Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Laifuka biyar da za su sa a hana ɗan Najeriya shiga Amurka
Ofishin jakadancin Amurka a Najeriya ya fitar da wani ƙarin bayani kan ƴan Najeriya da ke son zuwa Amurka da kuma waɗanda ke zaune a can.
Ofishin ya ce yana koƙarin ganin ya yi yaƙi da zamba da kuma shiga ƙasar ba bisa ƙa'ida ba.
A wani bayani da ofishin jakadancin ya wallafa a shafin sada zumunta, ya ce za a haramta wa duk wani da aka kama da laifin aikata rashin gaskiya wajen samun takardar shiga Amurka - shiga ƙasar har abada.
Wannan bayani shi ne mataki na baya-bayan nan da Amurkar ta ɗauka a yunƙurinta na daƙile kwararar baƙin haure zuwa cikin ƙasar.
"Ƙasar da ba ta da tsaron iyaka ba ƙasa ba ce", a cewar sanarwar.
Haka nan bayanin ya ce hukumomi sun sha alwashin gurfanar da duk wanda aka kama da aikata rashin gaskiya wajen neman biza da kuma duk wanda ya ba su masauki.
Ko a makon da ya gabata Amurka ta gargadi ƴan ƙasar waje da ke cikin ƙasar game da wuce lokacin da bizarsu ta tanada, da kuma duk mai niyyar yin hakan.
Ofishin jakadanci Amurka ya ce duk mutumin da ya wuce lokacin da doka ta ɗiba masa na zama a Amurka to zai fuskanci hukunci.
Amfani da takardun bogi wajen neman biza
Yin ƙarya ko zamba zai iya janyo wa mutum babbar matsala a wajen jami'an shige da fice na Amurka, abin da zai janyo a hana mutum samun biza da mayar da shi ƙasarsa da kuma haramta masa shiga Amurka har abada.
Jami'an shige da fice ba sa wasa da batun yi musu ƙarya, inda ko ɗan kuskure kaɗan mutum ya yi zai iya zama masa babbar matsala.
Wadannan su ne abubuwan da za su iya janyo wa mutum hukunci mai tsauri a wajen ƙoƙarin shiga Amurka.
Karkashin dokokin shige da fice na Amurka, aikata zamba da kuma yin ƙarya na nufin lokacin da mutum ya bayar da bayanan ƙarya ko kuma rashin ƙarin bayani don samun alfanu a wajen neman biza.
Wani ɓangare na tsarin shige da fice na Amurka ya bayyana cewa babu wani ɗan wata ƙasa da za a ba ri "da ya yi ƙarya cikin takardunsa wajen neman biza ko kuma wani abu" ya shiga Amurka.
Haka kuma, tsarin ya bayyana cewa duk wanda aka samu da laifin yin ƙaryar cewa shi ɗan Amurka ne a wajen jami'an shige da fice domin samun alfanu, zai fuskanci haramta masa shiga ƙasar na har abada.
ƙarerayi 5 da za su sa a hana ɗan Najeriya shiga Amurka
- Yin ƙarya lokacin neman biza - kamar bayar da bayann aikin da mutum yake yi wanda ba na gaskiya ba.
- Amfani da shaidar yin aure ta bogi domin samun takardar ƴancin zama na dindindin.
- Gabatar da takardun bogi, kamar bayanan asusun ajiyar banki na bogi da sauransu.
- Rashin bayyana lokacin neman biza na baya.
- Rashin bayyana ainahin abin da ya kai mutum - Wannan na nufin idan mutum ya shiga Amurka ta hanyar amfani da bizar yawon buɗe sai ya ɓige da zama na dindindin.
A cewar wata sanarwa daga ofishin jakadancin Amurka a Najeriya, ta ce aikata irin waɗannan abubuwa da muka lissafa a sama, zai iya janyo wa mutum hukunci da ya haɗa da:
- Haramta shiga Amurka har abada: Abin da wannan ke nufi shi ne wanda aka haramta wa shiga Amurka na har abada, ba shi da damar samun biza ko takardar zama na dindindin, idan ba Amurkar ce ta ɗage haramcin ba.
- Hana samun biza da takardar zama na dindindin: Hukumar shige da fice ta Amurka da kuma sashen jami'an sirri na duba bukatun neman biza domin gano ko akwai rashin gaskiya. Idan suka gano wani rashin gaskiya za su yi watsi da bukatar neman bizar.
- Mayar da mutum ƙasarsa - Duk mutumin da Amurka ta samu ya aikata zamba, zai fuskanci hukuncin mayar da shi ƙasarsa ta asali.
- Zargin aikata laifuka: A nan, idan jami'an shige da fice suka samu mutum ya aikata laifi, musamman amfani da takardun ƙarya, hakan zai janyo masa hukunci mai tsauri da ya haɗa da cin tara ko kuma ɗauri a gidan yari.