'Yan takarar shugabancin Najeriya 18 sun sa hannu kan yarjejeniyar zaɓe lafiya

Hoton taron yarjejeniyar zaben Najeriya

Asalin hoton, BBC/Kukah Centre

Bayanan hoto, 'Yan takarar sun amince su bi hanya ta shari'a idan suna da ƙorafi

‘Yan takarar shugabancin Najeriya 18 sun sanya hannu a kan yarjejeniyar amincewa da sakamakon zaben da za a yi ranar Asabar 25 ga watan nan na Fabarairu 2023.

Bisa tanadin yarjejeniyar, dukkanin ‘yan takarar sun amince cewa idan har ya kasance suna da wani ƙorafi kan zaɓen to za su bi hanyoyin da tsarin mulki ya tanada domin bi musu kadi.

Yarjejeniyar da aka yi a Abuja ranar Larabar nan wadda Kwamitin Zaman Lafiya na ƙasar ya shirye ta samu halartar dukkanin ‘yan takarar 18, tare da Shugaba Muhammadu Buhari, wanda za a gada.

Haka kuma tsohon shugaban ƙasar Kenya Uhuru Kenyata wanda shi ne jagoran masu sanya ido a zaɓen na Ƙungiyar Tarayyar Afirka, AU, da tsohon shugaban Afirka ta Kudu Thabo Mbeki duk sun halarta.

Dukkanin ‘yan takarar waɗanda suka haɗa da Bola Ahmed Tinubu na APC da Atiku Abubakar na PDP da Rabiu Musa Kwankwaso na NNPP da Peter Obi na LP da Omoyele Sowore na AAC, sun halarta tare da rattaba hannu a yarjejeniyar.

A jawabin Shugaban Najeriyar Muhammadu Buhari, ya buƙaci dukkanin 'yan takara da ke cikin zaɓukan da za a yi da su mutunta zaɓin masu zaɓe, kamar yadda INEC za ta bayyana.

Amma ya shawarci duk wanda ya kasance da ƙorafi a kan zaɓen da ya je kotu, sanna kuma ya yi kira da al'umma su kasance sun yarda tare da aminta da tsarin ɓangaren shari'ar ƙasar.

Tsohon shugaban Najeriya na soji Abdulsalami Abubakar wanda shi ne shugaban kwamitin na zaman lafiya ya kasance a wurin tare da Yakubu Gowon wanda shi ma tsohon shugaban kasar ne na soji.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A jawabin da ya aika wurin taron tsohon shugaban Najeriya na baya-bayan nan na farar hula Goodluck Jonathan, ya buƙaci hukumar zaɓe da jami’an tsaro su tabbatar zaɓen ya gudana cikin gaskiya da adalci da kuma inganci.

A jawabin wanda ɗaya daga cikin ‘yan kwamitin Rabaran Matthew Hassan Kukah ya karanta, Jonathan ya ce ana buɓatar yarjejeniyar zaman lafiyar domin hana ‘yan takara da abokan tafiyarsu daga amfani da bayanai na ƙarya domin tasiri a zaɓen, musamman a wannan lokaci na shafukan sada zumunta da muhawara.

Ya ce, babu wani lokaci da ya wuce yanzu idan aka yi la’akari da zaman ɗar-ɗar da ƙasar ke ciki a yanzu saboda zaɓen da ya dace a yi wannan yarjejeniya.

Jonathan ya ce, ‘’zaɓen ba yaƙi ba ne. Ƙasar na buƙatar dumukuraɗiyya da ta tsaya da ƙafarta. Duniya ta zuba mana ido kan yadda za mu samar da shugabancinmu da kuma tsarin samar da shugabancin da daidai.’’

Dakta Goodluck bai samu halartar taron ba saboda yana ƙasar Mali a matsayin wakili na ƙungiyar bunƙasa tattalin arzikin kasashen Afirka ta Yamma, ECOWAS ko CEDEAO, kan shawo kan rikicin ƙasar.

Shi ma tsohon shugaban ƙasar na soji Yakubu Gowon, ya shawarci ‘yan takarar ne da su kasance masu sanin ya kamata a harkokinsu.

Ya ce, Najeriya na buƙatar jagora wanda zai iya kawo mata tare da tabbatar da ribar dumukuradiyya ga jama’arta.’’

Gowon ya ƙara da roƙo ga waɗanda ke da niyyar haifar da matsala ga zaɓen da su sake shawara, su bayar da damar hanyar shawo kan matsalolin da ake ciki, cikin gaskiya da adalci, tare da fatan cewa za a yi zaɓukan lami lafiya da kuma sauyin gwamnati cikin kwanciyar hankali.

Sai dai duk da alƙawarin da 'yan takarar kan yi tare da sanya hannu a irin wannan yarjejeniya a matakin ƙasa da jihohi ana kokawa da cewa ba kasafai suke martaba ta ba, domin a kan samu rikice-rikice da tashin hankali kafin zaɓe da lokacin zaɓe da kuma bayan zaɓen.

Zaɓen na Najeriya na 2023 shi ne zaɓe mafi girma da duniya ta zuba ido a kansa a wannan shekara.

Tsoffin shugabannin ƙasashen Afrika biyar da suka halarci zaman sun haɗa da John Dramani Mahama na Ghana da Uhuru Kenyatta na Kenya da Joyce Bandah ta Malawi da Thabo Mbeki na Afrika Kudu da kuma Earnest bai Koroma na Saliyo.

Haka kuma akwai shugabar ƙungiyar ƙasashen Commonwealth Baroness Patricia Scotland da wakiliyar Sakataren Majalisar Dinkin Duniya a Yammacin Afrika Ms Giovanie Biha da wakilin Tarayyar Turai a Najeriya da kasashen Ecowas Samuel Isopi.