Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Martinelli zai bar Arsenal, Casemiro zai ci gaba da zama a United
Kofar Manchester United a bude take, don ba wa mai tsaron ragarta Andre Onana damar komawa Saudiyya, Bayer Leverkusen da Fenerbahce na duba yiwuwar nada Ange Postecoglou a matsayin koci, sannan farashin da Arsenal ta sanya kan Gabriel Martinelli ya sa kungiyoyi sun kasa nemansa.
Manchester United na iya barin golan Kamaru Andre Onana, mai shekara 29, ya koma Saudi Arabiya a kasuwar musayar 'yan wasa ta Pro League. (Teamtalk)
Dan wasan tsakiya na Brazil Casemiro, mai shekara 33, ya zabi ya ci gaba da zama a Manchester United maimakon komawa Al-Nassr domin taimaka masa da damar buga gasar cin kofin duniya ta 2026. (Goal)
Tsohon kocin Tottenham Ange Postecoglou na daya daga cikin 'yan takarar da ake tunanin za su karbi ragamar horar da Bayer Leverkusen bayan korar Erik ten Hag. (Sky Sports Germany)
Kulob din Fenerbahce na Turkiyya, wanda kwanan nan ya sallami Jose Mourinho, zai iya zama zabi ga Postecoglou, mai shekaru 60, wanda ya jagoranci Spurs zuwa ga nasara a gasar cin kofin Turai a bara kafin a kore shi. (Fabrizio Romano)
Dan wasan Brazil Antony, mai shekara 25, ya ce ya tattauna da Bayern Munich kafin ya kammala komawa Real Betis daga Manchester United, inda ya yi zaman aro a bara. (El Partidazo)
A shirye Arsenal take ta siyar da dan wasan gaban Brazil Gabriel Martinelli, mai shekara 24, a farkon bazara, amma farashin fam miliyan 60 da suka nema ya sa kungiyoyi dari dari, ko da yake wasu sun taya shi a kan £40m. (Mail)
Juventus ta dade tana kokarin daukar dan wasan gaban Faransa Randal Kolo Muani, mai shekara 26, daga Paris St-Germain tsawon watanni amma Tottenham ta kulla yarjejeniya da shi. (Gazzetta dello Sport)
Haryanzu Manchester United na sha'awar karfafa zabin tsakiyarta amma darektan kwallon kafa Jason Wilcox baya ganin hakan a matsayin babban fifiko. (Sky Sports)
Arsenal da Barcelona duk suna nuna sha'awarsu akan dan wasan baya na Nottingham Forest dan kasar Brazil Murillo mai shekaru 23. (Caughtoffside)
Tsohon kocin Wolves Gary O'Neil baya gaggawar komawa aiki amma yana jiran damar da ta dace bayan ya yi magana da wasu kungiyoyi bayan ya bar Molineux (Telegraph)