ke da ke fama da rashin karfin mazakutarsu da kuma na fitar da maniyyi suma suna cikin wadanda ke da matsalar rashin haihuwa.

Dr Obasohan ya kara da cewa maniyyin namiji sai ya hadu da na mace kafin ake samun kwayaye, sai dai wasu maza da ke fama da rashin karfin mazakuta su kan fitar da maniyyi da wuri wanda ba zai kai ga mace ba da har zai sa ta dauki ciki.

Har ila yau, Likitan ya ce kamuwa da wasu cutuka da ake dauka yayin saduwa suma su kan kawo wa maza matsala da kuma zai kai ga rashin haihuwa.

Abin da za ku yi domin magance matsalar rashin haihuwa?

Dr Bamisebi ya ce hanyar magance rashin haihuwa na sun bambanta saboda rashin lafiya da kuma cewa magance matsalar ya dogara ne kan bincike.

Ya ce ana maganin matsalar ne bisa ga abin da likita ya gano cewa shi ne ya haddasa matsalar.

Likitan ya ce da zarar likita ya gano dalilin rashin haihuwa da namiji ke tattaré da shi, to za a iya magance matsalar.

Dr Bamisebi ya kuma ce wasu matsaloli na rashin haihuwar namiji kan kai ga yin tiyata wasu kuma kan samu warkewa ta hanyar shan magani.

Ya ce ya kamata maza su guji daukar abu mai nauyi da kuma tabbatar da cewa sun ci abinci mai gina jiki da zai inganta haihuwa.

‘Har ila yau, cin abincin da ke samar da Vitamin C da Vitamin D da kuma Zinc na taimakawa wajen kara maniyyi.’’ in ji Dr Bamisebi.

A daya bangaren, Dr Obasohan ya ce idan naimji mai fama da lalurar rashin haihuwa ya kasance kuma yana shan taba ko kuma barasa, to ya kamata su daina domin samawa kansu lafiya da kuma magance matsalar.

Likitan ya ce duk namijin da ke da matsalar rashin haihuwa ya kuma kasance mai sanya matsassun kamfai, ya kamata su tabbata cewa suna sanya kayan da ba zai matse su ba.

Likitan ya kuma ce maza su rika cin abinci mai gina jiki da kuma ‘ya’yan itatuwa don taimaka musu samun haihuwa.