Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda wani magidanci ya cinna wa matarsa wuta a Anambra
Gwamnatin jihar Anambra ta yi allawadai da wani magidanci mai suna Sunday Nwaka wanda aka ruwaito ya cinna wa matarsa - Blessing Nwaka - wuta a garin Abagana da ke jihar.
Cikin wani jawabi da kwamishiniyar mata ta jihar, Ify Obinabo ta yi a lokacin da ta ziyarci iyalan marigayiyar, ta ce gwamnatin jihar za ta tabbatar da adalci a kan batun, kuma mijin matar zai girbi abin da ya shuka.
A daya gefen, shugaban karamar hukumar Njikoka - inda lamarin ya faru - Domini Ononiba ya alkawarta cewa gwamnatin jihar Anambra za ta tabbatar da 'ya'yan marigayiyar sun samun cikakkiyar kulawa.
A ranar Talata wani bidiyo ya bulla a shafukan sada zumunta, wanda yake nuna yadda Blessing Nwaka - wadda ita ce ke daukar dawainiyar iyalinsu - ta kone sosai sakamakon wutar da mijin nata ya cinna mata.
Abin da ya sa na cinna wa matata wuta - Mijinta
Mista Nwanna, mutumin da ake zargi da cinna wa matar tasa wutar a garin Abagana na jihar Anambra, ya amince da laifin sannan ya bayyana dalilin da ya sa ya aikata kisan kan.
Mutumin, wanda yanzu haka, ke hannun hukumar 'yansandan jihar Anambra, ya ce lamarin ya faru ne bayan da suka samu sabani da juna har ta kai su ga fada.
A lokacin da kwamishiniyar matan jihar, Ify Ibinabo ta tambaye shi, sai ya ce fadan da suka yi ne ya janyo musu haka.
"Abin da ya faru shi ne muna fada ne da matata, sai ta dauko makami ta dokeni da shi, sai na duba gefe na kuma ga jarkar fetur, sai na yi sauri na daukota na watsa mata na kuma cinna mata wuta''.
Sai dai ya ce bayan da ya ga wutar ta kama matar ganga-ganta ya yi nadama.
"Amma a lokacin da na ganta tana ci da wuta, na yi kokarin kashe wutar ta hanyar watsa mata ruwa, amma kusan duka jikinta ya kone''.
Da aka tambaye shi abin da ya haifar musu da rigimar da ta kai su ga fadan, sai Nwanna ya ce matar tasa kan fita daga gida ba tare da sanar da shi ba, kuma ba ta komawa gida sai tsakar dare.
"Takan fita daga gida ba tare da sanar da ni inda za ta je ba, sannan ba ta tashi dawowa sai wajen karfe 11 zuwa 12 na dare.''
Ya ce bai aikata abin da ya yi ba, da nufin kashe ta, saboda yana so da kaunarta matuka.
Bayan faruwar lamarin matar da mutu a asibiti, ranar Laraba da safe, sakamakon raunukan da ta ji a kunar.
Rundunar 'yansandan jihar dai ta ce tana ci gaba da gudanar da binkice kan lamarin.
'Yansandan sun ce bayanan da suka samu, sun nuna cewa ba wannan ne karon farko da mutumin ke barazanar kashe matar tasa ba, kuma 'ya'yansu sun fada wa 'yansandan cewa a baya mahaifin nasu ya taba dukan mahaifiyarsu da kwalba.
'Yansandan sun kuma shawarci ma'aurata cewa aure ba abu ne na tilastawa ba, don haka idan ma'aurata sun gaji da juna, abin da ya fi kyau shi ne su rabu da juna, maimakon su ci gaba da zama da juna har wani ta kashe wani.
Makwabtansu, sun ce ma'auratan sun saba rigima da juna, inda suka ce a baya ma'auratan sun yi zaman gudun hijira a birnin Jos na jihar Plateau, kafin su koma Anambra a baya-bayan nan.
A baya-bayan nan Najeriya na fuskantar karuwar rigingimu tsakanin ma'aurata.
Kungiyoyin kare hakkin dan'adam sun sha yin kira ga gwamnati ta tabbatar da hukunta wadanda aka samu da laifin cuzguna wa matansu, domin rage matsalar.