Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Dubban magoya bayan Real Madrid sun yi wa Mbappe tarbar girma
An yi wa Kylian Mbappe tarbar girma a Santiago Bernabeu, inda magoya baya 80,000 suka yi ta yin tafi lokacin da aka gabatar da shi sabon ɗan wasanta.
Real Madrid ta gabatar da Mbappe ranar Talata, bayan da ta ɗauki ɗan wasan daga Paris St Germain, wanda yarjejeniyarsa ya kare a karshen kakar da ta wuce.
An haska wani bidiyo mai ɗauke da tarihin kofi 15 da Real Madrid ta lashe Champions League da ƙwallayen da Mbappe ya zura a raga.
Daga nan shugaban Real Madrid Florentino Perez ya gabatar da Mbappe, bayan jawabin maraba da taya ƙungiyar murna da ta samu damar sayen ɗan wasan.
A bikin gabatarwa har da shugaban ƙungiyar na din-din--din,Jose Martínez Pirri da darakta Emilio Butragueno da tsoffin ƴan wasa da suka hada da Santamaría da Zidane da Raúl da Solari da Arbeloa da sauransu.
Tun cikin watan Fabrairu ɗan ƙwallon tawagar Faransa ya amince baka da baka cewar zai koma Sifaniya, sannan cikin watan Mayu aka sanar da zai bar PSG a karshen kakar da ta kare.
Tun farko an tsara cewar Mbappe mai shekara 25 zai koma Real Madrid ranar 1 ga watan Yuli, lokacin da aka buɗe kasuwar cinikayyar ƴan ƙwallo a La Liga.
To amma a lokacin ana buga gasar cin kofin nahiyar Turai ta Euro 2024 tare da tawagar Faransa a Jamus.
Sifaniya ce ta fitar da Faransa a zagayen kwata fainal a Euro 2024, inda ƙwallon ɗaya Mbappe ya ci a gasar, itama a bugun fenariti.
Mbappe ya lashe kofin duniya a 2018, kuma shi ne kan gaba a yawan cin ƙwallaye a PSG mai 256 a raga, tun bayan da ya koma ƙungiyar aro daga Monaco a 2017.
Ya amince da yarjejeniyar da za ta kare a Real zuwa karshen 2029, zai ke karbar £12.8m a kowacce kaka da karin ladan £128m da za a biya cikin shekara biyar, kuma zai rike kudin tallace-tallacensa.
Real Madrid ce ta lashe La Liga na bana na 36 jimilla da tazarar maki 10 tsakani da Barcelona, wadda ta yi ta ukun teburin babbar gasar tamaula ta 2023/24.
Haka kuma ita ce ta ɗauki Champions League, bayan doke Borrusia Dortmund a Wembley, kuma na 15 jimilla.