Mbappe ya sayi Caen ƙungiyar da ke buga Ligue 2 a Faransa

Lokacin karatu: Minti 1

Ɗan wasan Real Madrid, Kylian Mbappe ya kammala sayen ƙungiyar ƙwallon kafa ta Caen mai buga karamar gasa Faransa ta Ligue 2.

Interconnected Ventures, wanda Mbappe ya kafa, ya sayi kaso mafi tsoka a ƙungiyar ta ɓangaren hannun jarinsa a Coalition Capital.

Ƙyaftin ɗin Faransa, mai shekara 25, an sanar cewa ya kashe kusan Yuro miliyan 15, kimanin £12.6m, wanda ya biya ta hanyar asusun saka hannun jari da yayi.

Coalition Capital ya maye gurbin kaso mafi yawan masu hannun jari a baya a asusun saka hannun jari na Amurka Oaktree.

Pierre-Antoine Capton, shugaban hukumar kula da ƙungiyoyin kasar wajen sa hannun jari, shi ne yake mai karamin hannun jari a Caen.

"Wannan dama ce mai ƙyau ga Stade Malherbe Caen da yin hulɗa da Coalition Capital don ci gaban ƙungiyar. Idan ka auna kadararsa da hangen nesa na musamman ne a wasanni," in ji Capton.

Caen ta kare a matsayi na shida a kakar da ta wuce, wadda za ta fara gasar Ligue 2 ta 2024/24 ranar 17 ga watan Agusta da Paris FC.

Hakan zai zama kwana ɗaya kafin Mbappe ya fara buga wa Real Madrid gasar La Liga da Real Mallorca bayan da ya koma kungiyar daga PSG a bana.

Caen ta faɗi daga babbar gasar tamaula ta Faransa ta Ligue 1 a shekarar 2019.

Sanarwar da Caen din ta fitar ta ce: "Wannan ciniki yana nuna wani muhimmin mataki na ci gaban ƙungiyar, kuma yana karfafa burinsa na kasancewa a cikin wuraren tarihi a kwallon kafa ta Faransa."