Mijin matar da ke kiran maza su yi mata fyaɗe zai zaman shekara 20 a gidan yari

Asalin hoton, Getty Images
Alkalai a Faransa sun samu Dominique Pelicot, ɗan shekara 72, da laifi mai girman gaske na haddasa yi wa tsohuwar matarsa Gisele fyade, inda aka yanke masa hukuncin zaman gidan yari na tsawon shekara 20 bayan shafe makonni 16 a na shari'ah.
Ya shafe shekara 10 yana shirya yadda ake yi wa matar tasa fyaɗe, inda ya gayyato gwamman mutane baƙi su yi mata fyaɗe bayan sun sanya ta fita daga hayyacinta.
An kuma yanke wa maza hamsin hukunci tare da shi, tsakanin shekaru uku zuwa 15.
Da take Magana bayan an sanar da hukuncin, lauyar da ke kare Dominique Pelicot Beatrice Zavarro, ta ce wanda take karewar na duba yiwuwar ko zai ɗaukaka kara a game da hukuncin.
"Kotun ta yanke hukunci akan Dominique inda aka yanke masa hukuncin zaman gidan yari na shekara 20 ,amma zaiyi zaman kashi biyu bisa uku na shekarun da aka yanke yi masa a gidan yarin. Mr Pelicot ya karbi hukuncin amma kuma ta ce za su yi amfani da damarsu ta duba yiwuwar ɗaukaka kara a cikin kwanaki 10." In ji Beatrice.
A nata ɓangaren, Ms Pelicot ta godewa dukkan waɗanda suka ba ta goyon baya har aka kawo ga yanke hukuncin ciki har da iyalanta inda ta ce tana magana ne yau a cikin wani yanayi na juyayi.
"Wannan hukunci ne mai wuyar gaske to amma a yanzu abinda za ta fara tunawa shi ne ƴaƴanta uku da kuma jikokina saboda a dalilinsu ne ta yi wannan yaƙi har ta kai ga yanke wannan hukunci na yau". In ji Gisele.
Daga ƙarshe Ms Pelicot ta gode wa lauyoyinta inda ta ce sun yi rawar gani wajen ganin an ƙwatar mata hakkinta.
"Ba ta da na sanin wannan shari'a kuma tayi hakan ne saboda ya zama darasi ga ƴan baya."
Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito ɗaya daga cikin iyalan Pelicot na cewa abun takaici ne shekarun da aka yanke musu saboda ya yi kaɗan.
Bayan fitowarta daga kotun, waɗanda aka taɓa yi wa fyaɗe daga faɗin duniya sun fara aika mata da saƙonnin goyon baya da nuna ƙauna.
Martanin shugabannin duniya kan jajircewar Gisele
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A saƙon da ya aika wa Gisèle, shugaban Jamus Olaf Scholz ya ce: ''kin sauya daga ɓoye kanki kika bayyana kanki kuma kika yi yaƙi domin neman adalci. Kin bai wa mata a faɗin duniya murya mai ƙarfi. A ko da yaushe, kunya na tare da mai laifi. Mun gode Gisele Pelicot.''
Shi ma Firaministan Sipaniya Pedro Sanchez ya aike mata da saƙo ta shafinsa na X, yana cewa: ''irin wannan kare mutunci. Mungode Gisele Pelicot. Yanzu ƙunya zata sauya ɓangare.''
Ƴan siyaysa a Faransa sun fara tofa albarkacin bakinsu kan hukuncin a shafukan sada zumunta.
Wata ƴar majalisa a Faransa Marie Lebec ta ce '' ina girmama wannan matar saboda ƙarfin zuciyar ta. Ina fata idan aka ɗauke ta a matsayin misali, za mu fi iya kare mata daga cin zafari.''
Shi kuwa Manuel Bompard cewa yake yi, '' wannan shari'ar ta fyaɗe za ta shiga cikin tarihi. Za ta kasance wani muhimmin al'amari da zai sauya akalar yadda ake yaƙi da yi wa mata fyaɗe wanda ke ci wa alumma tuwo a ƙwarya".
Hukuncin shari'ar ya kuma fara jan hankalin shugabanni a faɗin duniya.











