Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Darajoji 10 na Arfah ranar Juma'a
Ba kasafai ranar Arfah ke faɗowa a ranar Juma'a ba, amma a bana za a yi tsayuwar Arfah ne a ranar Juma'a wacce ta kama 9 ga watan Zhul Hijja, wato 10 ga watan Yulin 2022.
Kamar yadda aka sani, a Musulunce Juma'a babbar rana ce mai daraja, kuma Arfah ma ta kasance rana mai daraja.
To ko waɗanne irin darajoji ne Arfah ke ƙarawa idan ta zo a ranar Juma'a?
Sheikh Dr Ibrahim Disina, wani babban malamin Islama a Najeriya ya fayyace mana hakan.
Shehin Malamin ya ce duk da cewa bai tabbata bai tabbata ba a Hadisi cewa: "Annabi SAW ya ce tana da falala, bai inganta ba cewa falalar hakan ya kai Hajji 70 ko 72 ba, amma wasu Malaman sun kalato wasu bayanai da za a iya nutsuwa da su kan ƙarin falalar idan ranar Juma'a ta zo a matsayin ranar Arfa.
End of Wasu labaran da za ku so ku karanta
1- Haduwar ranaku biyu mafiya daraja a waje guda, ranar Arfa ce mafificiyar Rana a shekara, Juma'a kuma mafificiyar Rrana cikin kwanakin mako.
2- Cikin ranar Juma'a ne ake samun wani lokacin da ake da tabbacin in ka yi addu'a a cikinsa za a amsa maka addu'arka, wannan lokacin shi ne bayan Sallar La'asar na ranar Juma'a.
A daidai wannan lokacin ne kuma wadanda ke Filin Arfa ran Jumma'ar ke yin dafifi kowa ya takarkare yana Addu'a.
3- A irin Wannan Rana ta Juma'a ne Annabi SAW ya yi tasa tsayuwar a Arfa lokacin Hajjinsa na ban kwana.
4- A daidai wannan ranar ce Musulmai a fadin duniya ke taruwa a Masallatan Juma'a don sauraron hudubobin Juma'a da Addu'o'i a garuruwansu kamar yadda Mahajjata daga fadin Duniya ke taruwa guri guda a Filin Arfa don sauraron Hudubar Arfa da yin addu'oi.
Wanda irin wannan dacewa baya faruwa sai in an sami dacewar Arfa ranar Juma'a.
5- Ranar Juma'a, ranar biki ce ga wadanda suke filin Arfa, wannan ne ma ya sa aka ce ba za su yi Azumi a ranar ba, kamar yadda ranar Juma'a ranar biki ce a kowane Mako ga mazauna gida.
6- A irin wannan ranar ce Allah ya cikawa Musulmai ni'imar da ya yi musu ta addini, da kuma bayanin kammaluwar hukunce-hukuncen shari'a.
Allah ya ambaci wannan baiwar da ni'ima cikin al-kur'ani mai girma.
7- Taron Arfa shine gangamin Musulmai mafi girma a duniya, a irin Wannan ranar ce za a Gangamin tashin al-ƙiyamah kamar yadda ya zo a Hadisin Annabi SAW.
Wannan taron tunatarwa ne ga mai hankali kan taron Al-ƙiyamah.
8- Allah ya cusa da dasawa Musulmai masu yi masa biyayya ganin girma, daraja da alfarmar ranar Juma'a da darenta, abin ya kai Mutane na tsoron yin aikin sabo a wannan lokaci.
Wannan kuma abu ne da zukatan mutane ke girmamawa.
9- Ashe yayin da ranar ta dace da ranar Arfa sai abin ya kara kambama ya habaka ya kuma kara girma a zukatan masu Imani.
10- A Ranar Arfa ce Allah ke kara saukowa ya kusanto zuwa ga bayinsa, sannan ya yi tinkaho da su wa Mala'iku sabon da yadda kowa ya yi butu-butu don neman yaddarsa.
Shi kuma Allah ya nemi mai neman gafara ya gafarta masa, mai neman rahama ya yi masa, mai bukatu kuma ya biya masa ita, in kuwa hakan ya dace da ranar Juma'a sai abin ya kara tumbatsa kasantuwar lokacin tun asali gurbin karbar addu'a ne.