Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Halin da ƴan kasuwar Arewacin Najeriya ke ciki a Kudu
Ƙungiyar ƴan kasuwar dabbobi da ke Lobanta Garke na jihar Abia, ta ce 'ƴa'ƴanta suna fuskantar barazana a jihar da ke Kudancin Najeriya, inda gwamnati ta basu wa'adin kwana 14 su bar kasuwar da suke sana'a.
Wannan ne ya sa ƙungiyar ta tashi tsaye don neman mafita kan batun, inda ta fara tuntuɓar ƙungiyoyi da hukumomi, don ganin an ɗauki matakan da suka dace.
Buba Abdullahi Kedemure wanda ya jagoranci ƴan kasuwar a ganawar da suka yi da ƙungiyar Northern Consensus Movement (NCM) a Kaduna, ya bayyana damuwa dangane da halin da ƴan asalin arewacin Najeriya ke ciki a shiyyar, lamarin da ya ce ya zama wajibi a dauki mataki.
Ya ce ''mutanen mu suna cikin fargaba. An zo an rusa mana gidaje, an rusa mana shaguna, matanmu suna kwana a makarantu, ba yadda za su yi. Manyan mu na Arewa su sa baki a cikin wannan lamarin.
Najeriya ƙasa ɗaya ce, kowa yana da damar ya zauna inda zai yi kasuwanci, tunda mu dai muna son zaman lafiya kuma muna son mu ci gaba da gudanar da harkokin mu na kasuwanci.
Dukkan mu da ka gan mu a nan, waɗan su a can aka haife su, waɗan su a can aka ahifi iyayayensu.''
A nasu ɓangaren, shugabannin ƙungiyar Northern Consensus Movement sun yi kira ga gwamnati da sauran shugabannin Arewacin Najeriya su ɗauki matakan gaggawa na don gudun kada ƙaramar magana ta zamo babba.
Shugaban ƙungiyar, Auwal Abdullahi Aliyu ya ce ''ba mu yarda da wannan ba kuma muna kira ga shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ƴan Arewa na neman kariyar shi, musamman ƴan Arewa da ke zaune a jihohin Inyamurai , suna neman ya shigo cikin wannan al'amari.
Duk jami'an tsaro da ya kamata su shigo, su shigo domin abinda muke gudu wa ƙasar shi ne, ka kore su, ka ƙona can, su ma fa suna da mutanen su a nan.''
Ya ƙara da cewa an san jama'ar Arewa da bin doka da oda don haka za su bi duk wata hanyar da doka ta yarda da ita don shawo kan wannan matsala.
''za mu je mu ga shugaban majalisar gwamnonin Arewacoin Najeriya, gwamnan jihar Gombe, da sarkin musulmi , za mu sanar da manyan jami'an tsaro cewa ga fa aboinn da ke faruwa, su ja hankalin gwamnonin kudu maso Gabas domin wannan muna kallon shi ne a matsayin wata hanya da za a kawo tashin-tashina a Arewa.''
To sai dai gwamnatin jihar Abia ta musanta cewa tana yunkurin korar ƴan Arewa ne daga jihar, ta kuma bayyana cewa ta ɗauki matakin ne domin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’ummarta.
Gwamnatin ta ce wurin ya zamo tamkar wata mattara ce ta masu aikata manyan laifuka, har ta kai ga a wurin ake kai kuɗin fansa ga masu garkuwa da mutane, don haka ta ɗauki matakin da ya dace don korar su daga wajen.
Sai dai ƴan kasuwar dabbobin sun musanta wannan zargi, suna masu cewa babu irin wannan labari daga ɓangaren su.
Yan kasuwar dai sun ce sun jima suna samun barazana sakamakon rashin jituwa tsakanin yan kasuwar arewacin Najeriyar da jama'ar kudancin kasar inda har ta kan kai ga an kona musu dukiyoyinsu, abun da ya sa da dama ke korafi.
A baya dai yan kasuwar sun sha dakatar da harkokinsu a can domin ganin mahukunta sun dauki matakin kare su.
Lamarin ya kara kamari ne tun bayan zafafar ayyukan 'yan tawaye a wasu daga cikin jihohin da ke kudancin Najeriyar.