Halin da ake ciki a Gaza wata shida da fara yaƙi

Palestinians look on at the site of an Israeli strike on a house in the southern Gaza Strip on 4 April 2024

Asalin hoton, Reuters

    • Marubuci, Soha Ibrahim
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Arabic

Duk da kudurin da kwamitin tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya ya bijiro da shi na buƙatar gaggauta tsagaita wuta da kuma sakin waɗanda ake garkuwa da su a Gaza a watan da ya gabata, ci gaba da lugudan wuta a yankin, wanda ya ke ci gaba da faruwa na tsawon watanni shida da suka wuce, hakan bai nuna cewa za a rage kai farmaki ba, kuma ba a samu raguwa ba na yawan waɗanda ke mutuwa da kuma jikkata.

Yaƙin da ake ci gaba da yi ya lalata ɗaukacin ababen more rayuwa a Zirin Gaza, inda gine-gine suka dawo kangaye, da kuma tilastawa mazauna zirin tserewa daga kudanci zuwa birnin Rafah, abin da ya janyo fargaba kan yiwuwar faɗa wa yunwa, kamar yadda wani rahoton MDD ya yi gargaɗi a watan da ya gabata.

Yaƙin ya ɓarke ne biyo bayan wani hari da Hamas ta kai ranar 7 ga watan Oktoba, wanda ya kashe mutum 1,200 akasari fararen hula, a cewar alkaluman da Isra'ila ta fitar.

Birtaniya, Amurka da kuma Tarayyar Turai sun ayyana Hamas a matsayin ƙungiyar ƴan ta'adda.

Yayin harin, an yi garkuwa da mutum 253. Kusan 130 ne ake ci gaba da rike da su a Gaza, inda aka yi tsammanin cewa 34 daga ciki sun mutu, a cewar jami'an Isra'ila.

Wasu dakarun Isra'ila 600 sun mutu tun harin na ranar 7 ga watan Oktoba, a cewar sojojin ƙasar, inda aka kashe aƙalla 256 tun bayan da Isra'ila ta kaddamar da farmaki ta ƙasa a Gaza a karshen watan Oktoba.

Ya zuwa rana ta 175 da fara yaƙin, aƙalla mutum 32,623 ne aka kashe sannan aka jikkata sama da 75, 092, a cewar hukumar kula da ayyukan agaji na MDD (OCHA).

Palestinian and Israeli deaths

Sannan zuwa rana ta 178 da soma rikicin, aƙalla mutum 32,916 - waɗanda yawancisu mata da ƙananan yara ne - aka kashe, a cewar ma'aikatar lafiya karkashin ikon Hamas a Zirin Gaza.

A cewar wani rahoton MDD da aka wallafa ranar 1 ga watan Maris, ya kiyasta cewa mata 9,000 aka ruwaito sojojin Isra'ila sun kashe a Gaza.

A cewar rahoton, alkaluman za su iya fin haka, saboda ana tunanin cewa gawawwakin da yawa na binne karkashin ɓaraguzai.

A cewar asusun kula da ƙananan yara na MDD Unicef, ta ce sama da yara 13,000 ne aka kashe a Gaza tun fara yaƙin.

Wasu ƴan siyasa, kamar shugaban Amurka Joe Biden, a baya sun sha aza ayar tambaya kan alkaluman da ma'aikatar lafiya ta Falasɗinawa ke fitar wa, sai dai Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce ta yi imanin cewa alkaluman waɗanda za a dogara da su ne.

'Bala'in matsalar ƙarancin abinci'

Aid lorries going into Gaza
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A cewar MDD, an tilastawa kashi 85 na al'ummar Gaza da aka yi wa ƙawanya cikin sama da miliyan 2.3 barin muhllansu saboda halin da ake ciki a Gaza, wanda ya kunshi ragargazar gine-gine da kuma janyo karancin abinci, ruwa, man fetur da kuma wutar lantarki.

A watan da ya wuce, wani rahoto da wata ƙungiyar samar da abinci ta IPC ta fitar wadda kuma ke samar wa gwamnatoci, MDD da kuma ƙungiyoyin agaji da bayanai na auna mizanin yunwa - ta yi gargaɗin cewa ana dab da faɗawa yunwa a Gaza.

"Ana sa ran rabin al'ummar Zirin Gaza (miliyan 1.11) za su faɗa yanayi na bala'i" idan aka zo ga batun samar da abinci da kuma yiwuwar faɗa wa cikin yunwa, in ji ta.

Isra'ila na kallon bayanan na MDD da cewa ba cikakku bane, kuma ta ce ƙungiyoyin agaji na MDD sun kasa rarraba agajin da ake kai wa kowace rana.

"A kowane lokaci, akwai ɗaruruwan motocin dakon kaya da aka rike a mashigar Kerem Shalom na Gaza bayan kammala duba su daga jami'an Isra'ila," in ji shugaban sashen kula da harkokin fararen hula na ma'aikatar tsaro a Isra'ila (Cogat) - wadda ke kula da harkokin fararen hula a Gaɓar Yamma da kuma Gaza da aka yi wa kawanya.

Ta ce "Isra'ila na sane da abin da yaƙin zai je ya haifar kan al'umma a Gaza", kuma ta musanta zarge-zargen cewa da gangan take yi don jefa al'ummar Gaza cikin matsalar ƙarancin abinci.

Kiraye-kiraye na ƙaruwa akan buƙatar buɗe hanyar shiga Gaza da kuma ba da damar shigar da kayan agaji ba tare da wani tarnaki ba, wanda, a cewar MDD, ana shigar da motocin dakon kaya aƙalla 500 zuwa Gaza a kowace rana kafin fara yaƙi.

A watan Maris, an samu motocin agaji 161 da ke shiga yankin Gaza a kowace rana, a cewar Hukumar MDD mai agaza wa Falasɗinawa ta UNRWA, wadda ke gudanar da babban aikin agaji a Gaza.

Isra'ila ta ce ba a kayyade yawan agajin jin kai da za a shigar Zirin Gaza ba.

Mutuwar ƴan jarida da ma'aikatan agaji

Deaths of journalists and aid workers

A cewar ƙungiyar kare hakkin ƴan jarida ta (IFJ), ta ce an kashe ƴan jarida da kwararru kan harkokin yaɗa labarai 99 waɗanda suka kasance Falasɗinawa, da ƴan Isra'ila huɗu, da kuma ƴan Lebanon uku.

Akwai kuma rahotannin jikkatar ƴan jarida 16, da ɓacewar guda huɗu, da kuma tsare 25 yayin da suke bakin aiki a Gaza, kamar yadda Kwamitin Kare Hakkin Ƴan Jarida (CPJ) ta ruwaito.

Ƴa jarida waɗanda ke ƙoƙarin aiko da rahotanni daga Gaza za su iya shiga zirin ne kawai idan suka bi ayarin sojoji Isra'ila kuma suka amince da sharuɗan da sojojin suka gindaya musu, wanda ya kunshi kasancewa tare da dakarun Isra'ila da kuma ba da rahotanni a duba kafin a wallafa.

Sama da ma'aikatan agaji 196 ne aka kashe a Gaza tun watan Oktoba, a cewar ƙungiyar agaji mai tattara bayanan tsaro da Amurka ke tallafawa, wadda ta tattara irin alkaluman cin zarafin da aka yi wa jami'an agaji.

Yawancin waɗanda aka kashe tun fara yaƙin wanda ya ɓarke watanni shida da suka wuce, sun kasance suna aiki da hukumar MDD mai agaza wa Falasɗinawa ta UNRWA, wadda ke sahun gaba a gudanar da harkokin agaji a Gaza.

Barazanar farmaki ta ƙasa

Map of Gaza

A tsawon makonni, Isra'ila na ci gaba da barazana kan kaddamar da farmaki ta ƙasa a Rafah, wanda ke kudancin Zirin Gaza, a kan iyaka da Masar wadda ke rufe a yanzu.

Yankin ya kasance wurin ƴan gudun hijira ga Falasɗinawa sama da miliyan 1.5, waɗanda yawanci aka ɗaiɗaita daga sauran yankuna a Zirin.

Jami'an MDD sun nuna fargaba kan yiwuwar faɗa wa bala'in matsalar jin kai "fiye da tunanin mutane" idan aka samu gagarumin mamayar sojojin Isra'ila zuwa cikin Rafah.

A Isra'ila, matsin lamba na ƙaruwa kan Firaminista Benjamin Netanyahu na amincewa da yarjejeniyar tsagaita wuta da za ta kai ga sakin gomman waɗanda ake garkuwa da su a Gaza da kuma gudanar da zaɓuka.

Dubban Isra'ilawa ne suka fantsama tsakiyar Birnin Kudus, a wata gagarumar zanga-zangar nuna adawa da gwamnati tun bayan ɓarkewar yaƙi a watan Oktoba.

Masu zangaz-zangar sun nuna ɓacin ransu kan yadda ake tafiyar da yaƙin da kuma sukar gwamnatin Isra'ila saboda kasa ceto ko kuma sakin dukkan waɗanda ake garkuwa da su.