INEC ta soma raba katin zaɓe na dindindin Najeriya

INEC Chair

Hukumar zaɓe mai zaman kanta a Najeriya ta fara raba katin zaɓe na din-din-din ga wasu daga cikin masu zaɓe a ƙasar. Hukumar ta ce waɗanda za a bai wa rijistar su ne mutanen da suka ba da sunayensu daga farkon 2022, zuwa lokacin da aka rufe aikin a watan Yuli. Zainab Aminu, jami'ar hukumar ta sanar da BBC cewa "Kamar yadda aka sani, an fara wannan aikin rajistar ne a watan Yulin 2021, aka yi zuwa watan Disamba - zango na daya da na biyu ke nan - kuma an samar da katunansu kuma tuni aka fara raba su."

Ta ce za a raba katunan ne daga ranar 12 ga watan Disambar 2022 zuwa 22 ga watan Janairun 2023, kuma za a yi rabon ne a dukkan kananan hukumomin Najeriya 774.

"Daga ranar 6 ga watan Janairun shekarar 2023 zuwa 15 ga watan, hukumar zabe za ta fadada raba katunan zaben zuwa dukkan gundumomi 8,809 da ke fadin kasar nan."

Daga ranar 15 zuwa 22 ga watan na Janairu, za a sake komawa ofisoshin hukumar zaben da ke jihohi domin ci gaba da raba katunan.

INEC Voter machine

Wadanda suka cancanci karbar katunan zabe

  • Wadanda suka cika shekara 18 da haihuwa kuma suka yi rajista a karon farko.
  • Wadanda suka bukaci a sauya musu rumfar zabensu daga wata rumfa zuwa wata rumfar.
  • Akwai wadanda katunansu suka lalace har suka kai da na'ura ba ta iya karanta su.
  • Sai kuma wadanda katunansu suka bata.

Zainab Aminu ta kuma bayyana irin shaidar da masu neman karbar katunan zabensu za su gabatar yayin da suka hallara a ofisoshin hukumar.

"Ana bukatar mutum ya tafi da wata takardar zabe ta wucin gadi da aka ba duk wanda yayi rajista. Idan babu wannan takardar wucin gadin, ana iya amfani da lambar da ke jikin kowane katin zabe mai suna Voter Identification Number."

Sai dai ta ce ko babu lambar, mutum na iya zuwa da kansa domin jami'an hukumar su nemo katin nasa.

"E, wannan haka yake, amma mun fi son a taho da takardar wucin gadin ko lambar ta VIN saboda saukin dubawa," in ji Zainab Aminu.