Sabbin rigingimu a PDP da ke haifar da babbar barazana ga takarar Atiku

Watanni uku gabanin gudanar da manyan zaɓuka a Najeriya da alama babbar jam'iyyar hamayya ta PDP na sake tsunduma cikin ɓaraka sakamakon rashin haɗin kai tsakanin mambobinta da ke sake fitowa fili.

Takaddama da ake yawaita samu a wannan lokaci tsakanin 'ya'yan jam’iyyar ta PDP ta soma asali ne tun bayan zaɓen da Atiku Abubakar ya yi wa Ifeanyi Okowa, a matsayin mataimakinsa a takara, bayan zaɓen fitar da gwani.

Tun wancan lokaci rigingimu suka rinka kunno kai musamman tsakanin gwamnan Rivers, Nyesom Wike da ɓangaren mutumin da ke yi wa jam’iyyar takara wato Atiku Abubakar.

Mutum 12 ne aka fafata da su a zaben fitar da gwani ko da yake akwai wadanda suka janye a ranar zaɓen, abin da ya sa fafatawar ta fi zafi tsakanin Atiku Abuabakar da kuma Gwamna Wike.

Sai dai duk da cewa an gama wannan zabe kuma ‘yan takara sun amsa karbar sakamakon da kuma yin alkawarin goyon bayan Atiku Abubakar, ga dukkanin alamu lamura sun sauya a wannan lokaci.

Shin mece ce matsalar?

Zaɓen Ifeanyi Okowa a matsayin ɗan takarar mataimaki da Atiku Abubakar ya yi, kusan shi ne musababbin matsalolin da PDP ke fama da ita a wannan lokaci.

Sannan akwai batun shugaban jam’iyyar ta PDP Iyorchia Ayu da shi ma ke fuskantar adawa, da ɓangaren Wike da ke tursasa cewa lallai a sauya shi.

Sai kuma ga shi a baya bayan nan an samu wasu gwamnoni biyar da suka hada kai har suke yi wa kansu laƙabi da G-5.

Waɗannan gwamnonni da suka hada da na Rivers da Oyo da Abia da Benue da Enugu, sun yi iƙirarin cewa sun haɗa kansu ne domin ceto Najeriya.

Ya girman barazanar take?

Duk da cewa har yanzu ɓangaren Atiku na ganin yana da karfi kuma ba lallai ne wannan barazana ta yi tasiri ko nakasu ga nasararsu ba, masu sharhi kan harkokin siyasa na ganin akwai matsala babba.

Gwamnan Benue, Samuel Ortom, ya ce za su ci gaba da zama a PDP su biyar ɗin, sai dai ba za su mara wa Atiku baya ba.

Ortom ya ce ba za su goyi bayan mutumin da bai damu da kashe-kashen da ake yi a yankunansu ba, da makiyaya ke aikatawa.

Gwamnan ya ce sun gana da Wike na Rivers da Makinde na Oyo da gwamnan Abia, Okezie Ikpeazu a Landan domin cimma yarjejeniya tsakaninsu.

Gwamna Ortom wanda shi kansa ke ganin Atiku ya aikata rashin adalci kan Wike, ya ce da shi da sauran abokansa gwamnoni na neman lallai ɗan takararsu Atiku ya yi sulhu da Wike.

Waɗannan gwamnoni biyar na ganin dole ne a yi wannan tafiya da su muddin ana neman cikakken goyon-bayansu.

Sai dai rikicin PDPn ba wai kawai anan ya tsaya ba, domin ko a Bauchi Atiku na bukatar babban kalubale ganin cewa gwamna mai ci na nuna alamomin ba ya yinsa.

Wannan ya kai ga bayyanar wata taƙaddama da ta turnuƙe jam'iyyar PDP a jihar Bauchin.

Shugabanninta sun zargi wasu fitattun 'yan jihar da shisshige wa ɗan takarar shugaban ƙasarsu, Atiku Abubakar, duk da yake a can ƙasa ba sa yin PDPn.

A wata wasiƙa da shugabannin PDPn suka aika wa uwar jam'iyyar ta ƙasa, sun ja hankalin ɗan takarar da cewa ya kwana da sanin cewa waɗanda yake ja a jika daga jihar ta Bauchi, 'yan zagon ƙasa ne kawai.

Akwai mafita?

A tattaunawarsa da BBC, Farfesa Kamilu Sani Fagge masanin harkokin siyasa a Jami’ar Bayero da ke Kano, ya ce ya kamata tun farko a yi tattaunawar siyasa domin warware wannan matsala.

Farfesa Kamilu ya ce a halin yanzu gaskiya wannan yanayi babbar illa ce ga PDP, saboda cikin wadannan gwamnoni biyar akwai kudu maso kudu da kudu maso gabas da kuma tsakiyar arewacin Najeriya da duk wanda ya rasa su to zai yi wahala ya samu kasar nan baki ɗaya.

Sannan ya ce babu mamaki dama na ciki na ciki, musamman a ɓangaren Wike, da ya nuna burin takara ya kuma kashe makuɗan kuɗaɗe.

"Sauran watakil dama suma akwai jikakkiya tsakaninsu da Atiku, kuma babbar matsala ita ce dukkaninsu sun gaza nuna kwarewarsu ta siyasa, wajen shawo kan matsalolinsu a tafi tare.

"Yanzu kowa gani yake shi sarki ne, ga kuma batun biyewa mazuga.

"Idan PDP ta ci-gaba da tafiya a haka to za tayi babbar asara a zaɓe mai zuwa", in ji Farfesa.

Farfesa Kamilu ya kuma ce a tsarin dimokuraɗiyya ko mutum guda ka rasa asarar ce, yanzu ga shi Bauchi ma na rawa.

A siyasar Najeriya gwamnoni na da muhimmanci sosai ga karfi a jihohinsu.

Don haka idan har Atiku bai ɗinke ɓarakar PDP ba kafin zaɓe, tafiyar ta kasance guda, to zai yi wuya ya kai labari.

Sharhi

Masana dai a yanzu na ganin shawara ta rage ga mai shiga rijiya, domin a yanayin da abubuwa ke tafiya a PDP sulhu ne kawai abin da zai iya ceto ta a wannan lokaci.

 Sai dai duk da cewa bangaren Atiku na nuna kamar wannan ba matsala ba ce, kwararru na ganin cewa a wannan gaɓa fittina ba ta kowa ba ce, domin duk wanda ya yi saki a wannan lokaci na iya rasa damarsa a babban zaɓe.