Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Daga gidan yari zuwa fadar shugaban ƙasa: Wane ne sabon shugaban Madagascar?
- Marubuci, Wedaeli Chibelushi
- Marubuci, Omega Rakotomalala
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Monitoring
- Marubuci, Sammy Awami
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Africa
- Aiko rahoto daga, Antananarivo
- Lokacin karatu: Minti 3
Idan da za a tambayi mutane game da Kanar Michael Randrianirina a tsibirin Madagascar kafin ƙarshen makon da ya gabata, da yawanci ba za su san shi ba.
Amma cikin kwanaki uku kacal, ya zama mutum mafi ƙarfi a ƙasar.
Ƙarfin Randrianirina ya fara ne a ranar Asabar, lokacin da a matsayinsa na shugaban rundunar sojojin CAPSAT - wani sashe na musamman na rundunar ƙasar - ya jagoranci dakarunsa zuwa tsakiyar babban birnin, inda dubban masu zanga-zanga ke neman shugaban ƙasar ya yi murabus.
Bayan tsohon shugaban ƙasa Andry Rajoelina ya gudu daga birnin, kuma majalisar dokoki ta kaɗa ƙuri'ar tsige shi. Randrianirina, wanda ke da shekara 51 a duniya, ya tsaya gaban fadar shugaban ƙasa ya sanar da manema labarai cewa rundunar sojin ƙasar ta ƙwace mulki.
Daga bisani kotun tsarin mulkin ƙasar ta tabbatar da shi a matsayin sabon shugaban ƙasar, duk da cewa Rajoelina har yanzu yana cewa shi ne shugaban ƙasa na gaskiya.
Randrianirina dai ya kasance mutum ne da ba a san abubuwa da dama game da shi ba duk kuwa da matsayinsa a rundunar sojin ƙasar.
Wane ne Randrianirina?
Abin da aka sani shi shi ne cewa an haife shi a ƙauyen Sevohipoty da ke yankin kudancin Androy.
Ya taɓa zama gwamnan Androy daga shekarar 2016 zuwa 2018 a lokacin mulkin tsohon shugaban ƙasa Hery Rajaonarimampianina.
Daga nan ya zama shugaban bataliyar sojoji a birnin Toliara, inda ya yi aiki har zuwa 2022.
Randrianirina ya kasance mai sukar Rajoelina, wanda shi ma ya ƙwace mulki ta hanyar juyin mulki a 2009 kuma ya sauka a shekarar 2013, sannan ya koma kan mulki bayan ya lashe zaɓe a 2018.
A watan Nuwambar 2023, an kai Randrianirina gidan yari wanda ke da tsaro sosai saboda a wurin ne ake ajiye manyan masu laifi ba tare da yi masa shari'a ba, bisa zargin tayar da fitina da shirya juyin mulki.
A lokacin, ɗalibai da sojoji da 'yan siyasa da dama sun yi zargin cewa an tsare shi ne bisa dalilan siyasa, kuma aka sake shi a watan Fabrairun 2024.
Kafin ya sanar da ƙwace mulki a ranar Talata, Randrianirina ya shaida wa BBC cewa shi kawai "bawan jama'a ne yayin da ya nuna natsuwa da fara'a da ƙwarin gwiwa amma ba girman kai ba.
Wani ɗan jarida na Malagasy mai suna Rivonala Razafison ya bayyana shi da cewa mutum ne mai sauƙin kai kuma jarumi ne mai gaskiya kuma mai kishin ƙasa.
Randrianirina kuma yana da ra'ayi kan yadda Faransa, tsohuwar mulkin mallakar Madagascar wadda ta samu yanci a 1960, har yanzu ke tasiri a ƙasar.
Lokacin da BBC ta ba shi damar bayar da amsa da harshen Faransanci, ya ce: "Me ya sa ba zan yi magana da harshena na Malagasy ba?" inda ya ƙara da cewa ba ya son ɗaukaka harshen ƙasar da ta yi musu mulkin mallaka.
Shugaban CAPSAT ɗin ya ce bunkasar jin daɗin al'umma ce babbar manufarsa, musamman a ƙasar da sama da kashi 75 na mutane ke rayuwa cikin talauci.
Ya bayyana cewa sojoji za su jagoranci ƙasar na tsawon shekaru biyu tare da gwamnati ta farar hula kafin a gudanar da zaɓe.
Rahotanni daga Reuters sun ce ana sa ran za a rantsar da Randrianirina cikin kwanaki biyu masu zuwa, a wani biki da zai zama kammalallen labarin yadda mutumin da ba a san abubuwa sosai game da shi ba ya zama shugaban ƙasa cikin kwanaki kaɗan.