Yadda mata ke gwagwarmaya a rayuwar yau da kullum a Yemen

Umm Adel

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi kiyasin cewa mata irin Umm Adel sune ke kan gaba wajen ciyar da ɗaya cikin iyalai uku da faɗa ya raba da muhallansu

Umm Adel ta rufe yatsunta yayin da take rike da wani dutse a hannunta, inda take kokarin kare kanta. Akwai manya karnuka a titin da take tafiya akai kuma mai cike da duhu. Suna cikin yunwa kum yawancinsu na ɗauke da ciwon haukan kare.

"Duk takun da nayi, sai zuciyata ta harba saboda ina tsoron kada karnuka su far min," in ji matar. "Babu hasken wuta kuma dukkan gidajen jama'a na rufe, don haka babu wanda zai taimaka min. Na yi kokarin tafiya sannu a hankali don kada karnukan su jiyo ni".

Tana rayuwa ne a Sanaa, babban birnin ƙasar Yemen.

Majalisar Ɗinkin Duniya ta bayyana matsalolin jin kai na ƙasar a matsayin mafi muni a duniya, inda kashi biyu bisa-uku na al'ummar ƙasar - kusan miliyan 21.6 - ke bukatar agaji a 2023.

Faɗa na tsawon shekaru takwas tsakanin dakarun gwamnatin ƙasar - da ke samun goyon baya daga haɗakar soji na Saudiyya - da kuma ƴan tawayen Houthi da ke biyayya ga Iran - wadda ke rike da ikon Sanaa da kuma wasu wurare a yammacin ƙasar - sun sanya ƴan ƙasar da dama shiga tasku, musamman ma mata da yara.

Mata irinsu - Umm Adel - na fama da matsalar ƙarancin abinci mai muni, inda kashi kaɗan na mata ne kaɗai ke aiki a Yemen.

Kuma duk da haka asusun kula da yawan jama'a na Majalisar Ɗinkin Duniya ya yi kiyasin cewa mata ne kan gaba wajen ciyar da ɗaya cikin iyalai uku da faɗa ya raba da muhallansu.

Yemen

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Umm Adel ta fito ne daga birnin Taiz da kudu maso yammacin ƙasar, wanda ƴan tawayen Houthi suka yi ƙawanya a tsawon lokacin yakin

A cikin karamin gidanta, kayan Umm Adel sun taru a kasa cikin datti.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Kunshe a cikin jakunkuna, sun shirya don a kwashe su ita da 'ya'yanta huɗu zuwa wani wuri.

Babu kayan ɗaki, don haka iyalai na kwana akan barguna a ƙasa.

Babu hotuna akan bangon ɗakinta ko wani abu na jin daɗi a gidanta. Wannan wuri ne kawai da mutum zai zauna don tsira da rayuwarsa. Abinci da kungiyoyin agaji ke rabawa ma sun yi ƙaranci.

Sau ɗaya aka taɓa bai wa Umm Adel agajin abinci, duk da ta yi kokarin yin rijistar kanta don karɓan tallafin sau da dama.

"Dole ne in nemo itace don kunna wuta domin in dafa shinkafa," in ji ta.

"Yawancin abincin da muke ci bai dafu da kyau ba, abin da zan iya samu kenan. Ɗa na ba shi da lafiya, kuma ba ni da kuɗin da zan iya siyo masa magani."

Ko da yake rayuwa a Sanaa tana da wuya, Umm Adel har yanzu tana jin kwanciyar hankali a nan fiye da Taiz, inda ta fito.

‘Yan tawayen Houthi dai sun yi wa birnin da ke karkashin ikon gwamnati ƙawanya a tsawon yakin da kuma yanke shi daga sauran sassan ƙasar.

"Yana da hatsari a can, mutane sun zama miyagu kuma suna ƙin juna. Na yi ƙoƙari na zauna a wurin don yarana don su kasance kusa da danginsu, amma na ƙasa hakan saboda babu wanda ya taimake ni."

Kungiyar Kare Hakkokin Bil Adama ta Yemen, ta ce a shekarar 2021 sama da mata da 'yan mata miliyan 10 ne ke bukatar taimako.

Umm Said

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Umm Said ita ce ke ciyar da gidansu musamman wajen ɗaukar ɗawainiyar 'ya'yanta da kuma jikokinta a daidai lokacin da yaranta ke faɗa da ƴan tawayen Houthi

Maeen Sultan al-Obeidi lauya ce kuma mai fafutukar kare hakkin ɗan adam a birnin Taiz.

"Mutanen da yakin ya fi shafa sun kasance mata," in ji ta.

"Faɗan ya ɗaiɗita da dama da kuma rasa masu ɗaukar ɗawainiyarsu. An tilastawa Iyaye su aurar da 'ya'yansu a ƙananan shekaru saboda matsin rayuwa. Mata da yawa sun rasa 'ya'yansu da mazajensu da kuma ƴan uwansu. Ga waɗanda ke fama da wahalhalu a sansanonin da aka kafa, babu ilimi ko ingantaccen kiwon lafiya".

Tana cikin damuwa kan lafiyar mata ta yau da kullum.

"A farkon yakin a yanke wuraren samun ruwan sha, don haka mata na tafiya wurare masu nisa domin ɗebo ruwa," in ji Maeen.

"An katse wuraren bayar da iskar gas, don haka mutane ke tafiya a kafa zuwa daji domin neman itace. Mata sun rasa wasu yatsunsu ko samun lahani a yankunan da ake hako ma'adinai saboda fashewar abubuwa lokacin da suka je neman itace don ciyar da 'ya'yansu. Wannan yaki ne da ya shafe komai".

Akalla mata 109 ne suka mutu ko kuma jikkata sanadiyyar ayyukan haƙar ma'adinai a wasu yankuna da kuma gonaki tun fara yakin a karshen 2014, a cewar alkaluma da wata hukumar bincike kan zargin take ƴancin ɗan adam ta gudanar tare da haɗin gwiwar ƙasashen waje.

A kowace rana, Mujahid Kamel, wani mai kanti a birnin Sanaa, na ganin yadda kwastomominsa ke fama da halin matsin rayuwa.

"Mutane na cikin kunci da yunwa da kuma matsin rayuwa a nan," in ji Mujahid. "Tsadar kuɗin mota da mai da kuma haraji sun sanya abubuwa yi mana wuya."

Samun isasshen abinci na ɗaya daga cikin babbar matsala da ƴan Yemen ke fama da ita. Yunwa babbar barazana ce.

Shirin Samar da Abinci ta Duniya ya ce agajin gaggawa da ake kai wa Yemen, shi ne irinsa mafi girma a ko'ina a faɗin duniya a 2022, inda aka samarwa mutane kusan miliyan 13 da agaji, musamman ma kuɗi don samun abinci.

Grocers in Sanaa say the rise in food prices has heavily affected people

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Masu kantin sayar da kayayyaki a Sanaa sun ce ƙaruwar farashin kayan abinci ya shafi mutane da dama

Mujahid ya ce a yanzu yadda mutane a Yemen ke sayen kayaki daban yake da a baya. "Sau tari suna da kuɗin sayen abinci na rana ɗaya ne kaɗai. Kuma abubuwan da suke ita saye sun haɗa da alkama da gari da kuma mai".

Umm Said ta ce tana sane da wannan hali na gwagwarmaya a kullum.

Tana rayuwa ne da iyalanta a Sanaa, kuma ta kasance a wurin tun soma yakin.

Ta fito ne daga Razih, wani yanki da ke arewacin lardin Saada da ke kusa da iyaka da Saudiyya, inda take tuno lokacin da ta karɓi 'ya'yanta huɗu da ƴan mata guda uku domin barin wurin.

"Wani hari ta sama ya ruguza gidanmu gabaki-ɗaya. Babu abin da ya rage face ɓurɓushi na toka," in ji ta.

"Muna rayuwa cikin fargaba a kowace rana saboda an kai hari a wurare da dama da ke yankinmu. Mun rasa gidajenmu da wani karamin kanti na mijina, inda daga nan ne muka zo Sanaa da tilasta mana rayuwa cikin kogo a kan tsaunuka.

"Na kasa daina kuka, kuma haka yara na ma. Mun zauna cikin duhu saboda ko ɗan wutar da muka kunna za ta iya janyo hari ta sama."

Komawa rayuwa a cikin birni ya sanya Umm Said shiga bukatar son samun kuɗi don ciyar da iyalanta ganin irin wahalar rayuwa da take fama da shi.

A yanzu 'ya'yanta da dama na faɗa da ƴan tawayen Houthi a kan tsaunuka, wanda ke nufin ita za ta ɗauki ɗawainiyar jikokinta ma.

Tana samun ƴan kuɗaɗe saboda sayar da tufafi da take yi a wuraren bukukuwa, sai dai ba koyaushe take yin hakan ba saboda yanayin lafiya, kuma kuɗin da take samu bai taka kara ya karya ba.

"A yawan lokuta mun kasance muna kwana ba tare da cin abincin dare ba," in ji ta. "Wuyata na min zafi, kuma ina wahala wajen yin numfashi. Amma abin da zai hana ni yin kasuwanci shi ne mutuwa."