Mece ce kotun hukunta manyan laifuka ta duniya, ICC kuma mene ne aikinta?

Asalin hoton, Getty Images
Kotun hukunta manyan laifuka da ake kira da "International Criminal Court" a Turance ko kuma ICC a taƙaice kotun duniya ce wadda ke da ikon gabatar da ƙara dangane da kisan kiyashi da laifukan yaƙi da na take haƙƙin bil'adama.
A watan Nuwamba ne, kotun ta aike da sammacin kama firaiministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu da tsohon ministan tsaron Isra'ilar, Yoav Galant da kuma kwamandan sojin ƙungiyar Hamas wanda aka haƙiƙance ya rasu - Mohammed Deif.
Me kotun ta ICC ke yi?
An dai kafa kotun wadda take a birnin Hague da ke kasar Holland ne a shekarar 2002 domin kama mugayen shugabanni da laifin ta'asar da suke yi.
Shugabannin ƙasashen duniya ne dai suka buƙaci a kafa ta kotun biyo bayan yaƙin Yogoslavia da kisan kiyashin ƙasar Rwanda.
ICC ce ta zamo wani wuri na ƙarshe da za a hukunta waɗanda suka aikata wasu laifukan da hukumomi da shugabannin ƙasashe suka gaza hukuntawa.
Hakan na nufin kotun za ta iya hukunta laifukan da aka aikata ne daga ranar 1 ga watan Yulin 2002, lokacin da dokar da ta kafa kotu ta fara aiki.

Dokar mai suna "Rome Statute" wadda ta kafa kotun ta samu sa hannun ƙasashe 124.
Sannan ƙarin 34 sun rattaɓa hannu kuma akwai yiwuwar za su amince da ita ta yi aiki a kansu.
Sai dai kuma Isra'ila ba mamba ba ce sannan ita ma Amurka ba ta cikin jerin mambobin kotun.
Waɗanne hukunci kotun ICC ta yi?
Hukuncin kotun na farko shi ne na watan Maris ɗin 2012 wanda ta yi kan Thomas Lubanga, madugun ƙungiyar tayar da ƙayar baya da ke Jamhuriyar Dimokraɗiyyar Congo.
Kotun ta same shi da laifin yaƙi mai alaƙa da amfani da ƙananan yara a rikicin da ƙasar ta yi fama da shi inda kuma ta yanke masa hukuncin zaman gidan yari na tsawon shekara 14.
Wani babban mutum da aka taɓa gurfanarwa a gaban kotun shi ne tsohon shugabanƙasar Ivory Coast, Laurent Gbagbo. An tuhumi Gbagbo a 2011 da laifukan kisan kai da fyaɗe da tursasa jama'a da "sauran ayyukan rashin imanin", duk da cewa an wanke shi daga dukkan tuhume-tuhumen.

Asalin hoton, AFP
Daga cikin mutanen da kotun ta ICC ke nema ruwa a jallo sun haɗa da Joseph Kony, jagoran ƙungiyar ƴan tawayen Uganda da ake kira Lord's Resistence Army. An tuhume shi da aikata laifukan cin zarafin ɗan'adam da na yaƙi da suka haɗa da garkuwa da dubban ƙananan yara.
Kotun tana kuma na da sammaci a kan tsohon shugaban ƙasar Sudan, Omar al-Bashir bisa tuhumar kisan ƙare dangi da laifukan yaƙi da na tursasa bil'adama.
ICC na shan suka daga tarayyar Afirka kan yadda kotun ta kafa ƙahon zuƙa kan nahiyar Afirka.
Sai dai kuma kotun ta musanta zarge-zargen nuna bambanci inda ta ce yawancin ƙasashen da abin ya shafa ne ke kai ƙarararrakin ko kuma Majalisar Ɗinkin Duniya.
A 2023, kotun ta ICC ta fitar da sammacin kama shugaban Rasha, Vladimir Putin. Kotun ta yi zargin cewa yana da hannu a ayyukan yaƙi, kuma ta ɗora tuhumar tata ne a kan ɗaukar ƙananan yara ba bisa ƙa'ida ba daga Ukraine zuwa Rashar.
Ta yaya kotun ke hukunta wanda ake zargi da aikata laifi?
Kotun ta ICC dai ba ta da ƴansanda na kanta da za su iya bin diddigin mutum har su kama shi.
Sai dai ICC na dogara ne ga ƴansandan ƙasashe a lokacin da aka kai ƙara ta hanyar kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ko kuma ƙasar da take mamba ce, wajen kama wanda ake tuhuma da kuma tasa ƙeyarsa zuwa Hague.
Mai gabatar da ƙara ne yake farawa da buɗe bincike idan ƙara ce da Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya ne ya shigar da ita ko kuma ƙasar da ta amince da hukuncin kotun.
Wanda ake zargin ka iya ɗaukar wani mataki a kan kansa to amma hukunci na faruwa ne bayan wata tawagar alƙalai ta amince.
Ƙasashe mambobi ne ka zaɓar mai gabatar da ƙara da kuma alƙalan kotun.
Idan ƙara ta kai ga hukunci, to dole ne sai an tabbatar da tuhumar ba tare da wata tababa ba cewa mutumin da ake zargin ya aikata laifin. Alƙalai uku za su duba shaidu sannan sai su gabatar da hukunci, idan aka samu wanda ake zargin da laifi.
Me ya sa Amurka ba ta kasance mamba a kotun ICC ba?
A lokacin da ake mahawarar kafa kotun ta ICC, Amurka ta ce dakarunta ka iya fuskantar hukunci da bai dace ba.
A wani lamari da ya fuskanci kakkausar suka a watan Yuli 2002, Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya ya zaɓi wani matsayin sassauci da ya bai wa dakarun Amurka cin karensu babu babbaka na watanni 12 ba tare da fuskantar hukunciba, da za a rinƙa sabuntawa a kowacce shekara.
Sai dai Kwamitin Tsaron ƙarƙashin shugabansa na wancan lokacin Kofi Anan ya ƙi amincewa ya sake sabunta wannan dama ga sojojin na Amurka a watan Yunin 2004, bayan wasu hotunan dakarun na Amurka sun fito inda suke cin zarafin fursunoni ƴan Iraqi.
Ana yi wa kotun kallon rauni saboda rashin kasancewar Amurka a ciki.
Sai dai kuma Amurkar kan bai wa kotun haɗin kai a wasu ƙararrakin.
Shugaba Joe Biden ya umarci hukumomin tattara bayanan sirri na ƙasar da su bai wa kotun shaidun da ke nuna aikata laifukan yaƙi da ake tuhumar shugaban Rasha Vladimir Putin.
Waɗanne ƙarin ƙasashe ne ba mambobin kotun ICC ba?
Akwai ƙasashe masu tasiri da dama da ba mambobin kotun ba ne kuma hukuncin ICC ɗin bai hau kansu ba.
Ƙasshen sun haɗa da China da India da Pakistan da Turkey duk ba su saka hannu kan yarjejeniyar da ta kafa kotun ba.
Sauran su ne Isra'ila da Egypt da Iran da Rasha.
Mene ne tasirin ICC kan kotunan ƙasashe mambobi?
Ƙasashen da suka rattaɓa hannu kan dokar kotun ICC ka iya son samun damar hukunta duk irin laifukan da kotun ta ICC ke iya yi - idan suka kasa kuma sai ita kotun hukunta manyan laifukan ta duniya ta kai ɗauki.
Wasu gwamnatoci tuni sun fito da dokoki na yin sauyi ga tsarin shari'arsu.
A ina kotun ICC ke samun kuɗaɗenta?
Ƙasashe mambobi ne suke tallafama mata. Tsarin tallafawar ya yi kama da irin tsarin tallafa wa Majalisar Ɗinkin Duniya daidai gwargwadon arziƙin kowacce ƙasa.
Sai dai kuma rashin kasancewar Amurka mamba ya sanya tsarin tallafin kuɗi ga kotu ya yi wa wasu ƙasashe mai wuya.
Burtaniya da Japan da Jamus da Faransa duka na daga cikin ƙasashen da suka fi kowacce ƙasa tallafa wa kotun.











