Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Man United ta haƙura da Martinez, Liverpool ta ƙi yarda Gomez ya koma AC Milan
Manchester United ta hakura da neman golan Aston Villa Emiliano Martinez, Liverpool ta yanke shawarar kin sayar da Joe Gomez duk da tayin da AC Milan ta yi masa yayin da Chelsea ke ganin Sterling zai yi kwantai.
Aston Villa ba ta samu wani tayi daga Manchester United ba, kan golanta dan Argentina Emiliano Martinez duk da cewa ana alakanta dan wasan mai shekaru 32 da komawa Old Trafford. (Sky Sports)
Manchester United dai ta yanke shawarar kin zawarcin Martinez ne saboda shekarunsa da zunzurutun albashinsa na fan 200,000 a mako. (Mirror)
Martinez dai ba ya sha'awar komawa Galatasaray duk da rahotanni daga Turkiyya na cewa kungiya ta masa tayin fam miliyan 21.6. (Daily Mail)
Liverpool ta ki yarda Joe Gomez, mai shekara 28, ya koma AC Milan bayan yunkurin da suka yi na sayen dan wasan bayan Ingila Marc Guehi, mai shekara 25, daga Crystal Palace ya ci tura. (Fabrizio Romano)
Bayern Munich na son dauko dan wasan Najeriya Ademola Lookman, mai shekara 27, daga Atalanta a ranar karshe. (Sky Sports)
Da alama dan wasan gaba na Chelsea Raheem Sterling na shirin ci gaba da zama a Stamford Bridge, duba da cewa ba wata kungiya da ta neme shi daga Turkiyya, da Saudiyya da Amurka, ga shi kuma an kusa rufe kasuwanninsu (The Athletic)
Crystal Palace ta janye daga yarjejeniyar aro da Tottenham kan dan wasan Isra'ila Manor Solomon, mai shekara 26, duk da yarjejeniyar da ta ba su damar karin lokaci don kammala cinikin. (Sky Sports)