Abin da ya kamata ku sani game da takun saƙa tsakanin Habasha da Somaliya

Somaliya da Habasha

Asalin hoton, Getty Images

Somaliya ta kori jakadan ƙasar Habasha daga ƙasar tare da ba da umarnin rufe wasu ofisoshin jakadanci biyu a wani sabon rikici na diflomasiyya tsakanin ƙasashen da ke makwabtaka da juna a yankin kusurwar Afrika.

Mogadishu kuma ta kira jakadanta daga Addis Ababa, babban birnin Habasha, don "taattaunawa ta musamman" bayan da ta zargi makwabciyarta da yin katsalandan a "al'amuran cikin gida" na Somaliya.

A baya dai Habasha ta musanta zarge-zargen keta ƴancin cin gashin kan Somaliya amma har yanzu ba ta mayar da martani kan sabbin matakan ba.

Me ke haddasa rikicin?

A map showing the Horn of Africa

Asalin hoton, bbc

Bayanan hoto, Ƙasar Habasha wadda ba ta da mashigar ruwa ta musanta cewa tana keta ƴancin ƙasar Somaliya

Takaddama tsakanin ƙasashen biyu ta ɓarke ne a lokacin da Habasha wanda ba ta da ruwa ta kulla yarjejeniyar tashar jiragen ruwa da jamhuriyar aware ta Somaliland a watan Janairun wannan shekarar.

A cewar yarjejeniyar, wadda ba ta da goyon bayan doka, kuma ake kallonta a matsayin wata niyyar kulla wata yerjejeniya nan gaba, Habasha za ta iya karɓar hayar fili a bakin teku da ya kai tsawon kilomita 20 don gina sansanin sojin ruwa.

Hakan ya ɓata wa Somaliya rai, saboda ta ɗauki Somaliland a matsayin yankin da ke ƙarƙashn ikonta. Ta bayyana yarjejeniyar a matsayin rashin mutunci da kuma yi wa zaman lafiya zagon ƙasa.

A lokacin, jami'ai a Somaliland sun ce Habasha, ita ce ƙasa ta farko a duniya da za ta amince da matsayinta ta ƙasa mai cin gashin kanta.

Somaliland dai ta ɓalle daga Somaliya sama da shekaru 30 da suka gabata, amma ƙungiyar Tarayyar Afirka (AU) da Majalisar Ɗinkin Duniya ba su amince da ita a matsayin ƙasa mai ƴancin kanta ba.

Hukumomi a Habasha ba su fito fili sun amince da cewa za su amince da ƴancin Somaliland ba. A madadin haka, sun ce za su ba da hannun jari ga kamfanoni masu riba kamar Ethiopian Airlines.

Ko an yi yunƙurin shiga tsakani?

Yarjejeniyar ta janyo suka daga ƙasashen duniya kan Addis Ababa yayin da ƙungiyar AU da wasu ƙasashen yammacin duniya ciki har da Amurka suka yi kira da a mutunta ƴancin ƙasar Somaliya.

A wani yunkuri na samun goyon bayan ƙasashen yankin shugaban ƙasar Somaliya, Hassan Sheikh Mohamud ya ƙaddamar da gagarumin aikin diflomasiyya inda ya ziyarci ƙasashen Eritriya da Masar - ƙasashe biyu da ba su jituwa da Habasha.

An yi ta ƙoƙarin yin tattaunawar diflomasiyyar bayan fage don sassauta tashin hankali amma ba a saurari buƙatar Somaliya na a sauya yarjejeniyar bai ɗaya ba.

Me yasa Habasha ke buƙatar damar shiga teku?

Ƙasancewarta mai yawan al'umma kusan miliyan 120, Habasha ita ce ƙasa mafi yawan jama'a a duniya da ba ta da ruwa.

Fiye da kashi 90 cikin 100 na kasuwancinta na ƙasa da ƙasa na bi ne ta ƙaramar makwabciyarta, Djibouti.

Jami'ai a Addis Ababa na ganin hakan bai kamata ya ci gaba da kasancewa ba.

Kafin a rattaɓa hannu kan yarjejeniyar ta Somaliland, firaministan Habasha Abiy Ahmed, ya ce samun damar shiga teku lamari ne mai matuƙar muhimmanci ga ƙasarsa.

Kalaman nasa na cewa Habasha za ta nemi hanyoyin lumana don samun damar shiga tashar jiragen ruwa amma "idan hakan ya faskara, za mu yi amfani da karfi" ya haifar da tashin hankali a yankin.

Ita ma Habasha tana da burin gina rundunar sojin ruwa - duk da cewa ba ta da ruwa.

A shekarar 2018 Abiy ya ce ya kamata Addis Ababa ta kafa rundunar sojan ruwa daidai da sojojinta na sama da na ƙasa.

Yaya muhimmancin waɗannan sabbin matakan?

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Korar jami'an diflomasiyyar Habasha da Somaliya ta yi, ya yi nuni da ƙarin tashin hankali.

An sanar da matakin ne kwana guda bayan da Addis Ababa ta karɓi baƙuncin jami'ai daga yankin Puntland mai cin gashin kansa na Somaliya.

A baya-bayan nan ne dai yankin na Puntland ke takun saƙa da gwamnatin ƙasar Somaliya dangane da sake fasalin tsarin mulkin ƙasar.

A ɗan tsakanin nan ne majalisar dokokin tarayyar Somaliya ta zartas da gyare-gyaren kundin tsarin mulkin ƙasar da suka haɗa da gabatar da zaɓen shugaban ƙasa kai-tsaye da kuma amincewa da shugaban ƙasar ya zaɓi firaminista.

Sai dai lardin Puntland da ke arewa maso gabashin ƙasar ya yi watsi da matakin.

Puntland wadda ke da matsayin yanki mai cin gashin kanta tun daga ƙarshen shekarun 1990, ta ce za ta fice daga tsarin tarayya tare da gudanar da mulkin kanta da kanta har sai an gudanar da zaɓen raba gardama na ƙasa.

Tafiyar wakilan Puntland zuwa Addis Ababa sakamakon wannan rarrabuwar kawuna ta tayar da ƙura a Mogadishu.

Ba a dai tabbatar da irin matakan ramuwar gayya da Habasha za ta ɗauka ba. Amma ba a tunanin ɓarkewar yaƙi da makamai.

Sai dai kuma, taɓarɓarewar dangantakar na iya yin tasiri a yaƙin da ake yi da masu iƙirarin jihadi a yankin kusurwar Afirka.

Tuni dai akwai fargabar cewa ƙungiyar Al-Shabaab da ke da alaƙa da Al-Qaeda za ta iya amfani da tashin hankalin wajen ɗaukar mayaƙa da kuma ƙara barazana ga tsaro a yankin.

Har ila yau, ƙasar Habasha na ɗaya daga cikin ƙasashen da ke ba da gudummawar sojoji ga tawagar wanzar da zaman lafiya ta Tarayyar Afirka a Somaliya.

Ana sa ran tawagar za ta fice daga ƙasar a ƙarshen wannan shekarar, tare da miƙa ayyukan tsaro ga gwamnatin Somaliya.

Sai dai takun saƙa tsakanin Somaliya da ɗaya daga cikin makwabtanta mai muhimmanci na iya yin tasiri kan wannan lamarin.