Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Endrick ya sharɓi kuka lokacin da Real Madrid ta gabatar da shi
Real Madrid ta gabatar da Endrick a gaban magoya baya ranar Asabar a Santiago Bernabeu, wanda ya ɓarke da kuka.
Ya ce dalilin kukan shi ne ''Tun ina ɗan yaro na ke mai goyon bayan Real Madrid, yanzu kuma na zama ɗan kwallon ƙungiyar.''
Filin ya ɗauki magoya baya da yawa har da ƴan Brazil da dama, waɗande ke dauke da rigar kasar da kuma ta ƙungiyar Palmeiras.
Fitattun tsoffin ƴan wasan Real Madrid sun halarci bikin tare da iyayen Endrick, haka shima mahaifin ɗan wasan, Douglas Ramos ya sha kuka a lokacin da zai zauna a kan kujera.
Yadda aka tsara wa Endrick tunkarar kakar bana
Matashin ɗan Brazil ya fara da zuwa aka auna koshin lafiyarsa daga nan ya saka hannu kan ƙunshin yarjejeniya daga nan ya je Bernabeu, inda aka gabatar da shi.
An bai wa ɗan wasan riga mai lamba 16 da zai yi amfani da ita a ƙungiyar a kakar farko da zai taka leda a Real Madrid.
Alvaro Odriozola ne ya yi amfani da lamba 16 a ƙungiyar da ta lashe La Liga da Champions League a kakar da ta wuce, Odriozola ya koma Real Sociedad.
Ɗan wasan zai je Amurka ranar Lahadi 28 ga watan Yuni a wasannin sada zumunta da Real Madrid za ta kara, domin shirin fuskantar kakar 2024/25.
Kenan ana sa ran Endrick zai buga wa Real Madrid wasanni, domin a auna kwazonsa, bayan da za ta kara da Barcelona da Chelsea, kafin European Super Cup.