Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Dokar hana zirga-zirga ta fara aiki a jihar Kano
Gwamnatin jihar Kano ta kakaba dokar hana zirga-zirga a fadin jihar na tsawon awa 24.
A wani bayani da ya fitar, mai magana da yawun gwamnan jihar Muhammad Garba, ya ce dokar ta fara aiki ne daga karfe takwas na safiyar Litinin zuwa karfe takwas na safiyar Talata.
An dai sanya dokar ce jim kadan gabanin sanar da sakamakon zaben gwamnan jihar, wanda ya ayyana Abba Kabir Yusuf na jam'iyyar NNPP a matsayin wanda ya yi nasara.
Muhammad Garba ya ce gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje ya bayar da umurnin sanya dokar ne domin dakile duk wani yunkuri na bata-gari wajen barnata dukiyar al'umma.
Murnar magoya bayan NNPP
Magoya bayan jam'iyyar NNPP a jihar Kano sun yi gangami tare da murnar nasarar da Abba Kabir Yusuf ya samu a zaben gwamnan jihar.
Daruruwan magoya bayan jam'iyyar sun taru a kofar gidan jagoran jam'iyyar, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da ke kan titin Miller a jihar ta Kano.
An gudanar da shagulgula a wadansu titunan jihar ta Kano kamar su Zoo road da dai sauransu.
A ranar Litinin da safe ne hukumar zaben Najeriya mai zaman kanta INEC ta ayyana Abba Kabir Yusuf na jam'iyyar NNPP a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar Kano.
Abba Kabir, wanda ake yi wa da laƙabi da Abba Gida-gida ya samu nasara ne a kan abokin hamayyarsa na jam'iyyar APC mai mulki Nasiru Yusuf Gawuna.
Gawuna shi ne mataimakin gwmnan jihar Kano.