Ƴakin Ukraine: Kwamandan dakarun sojojin hayar Rasha na neman mafaka a Norway

Asalin hoton, GULAGU.NET
Wani tsohon kwamandan kungiyar sojojin hayan Rasha ta Wagner, ya ce yana neman zaman mafaka a Norway bayan barin kungiyar.
Andrey Medvedev mai shekara 26, ya tsallaka iyaka zuwa Norway a Juma'a da ta gabata, wajen da jami'an tsaron kan iyaka suka tsare shi.
Ana rike da shi a halin yanzu a yankin Oslo, inda yake fuskantar zargin shiga ƙasar ta Norway ba bisa ka'ida ba, a cewar lauyansa Brynjulf Risnes, yayin tattaunawa da BBC.
Mr Risnes ya ce wanda yake karewa ya bar kungiyar Wagner ne bayan fafatawa a ƴakin Ukraine. Wani jami'in tsaron kan iyaka ɗan Norway, ya faɗa wa BBC cewa an tsare wani ɗan Rasha bayan tsallake iyakar ƙasar mai nisan kilomita 198 da Rasha.
Sai dai, ya ce bai kara wani martani ba saboda dalilai na tsaro.
Shugaban 'yan sanda a yankin Finnmark na Norway, Tarjei Sirma-Tellefsen, ya ce jami'an samamen kan iyaka sun tsare wani wadda ya ce ya nemi buƙatar a bashi mafaka.
Sai dai kungiyar kare hakkin ɗan adam ta Rasha mai suna Gulagu.net, waɗanda suka taimaki mista Medvedev , sun tabbatar da cewa sun san shi.
Ana da yakinin cewa tserewarsa ita ce abu na farko da aka ji daga kungiyar ta sojoji da ke komawa zuwa ƙasashen yamma.
Wanda ya kirkiro da kungiyar kare hakkin ɗan adam ta Gulagu.net, Vladimir Osechkin, ya faɗa wa BBC cewa mista Medvedev, ya shiga kungiyar Wagner ne a watan Yulin 2022 a kan kwantiragin watanni huɗu, sai dai, ya tsere bayan ganin abubunwa take 'yancin ɗan adam da aikata laifukan ƴaki lokacin da yake aiki da kungiyar a Ukraine.
Ya ce mista Medvedev tsohon soja ne a rundunar sojin Rasha, inda daga baya aka tura shi gidan yari tsakanin shekara ta 2017 zuwa 2018, kafin ya shiga kungiyar Wagner.
Ya kasance shi ne mai lura da rundunonin Wagner a Ukraine, inda kungiyar take aike mi shi dakaru 30 zuwa 40 a kowane mako, a cewar mista Osechkin.
A wani hoton bidiyo da kungiyar Gulagu.net ta wallafa a kafofinta na sada zumunta, mista Medvedev ya ce ya tsere daga Ukraine ne a watan Nuwamba bayan samun labarin cewa kungiyar Wagner za ta tsawaita zamansa.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Bayan shafe watanni biyu a karkashin ƙasa a Rasha, daga nan ya tsallake iyaka zuwa Norway a mako da ya gabata.
Mista Risnes ya ce wanda yake karewa shi ma ya ga laifukan yaki daban-daban yayin faɗa a Ukraine, wanda ya kunshi 'ganin kisan waɗanda suka tsere' da wasu jami'an cikin gida na kungiyar Wagner ke yi.
"Yana ganin an yaudare shi, saboda haka ya yanke shawarar tafiya,'' a cewar Mista Risnes.
Ya kara da cewa yana da da yakinin mista Medvedev ya naɗi wasu hujjoji na laifukan ƴaki da aka aikata a Ukraine zuwa Norway, sannan yana da niyyar bai wa kungiyoyin da ke binciken laifukan ƴaki bayanai a makonni masu zuwa.
A martaninsa, shugaban kungiyar Wagner, Yevgeny Prigozhin, ya yi watsi da zarge-zargen.
A wata sanarwa da ɗaya daga cikin kamfanoninsa ya fitar, Prigozhin, ya ce abin ya ba shi dariya, inda ya ce mista Medvedev bai san me yake yi ba, kuma shi ɗan Norway ne.
Prigozhin ya kuma zarge shi da laifin 'cin zarafin fursunoni' da kuma cewa tsohon jami'in nasa yana da 'haɗarin gaske'.
Sai dai, mista Risnes ya faɗa wa BBC cewa kalaman na shugaban Wagner ba gaskiya ba ne.
Jami'ai a Birtaniya sun ce suna da ƴakinin cewa kungiyar Wagner na da dakaru da ya kai kashi 10 a cikin sojojin Rasha da ke ƴaki a Ukraine, kuma sun taka rawa wajen taimakawa sojin Moscow karbe iko da garin Soledar da ke gabashin yankin Donbas a mako da ya gabata.
Dubban sojojin kungiyar sun kasance fursunoni da suka fito daga gidan yari. Mista Prigozhin - wadda tsohon mai laifi ne - ya yi wa sojojinsa alkawarin basu 'yanci saboda aiki na watanni shida da suka yi a Ukraine.
Kafin Rasha ta mamayi Ukraine, sojojin Wagner basu da yawa. An yi imanin cewa yawancinsu kwararrun tsoffin soji ne, wanda kuma ya kunshi wasu daga dakaru na musamman na Rasha.
An yi imanin cewa tun 2015, kungiyar ta fara tura dakarunta zuwa Syria da Libya da Mali da kuma Jamhuriyar Tsakiyar Afirka.











