Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Cin amana uku da suka sauya tarihi a duniya
Tarihi na ɗauke da labarin maciya amana da masu goyon baya da kuma 'yan ba ruwanmu.
A lokuta da dama cin amana na kawo sauyi cikin wasu tsare-tsare.
BBC ta kawo misalin irin waɗannan cin amana: Daya daga ciki ne ya yi sanadiyyar hamɓarar da mulkin wani babban sarki.
Akwai kuma cin amanar da ya yi sanadin kashe wani fitattacen jagoran al'ummar Rum.
Yayin da cin amana na uku ya bayar da gudummawa waje samun nasara a yaƙin Birtaniya da Amurka.
Julius Caesar: Taka-tsantsan da makusanta
Cin amanar da aka yi wa Julius Ceaser ranar 15 ga watan Maris shekara ta 44 kafin haihuwar Annabi Isa (A.S) ta sauya tsarin Rum.
Jinjina ga marubuci William Shakespear wanda ya yi amfani da kalmar 'Beware of The Ideas of March' watau ka yi taka-tsantsan da mutanen da ke kusa da kai.
Abinda ha kan ya ke nufi shi ne ranar 74 a kalandar Rum ita ce dai dai da ranar 15 ga watan Maris kuma ranar da aka ci amanar Julius Ceaser.
Julius Ceaser ya kasance Janar na Soja kuma mai faɗa aji a ƙasar Rum. A shekara ta 44 kafin haihuwar Annabi Isa ya ayyana kan sa a matsayin mai mulkin kama-karya na dindindin.
Abinda ke nufin shi kadai zai mulki 'kasar Rum.
Maƙiyansa a siyasa sun yi fargabar zai iya yin ƙarfi sosai abinda ya sa suka ɗauki alwashin hamɓarar da shi.
Jagorori uku Marcus Junius Brutus da Gaius Cassius Longinus da kuma Decimus Junius Brutus dukkansu sanatoci ne a majalisa.
Decimus Brutus ya fi kowa kusanci da Caesar har ma yana tunanin shi zai gaje shi. Amma Marcus Brutus yana adawa da Caesar -kuma sun fafata a ya'kin Battle of Pharsalus a shekara ta 48 daga baya Ceaser ya yi masa afuwa har ma ya 'kara masa girma.
Su ukun tare da wasu mutane 60 ne suka yiwa Caesar 'kawanya a zauren majalisar dattawa kuma suka kashe shi.
Ba zamu iya cewa ga wasiyyar Caeser ta karshe ba, amma marubuci Shakespeare ya bayyana tsananin cin amanar a wasan kwaikwayon da ya rubuta mai tarihi.
A ciki Julius Caesar ya tambayi Marcus Brutus "har da kai Brutus?", - hakan na nufin bai yi zaton mutumin da ya yiwa afuwa kuma ya ƙarawa girma har ya ɗauke shi a matsayin aboki zai ci amanar sa ba.
Sai dai wadanda suka ci amana tare da kashe Ceaser sun manta matsayinsa da kuma irin farin jinin da Ceaser ke da shi wurin al'umma.
Yayin da suka sanar da mutuwar sa a zauren Capitoline Hill da ke Rum sai jama'a suka yi tsit kowa ya yi shiru daga nan kuma sai wuri ya yamutse inda aka kori Marcus Brutus da Decimus Brutus da kuma Cassius daga gari.
Mutuwar Ceaser ce ta kawo 'karshen mulkin Rum, daga nan sai Gaius Julius Caesar Octavianus Augustus ya zama Sarkin Rum na farko.
Sarauniya Isabella ta Faransa
Ya yin da sarauniyar farko ta bayyana a Biritaniya a karni na 16, akwai sarakuna mata da suka yi fice a tarihi.
Ɗaya daga ciki ita ce Isabella ƴar Faransa wadda ake kira "She-Wolf of France," ta taka muhimmiyar rawa wajen kashe Sarki Edward II na Ingila a shekara ta 1327.
Ƴar Sarkin Faransa Philip IV an haife ta a farkon shekara ta 1290 ta auri Edward ranar 25 ga Janairu1308.
Edward ya shahara cikin manyan mutane, na farko Piers Gaveston wanda aka kama kuma aka kashe shi a watan Yuni 1312 da manyan mutane da aka samu da laifi, akwai kuma Hugh Despenser.
Lokacin da Edward ya ce zai yaki Isabella.
Despenser ya zarge ta leƙen asiri don haka ya 'kwace kadarorinta kuma ya hana ta ganin mijinta.
Duk da cewar Edward ya yi niyyar aikenta Faransa don tattaunawar sulhu da 'dan uwanta.
Edward ma na son ziyartar Charles IV a Faransa amma ba ya son barin Ingila saboda barazanar da 'yan tawaye suka yi masa tare da Despenser.
Maimakon haka sai ya tura ɗansa kuma mai jiran gado.
Issabella ta samu kanta ƙarkashin kulawar 'dan uwanta.
Ta yi amfani da karfin ikon da take da shi wajen baiwa sarki zabi. Isabella da 'yarima mai jiran gado zasu koma idan aka sauke Despenser daga mulki kuma aka mayar mata da kadarorinta da matsayinta, amma Edward ba shi da niyyar amincewa da bukatar ta.
Isabella ta hada kai da Roger Mortimer, wani 'dan Ingila da ya yi gudun hijira bayan ya yiwa Sarki tawaye inda suka 'kulla yadda zasu kutsa Ingila su hambarar da sarki daga mulki.
Sun yi amfani da kudade da makaman da suka samu daga Belgium wajen kutsawa Ingila ranar 24 ga watan Satumban shekara ta1326.
Sarki Edward ya rasa magoya baya abinda ya sa Isabella ta 'kara samun hadin kai daga 'yan uwan sarkin da danginsa.
An kama Hugh Despenser an kashe shi ya yinda aka sauke Edward daga mulki sannan aka kashe shi a Berkeley Castle daga baya.
Sarki Edward na III ya fara mulki a irin ranar da aka yi auren iyayensa da ke rikici da juna, ranar 25 ga watan Janairun shekara ta 1327 .
Benedict Arnold: Babban mai cin amana a Amurka
A Amurka sunan Benedict Arnold dai dai ya ke da cin amana. Ya kasance jarumi a wurin George Washington saboda ya taimakawa Amurka ta samu nasara a yakin Fort Ticonderoga cikin watan Mayu a shekara ta 1775
Ya samu 'karin nasara a yakin Saratoga a shekara ta 1777, lamarin da ya sanya Faransa hada kai da masu juyin juya hali, sai dai lamari ya sauya daga baya bayan Arnold ya ci amanar Amurka ta hanyar fara yiwa Birtaniya leken asiri.
Arnold na ganin Amurka bata biya shi yadda abinda ya kamata ba kuma an fifita wasu mutane akan sa.
Almubazzarancin matarsa ya sa shi cin bashi har Washington ta zarge shi da karya doka Lamarin da ya 'bata masa rai, ga bashi ya yi masa yawa daga nan sai ya 'kulla ala'ka da Birtaniya.
Da Washington ta ba shi kwamandan sojoji a shekara ta 1780.
Sai Arnold ya dage zai shugabanci tsaro a West Pont da New York da kuma kogin Hudson. Yankuna ne masu muhimmanci a harkokin sadarwa da sufuri.
Ya yi shirin ragewa yankin 'karfin tsaro sannan ya mikawa Birtaniya wadda zata ba shi fan 20,000 tare da yiwuwar yaudarar Washington ta fada hannun abokan gaba.
An bankado shirin Arnold ne sakamakon kama wani jami'in leken asirin Birtaniya kuma abokin Arnold da wasu takardu. Amma ya yi sa'ar tserewa inda ya shiga jirgin yakin Birtaniya mai suna HMS Vulture.
An yi masa 'karin girma zuwa Birgediya Janar daga nan kuma ya fara yakar tsoffin iyayen gidansa.
Ya koma Ingila da zama har ya mutu a shekara ta 1801.