Tauraron fim Arnold Schwarzenegger na jagorantar taron sauyin yanayi

 Arnold Schwarzenegger

Fitaccen tauraron fim din Amurka kuma dan siyasa, tsohon gwamnan jihar California Arnold Schwarzenegger yana gudanar da taronsa na shekara-shekara a kan sauyin yanayi.

Taken taron na bana a babban birnin Australia, Vienna, shi ne alakar da ke tsakanin kare yanayi da kuma tsaro.

A kalamansa Mista Schwarzenegger, ya ce idan duniya ta hada kai to za ta iya kawar da matsalar gurbatar yanayi, ta kuma gina makoma mai kyau da tsafta ga al’umma da za ta zo a nan gaba.

Ya ce yanzu lokaci ya yi da kowa zai daina maganar abin da zai rasa, maimakon haka duniya ta mayar da hankali a kan hanyoyin samun mafita wadanda ya ce tuni akwai su, da kuma abin da mutane za su cimma.

Tattaunawa a kan sauyin yanayin Ukraine da ke fama da yaki na daga cikin abubuwan da za a yi a taron.

Baya ga ‘yan siyasa taron zai kuma kunshi manyan shugabannin harkokin kasuwanci da matasa.

Arnold Schwarzenegger ya zama jigo a fafutukar samar da iska mai tsafta da amfani da makamashi maras gurbata muhalli ko dumama yanayi tun a lokacin da yake gwamnan jihar California a tsakanin shekara ta 2003 da 2011.

Kuma tun bayan da ya bar mulki yake amfani da matsayinsa na tauraro da kuma tasirinsa wajen yada manufofi na rage hayaki mai gurbata muhalli musamman da shirinsa da ya yi wa lakabi da Schwarzenegger Climate Initiative.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Haka kuma yana fafutukar ganin mutane sun rungumi tsarin sauyin yanayin rayuwarsu ta yadda hakan zai iya taimaka wa wannan fafutuka da kuma lafiyar su kansa.

Yakan bayar da misalin yadda ya rage cin nama ya karkata ga kayan lambu da sauran kayan abinci dangin ganye, tare da nuna yadda ya ce lafiyarsa ta inganta a sanadiyyar hakan.

Mista Schwarzenegger ya kuma yi amanna fasaha na tasiri wajen cimma buri na yaki da matsalolin sauyin yanayi.

Ya bayar da misalin wata katuwar motarsa ta musamman kirar homa jip (Hummer) mai manya-manyan tayoyi, kama da ta sojoji, wadda yake sauya aikinta daga mai amfani da man gas na dizil zuwa mai amfani da batir, inda ya ce idan ya mayar da ita kan aiki da lantarkin ta fi karfi da kuma gudu.

A wata hira da ya taba yi da BBC tauraron fim din ya ce rage hayaki mai gurbata muhalli zai taimaka wa kasashe da tattalin arzikin duniya.

Ya ce shugabannin da suke ikirarin cewa yaki da sauyin yanayi na cutar da tattalin arziki sakarkaru ne ko makaryata.

Ko kuma ba su san yadda ya kamata su bullo wa lamarin ba, domin a cewarsa su sun gano yadda za a yi hakan, kawai abu ne na kuduri da zuciyar yin hakan.