Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Amurka ta amince Denmark da Netherlands su bai wa Ukraine jiragen yaƙi
Amurka ta amince Denmark da Netherland su aike da jiragen yaƙi kirar F-16 da ta ƙera zuwa Ukraine, bayan matuƙan jirgin Ukraine sun gama samun horon yadda za su tuƙa jiragen.
“Ta haka Ukraine zai ta iya amfani da sabon ƙarfin da za ta samu,” in ji kakakin Ma’aikatar harkokin wajen Amurka.
Ukraine ta ji daɗin wannan mataki wanda ta yi ta neman a ɗauka tun bara.
Amma zai ɗauki watanni kafin Kyiv ta iya samu damar amfani da jiragen F-16 domin harin ramuwa kan dakarun Rasha masu ƙarfi.
Netherland na da irin waɗan nan jirage ƙirar F-16, 24 da suke aiki yanzu amma ta yi shirn rabuwa da su domin ta maye gurbinsu da sabbin jiragen yaƙi na zamani.
Ita kuma Denmark na shirin kara yawan jiragen ruwanta suka 30 kamar dai F-16 da take su.
Tun da fari Amurka da ƙawayenta sai da suka yanke shawarar ka da a baiwa Ukraine waɗan nan jirage ƙirar F-16, domin fargabar ka da yaƙin ya kai matakin da Rasha za ta yi amfani da nukiliyarta kan Ukraine.
Rasha wadda ta fara mamayarta a Ukraine a watan Fabirairun 2022 – ba ta ce komai ba har yanzu kan wannan mataki.
Duka ƙasashen Denmark da Netherland sun samu shalewar hakan a hukumance, domin kai waɗan nan jiragen yaƙi, kamar yadda kakin ma’aikatar harkokin wajen na Amurka ya bayyana.
Kakaki ya ƙara da cewa za a fara wannan shiri ne “da zarar rukunin farko na matuƙa jirgin sun kammala samun horo”.
Ministan harkokin wajen Netherland ya yi maraba da wannan mataki na Amurka, yana cewa, “wannan wani mataki ne da zai sa Ukraine ta kare mutanenta da ƙasarta”.
“Yanzu za mu ƙara tattauna batun da sauran ƙawayenmu na Tarayyar Turai,” kamar yadda ya wallafa a shafinsa na X, wanda aka fi sani da Twitter.
Shi ma Ministan Harkokin Tsaron Denmark Jakob ƙara kambama kalamsa ya yi.
“Gwamnati ta sha maimaita cewa taimakon ne abu na gaba bayan bai wa matuƙa jiragen horo. Muna tattauna batun da ƙawayenmu na kusa,” ya gaya wa kamfanin dillancin labarai na Denmarka.
A can kuma Ukraine, Ministan harkokin tsaron ƙasar Olesksii Reznikov ya bayyana wannan mataki na Amurka a matsayin “babban labari”.
“Sojojinmu sun tabbatar da cewa mutane ne masu saurin koyar abubuwa cikin ƙanƙanin lokaci. Kwanan nan za mu nuna cewa ba mai hana Ukraine samun nasara.
Muna godiya ga dukkan abokan hulɗarmu da abokanmu da ke Amurka, Netherland da kuma Denmark baki ɗaya. Muna kan turbar nasara!” ya rubuta a X.
A karshen wannan watan ake sa ran duka ƙawayen Ukraine 11 na Yamma za su fara horas da matuƙa jiragen Ukraine da za su shirya zuwa shekara mai zuwa.
A farkon wannan makon kakakin sojin saman Ukraine ya ce Kyiv ba za ta iya tuƙa jiragen yakin na F-16 ba a wannan lokacin.
Nau’in jirgin saman F-16 an yi amannar yana ɗaya daga cikin jiragen yaƙin da ake godara da su babu kokonto.
Yanayin ƙarfin saitin F-16 zai bai wa Ukraine damar kai hari kan dakarun Rasha a ko wanne irin yanayi ko da daddare ne ba tare da gaza samun abin da ake so ba.
Ukraine na da jirage masu yawa ƙirar MiGs – amma duka an yi su ne tun lokacin tarayyar Soviet, kuma a yanzu haka Rasha na yi wa ƙasar fata-fata a sama.
Akwai buƙatar Kyiv ta koyi sabbin dabarun yaƙi na zamani domin ta kare samaniyarta daga hare-haren makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa – ko ta ƙarfafa hare-haren ramuwar da take yi a kudu da gabashin ƙasar.