Dalilai huɗu da suka sa Hamas ta kai wa Isra'ila hari

Harin da ƙungiyar Hamas ta Falasɗinu ta ƙaddamar kan Isra'ila a ranar 7 ga watan Oktoba, ba a taɓa ganin irin sa ba ta fuskar girma da tashin hankali.

Hakan ya zo ne ba zato ba tsammani amma sakamakon zaman ɗarɗar da aka shafe shekaru da dama ana yi tsakanin Isra'ila da Falasdinawa.

Hamas ta ce akwai dalilai da dama da suka haddasa harin nasu - mun duba huɗu daga cikin su.

Gaza

Zirin Gaza yanki ne mai tsawon kilomita 41 da faɗin kilomita 10 tsakanin Isra'ila da Masar da kuma tekun Bahar Rum.

Ya kasance gida ga kusan mutane miliyan 2.3 kuma ya kasance ɗaya daga cikin wurare masu cunkuson jama'a a duniya.

Ya ƙunshi yankin na Falasɗinawa tare da yankin yamma da gaɓar kogin Jordan da kuma gabashin birnin Ƙudus.

Kimanin kashi 80% na al'ummar Gaza sun dogara ne da taimakon ƙasa da ƙasa, a cewar MDD, kuma kusan mutane miliyan ɗaya ne ke dogaro da tallafin abinci na yau da kullun.

Wannan yana nufin rayuwar yau da kullun na da wahala ga mutanen da ke zama a yankin.

A cewar Majalisar Dinkin Duniya, a cikin 2021 ana samun wutar lantarki na tsawon sa'o'i 13 ne kawai a rana.

Hukumar lafiya ta duniya ta ce mutum na bukatar aƙalla lita 100 na ruwa a rana domin sha da wanka, da dafa abinci da kuma wanka. A Gaza kimanin lita 88 ne matsakaicin amfanin da ake yi da ruwa.

Isra'ila ce ke kula da sararin samaniyar Gaza da gaɓar ruwanta, tare da takaita mutane da kayan ke iya shiga da fita ta mashigin kan iyaka.

Hakazalika, Masar tana iko da masu shiga da fita ta kan iyakarta da Gaza. Suna kiyaye wannan lamari ne domin mahimmancin da ya ke da shi ga tsaro.

Yanzu, a matsayin martani ga harin da aka kai a ƙarshen mako, gwamnatin Isra'ila ta sanar da "cikakken killace" Gaza wanda ya haɗa da hana kai kayan abinci, ruwa da man fetur.

A cikin gida, Gaza ta kasance ƙarƙashin ikon Hamas tun shekara ta 2007, lokacin da ƙungiyar ta masu kishin Islama ta fatattaki dakarun da ke biyayya ga gwamnatin Falasdinu da ke mulki a lokacin, bayan wani rikici mai tsanani.

A shekara ta 2014, bayan wani dan gajeren rikici da ta yi da ƙungiyar Hamas, Isra'ila ta ayyana wani killataccen yanki da ke kewaye da Gaza domin kare kanta daga hare-haren makaman roka da kuma kiyaye kutse daga mayakan Hamas, amma yankin ya rage yawan filayen da mutane za su zauna su kuma yi noma.

Masallacin al-Aqsa

Babu alamar da ke nuni da irin takun saƙar da ake yi tsakanin Isra'ila da Falasdinawa fiye da masallacin al-Aqsa da ke gabashin birnin Kudus.

Yana da katafaren haraba da ke kan wani tudu, shi ne wuri na uku mafi tsarki a Musulunci, amma kuma wuri ne mafi tsarki ga Yahudawa, wadanda suka san shi da ''Temple Mount''.

A cikin wani faifan murya da aka fitar a lokacin da aka kai harin, Muhammad al-Deif, wanda shi ne kwamandan reshen soji na Hamas, da aka sani da rundunar al-Qassam, ya ce harin da Hamas ta kai ramuwar gayya ne kan abin da ya kira hare-haren da Isra'ila ke kai wa masallacin al-Aqsa a kullum.

Ya ce ‘yan Isra’ila “sun zagi Annabinmu a cikin harabar masallacin al-Aqsa”.

A cikin 'yan shekarun nan, 'yan Isra'ila sun kara yawan yadda suke kai ziyara a harabar masallacin, lamarin da ke matukar damun Falasdinawa.

An sha samun arangama tsakanin Falasdinawa da jami'an tsaron Isra'ila a harabar masallacin.

A cikin watan Afrilu, 'yan sandan Isra'ila sun kai farmaki kan masallacin ta hanyar amfani da gurneti da harsasai na roba bayan rikici kan gudanar da ayyukan addini a harabar.

A cikin 2021, wani hari da Isra'ila ta kai ya haifar da ɓarkewar rikici na kwanaki 11 tsakanin Isra'ila da Hamas.

Wani babban wakilin ƙungiyar Hamas a ƙasar Lebanon, Osama Hamdan, ya shaida wa BBC cewa, sun damu da manufar gwamnatin Isra'ila kan msallacin, yana mai cewa duk wani sauyi zai zama "wuce gona da iri".

Hukumomin Isra'ila sun ce sun ƙuduri aniyar kiyaye 'yancin gudanar da ibada a harabar masallacin.

Matsugunan Yahudawa

Tun bayan da Isra'ila ta mamaye yankunan bayan yaƙin 1967, yawan matsugunan Yahudawa, musamman a yankin Gaɓar yamma da kogin Jordan, na ci gaba da ƙaruwa.

Majalisar Dinkin Duniya ta kiyasta cewa kimanin Yahudawa 700,000 ne ke zaune a yankin da aka mamaye a shekarar 2022.

Majalisar Dinkin Duniya da akasarin ƙasashen duniya na ganin cewa matsugunan sun saɓa wa doka a ƙarƙashin dokokin ƙasa da ƙasa, ko da yake Isra'ila ba ta amince da hakan ba.

An samu ƙaruwar tashe-tashen hankula da masu tsattsauran ra'ayin Isra'ila ke yi kan fararen hulan Falasɗinawa a yankin Gaɓar yamma da kogin Jordan da aka mamaye a wannan shekaran, inda ake samun rahotannin rikice-rikice sama da 100 a kowane wata a cewar MDD.

Ta yi gargadin cewa an kori wasu mutane 400 daga ƙasarsu tun daga farkon shekarar 2022.

A cewar Osama Hamdan na Hamas, Falasdinawa na fargabar cewa Isra’ila na shirin korar Falasdinawa daga yankin Gaɓar yamma kogin Jordan.

Zamantakewa tsakanin 'yan Isra'ila da Larabawa

Isra'ila na gudanar da cikakiyar hulɗar diflomasiyya da wasu kasashen Larabawa guda biyu ne kacal, wato ƙasahen Masar da Jordan, bayan ƙulla yarjejeniyar zaman lafiya da su a shekarun 1979 da 1994.

Sai dai a shekarun baya-bayan nan ta fara share fagen ƙulla irin wannan yarjejeniyar da wasu muhimman ƙasashen da ke yankin kamar Hadaɗɗiyar Daular Larabawa.

A watan Satumba, Yarima mai jiran gado na Saudiyya, Mohammed bin Salman, ya shaida wa tashar talabijin ta Fox News ta Amurka cewa, ƙasarsa “a kowace rana tana ƙara kusantar” daidaita alaka da Isra’ila.

Koda yake a baya Saudiyya ta bayyana cewa duk wata yarjejeniya za ta bukaci a sami muhimmin ci gaba wajen samar da ƙasar Falasdinu, amma ƙungiyar Hamas na adawa da matakin, tana mai cewa daidaitawa zai rage matsin lamba ga Isra'ila na amincewa da buƙatun Falasdinawa.

A wani jawabi da ya yi ta gidan talbijin a ranar 7 ga watan Oktoba, shugaban ƙungiyar Hamas, Ismail Haniyeh, ya soki ƙasashen Larabawa da ke ɗaukan matsaya na sasantawa da ƙasar Isra'ila.

"Duk yarjeniyoyin daidaitawa da kuka amince da waɗannan mutanen ba za su iya magance wannan rikicin ba," in ji shi.