Mijina ya tafi ci-rani shekara 12, yanzu ji nake kamar bazawara

- Marubuci, Prince Malik
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Urdu, Shakargarh
“Ya kamata waɗanda ke tafiya ci-rani a ƙasashen waje aƙalla su rinƙa tunawa da matan da suka bari a gida.” Waɗannan ne kalaman Sa’eqa Najib, wata mai shekara 40 daga yankin Shakargarh na ƙasar Pakistan, wadda mijinta ya yi amfani da ɓarauniyar hanya domin tafiya Turai, shekara 12 da suka gabata.
Baya ga cewa Sa’eqa ta iya riƙe 'ya'yanta biyar tun bayan tafiyar mijin nata, yanzu kuma tana shirin tura babbar 'yarta jami’a.
Sa’eqa ta ce a lokacin da suka yi aure, mijinta na aiki ne da wani kamfanin haɗa magunguna, sai dai albashin da ake biyansa babu yawa, ba ya isar su.
Daga nan sai mijin nata ya fara tunanin tafiya ƙasar waje.
Ta ce mijinta ya ɗauki harama ta ɓarauniyar hanya, inda ya fara da isa Turkiyya, daga nan ya shiga Girka, ya ƙarasa zuwa Italiya, lamarin da ya ɗauke shi shekara biyu.
Kuma ta ce tun daga wancan lokacin ba ta ƙara ji daga mijin nata ba.
Ta ƙara da cewa bayan kimanin shekara uku wani da ya san mijinta ya ce mata yana nan a raye, yana zama a wani sansani a Italiya.
Ya ce a lokacin da ya gan shi ana jinyarsa ne saboda raunukan da ya samu a lokacin tafiyar da ya yi.
Ya shaida masa cewa ya samu matsala da ƙwaƙwalwarsa sanadiyyar wahalar da ya sha a hanya.

"Kada ka yarda ka zama mabaraci"
Sa’eqa Najib ta ce bayan tafiyar mijinta, dole ta bar gidan da suke zama ta nemi wani gidan haya mai sauƙi ita da 'ya'yanta biyar.
Daga nan sai ta fara aiki a matsayin ƙaramar ma’aikaciya a wani kamfani mai zaman kansa inda ake biyanta ɗan ƙanƙanin albashi.
Da wannan ne ta riƙa ɗaukar nauyin kanta da 'ya'yanta.
Ta ce a wasu lokuta sukan samu abinci daidai gwargwado, amma wasu lokutan sukan ci abinci ne sau ɗaya a rana.
Haka nan akwai lokutan da akan bi ta bashin kuɗin makarantar yara na tsawon watanni, kuma babu taimako da ta samu daga wani.
Ta ce a wani lokaci ma ta gaza biyan kuɗin haya a gidan da take zama na tsawon wata shida, abin da ya sanya mai gidan ya ƙwace mata wasu daga cikin kayanta, amma daga baya ta karɓa bayan biyan kuɗin.

Daga mai kula da gidan abinci zuwa mai shagon abinci
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Sa’eqa ta ci gaba da tafiyar da rayuwarta a haka ba tare da karaya ba. Bayan wani lokaci ne ta haɗu da wani ɗan kasuwa wanda ke da aniyar buɗe gidan sayar da kayan maƙulashe, inda ya bai wa Sa’eqa aikin kula da sana’ar.
Ta ce duk da cewa ba ta ƙware a ɓangaren sayar da irin wannan abinci ba, ta yi ta ƙoƙari domin ganin ba ta gaza ba.
Ta ce ta yi amfani da ƙwarewarta a matsayin matar aure wadda ke dafa wa iyalanta abinci, wajen ganin ta tafiyar da lamurran sabon wurin.
Duk da cewa Shakargarh yanki ne da babu cigaba mai yawa, ta rinƙa ɗaukan abin da take haɗawa a kai tana sayarwa a bakin titi har sana’ar tata ta zauna sosai.
Yanzu Sa’eqa ta kwashe shekara uku tana tafiyar da ɗakin abincin, yanzu haka ta tashi daga matsayin mai kula da shagon zuwa ɗaya daga cikin waɗanda suka mallake shi.
Yawancin waɗanda ke aiki a matsayin masu kai abinci a shagon nata ƴan mata ne waɗanda suka fito daga gidajen masu ƙaramin ƙarfi.
A tsawon wannan lokaci, Sa’eqa ta samu nasarar sayen fili, inda ta gina gidan da a yanzu take zaune tare da ƴaƴanta, kuma ƴaƴan na zuwa makaranta mai kyawu.

"Ko da miji ko babu yanzu ɗaya ne a gare ni"
Sa’eqa ta ce a yanzu 'ya'yanta na gaisawa da mahaifinsu ta manhajar WhatsApp, sai dai duk da haka har yanzu ba ya turo musu wani tallafi ko kuɗin tafiyar da lamurran gida ko na makaranta, domin duk wannan tsawon lokaci da ya kwashe har yanzu yana Italiya.
Sannan bai samu takardar zama bisa ƙa’ida ba.
Ta ce a lokacin da mijin nata ya tsallake ya tafi ci-rani tana da kimanin shekara 29, inda a haka ta ci gaba da ɗawainiya da 'ya'yanta biyar.
Sa’eqa ta sadaukar da rayuwarta da duk wani jin daɗi domin gina 'ya'yanta a tsawon wannan lokaci, yanzu ta ce burinta ya cika game da irin kulawar da take son bai wa yaran nata.
Yanzu Sa’eqa ta ce tana shirin ɗaukar nauyin babbar 'yarta zuwa Portugal domin ci gaba da karatu.
A cewarta, yanzu ba ta tunanin mijinta ko kaɗan saboda irin wahalar da ta sha “yanzu ko da shi, ko babu shi duk ɗaya ne a wurina.”
Ta haifi ƙaramin ɗanta ne daidai lokacin da mijin nata ya tafi ci-rani, yanzu shekarun yaron 12.
Ta ce 'ya'yanta sun yi rashin irin ƙaunar da uba ke nuna wa 'ya'yansa da kuma soyayyar da ya kamata uwa ta nuna wa 'ya'yanta.














