Waiwaye: Zargin El-Rufai kan Ribadu da Uba Sani da tsawaita wa'adin Ganduje

Lokacin karatu: Minti 4

Wannan maƙale ce da ke kawo muku bitar muhimman labaran da suka faru a Najeriya cikin makon da muke bankwana da shi

Uba Sani da Nuhu Ribadu ba abokaina ba ne yanzu - El-Rufa'i

Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i ya bayyana cewa 'a yanzu Uba Sani ba abokinsa ba ne' bayan abubuwan da ke faruwa baya-bayan nan.

El-Rufa'i ya bayyana hakan ne a tattaunawar da ya gudanar da tashar talabijin ta Arise da yammacin ranar Litinin.

Bayan kammala wa'adinsa na shekara takwas a matsayin gwamnan jihar Kaduna, tsohon gwamnan na fuskantar bincike kan kuɗaɗe da ake zargin sun yi ɓatan-dabo a lokacin mulkinsa.

Lamarin ya haifar da muhawara kasancewar tsonon gwamnan da gwamna mai ci Uba Sani sun kasance makusanta tsawon shekara takwas na mulkin tsohon gwamnan.

El-Rufa'i ya ce "a yanzu Uba Sani da Nuhu Ribadu ba abokansa ba ne bayan da ya zargi Ribadu da kitsa ''ruguza'' shi a siyasance ta hanyar amfani da Uba Sani.

APC ta tsawaita wa'adin mulkin Ganduje

A tsakiyar makon ne kuma jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya ta kaɗa ƙuri'ar amincewa da salon jagorancin shugabanta, Abdullahi Umar Ganduje.

A taron da jam'iyyar ta kammala a ranar Laraba a Abuja, masu ruwa da tsaki na jam'iyyar sun yaba da rawar da Ganduje ya taka tun bayan naɗa shi kan muƙamin a watan Agustan 2023.

Hakan na nufin cewa tsohon gwamnan na jihar Kano zai ci gaba da jagorancin jam'iyyar har zuwa lokacin da za a yi babban taronta na ƙasa, inda za a zaɓi cikakken shugaba.

A watan Agustan 2023 ne kwamitin gudanarwa na jam'iyyar ya tabbatar da Ganduje a matsayin shugaban jam'iyyar na riƙo na ƙasa, bayan ajiye aikin shugaban jam'iyyar da ya gabace shi, Sanata Abdullahi Adamu

Buhari ya koma zama a gidansa na Kaduna

A cikin makon nan ne tsohon Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya koma gidansa na birnin Kaduna daga Daura na jihar Katsina.

Tun bayan saukarsa daga mulki a watan Mayun 2023, Buhari ke zaune a mahaifarsa ta Daura da ke jihar Katsina.

Tsohon shugaban ya samu rakiyar Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima, da Gwamnan Borno Babagana Zulum, da Gwamnan Kaduna Uba Sani.

Akwai kuma sauran 'yansiyasa da tsofaffin jami'an gwamnati da suka tarɓi shugaban a gidan nasa.

Dangote ya sake rage farashin man fetur

A ranar Laraba ne kamfanin Dangote ya sanar da rage wa dillalai abokan hulɗarsa farashin litar man zuwa N825 daga N890, ragin naira 65 kenan.

Karo na biyu kenan kamfanin yana rage farashin man a watan Fabrairun 2025, abin da dillalan man suka bayyana da "abin a yaba".

Rage farashin ya sa man na Dangote ya zama mafi araha idan aka kwatanta da wanda ake shiga da shi ƙasar daga ƙasashen waje.

Sanata Natasha ta kai ƙarar Akpabio kan 'ɓata suna'

A cikin mako ne kuma Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan mai wakiltar mazaɓar Kogi ta tsakiya a Majalisar Dattawan Najeriya ta shigar da shugaban majalisar ƙara a gaban kotu kan ɓata mata suna.

A ƙarar da ta shigar gaban Babbar Kotun Tarayya a Abuja ranar Talata, 'yarmajalisar ta zargi Sanata Godswill Akpabio da mataimakinsa na musamman, Mfon Patrick, da yin kalaman ɓata suna a kanta.

Ta nemi kotun ta tilasta wa mutanen janye kalaman, su nemi afuwarta a wani shafin jarida, sannan su biya ta diyyar naira biliyan 100.

A makon da ya gabata ne sanatar da shugaban suka yi cacar baki a zauren majalaisar bayan Akpabio ya sauya mata wurin zama, abin da ya jawo cecekuce tsakanin 'yan Najeriya musamman a shafukan sada zumunta.

Turji ya kafa sabuwar daba a Sokoto - mazauna yankin

A farkon makon ne kuma al'ummar Sabon Birni a jihar Sokoto da ke arewa maso yammacin Najeriya suka bayyana kokensu bayan da suka ce riƙaƙƙen ɗan bindiga Bello Turji yana nan a ƙauyukansu, inda ya ke ci gaba da garkuwa da mutane da sanya masu haraji.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da rundunar sojin ƙasar ke cewa tana bibiyar Turjin kuma nan ba da jimawa ba za ta ga bayan sa.

Al'ummar yankin ƙaramar hukumar Sabon Birni ta jihar Sokoton sun ce yanzu haka Bello Turji ya kafa sabuwar daba a yankinsu, inda ya ke tura yaransa su aikata ɓarna a ƙauyukan yankin.

Sun ce Turji da yaran nasa sun dawo da kai hari kan ƙauyuka ne bayan janyewar sojojin Najeriya da a baya suka yi ɓarin wuta a maɓoyar ƴan bindigar.