Yadda ni da mijina muka yanke shawarar yin soyayya da wasu mutane na daban

    • Marubuci, Marina Rossi
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Brasil
    • Aiko rahoto daga, São Paulo
  • Lokacin karatu: Minti 5

A ranar murnar cika shekara goma da yin aurensu, Dakta Ilana Elea wadda ta kasance marubuciya kuma mai koyarwa, ta bijiro da wani batu tsakaninta da mijinta wanda zai sauya rayuwar aurensu: Yin soyayya da wasu mutane na daban.

Ta kammala karatu ne a bangaren neman shawarwari na yadda ake yin jima'i a wata cibiya a Brazil, amma ta koma rayuwa a Sweden tun shekara ta 2011.

Ta kasance tana nazari kan masu yin soyayya da wasu mutanen na daban na dan lokaci, yayin da kuma take rubuta wani littafi kan jima'i.

Mijinta ya amince da batun inda suka yi murna kan haka. Shekara biyar bayan nan, ma'auratan sun kwatanta rayuwarsu a matsayin mai nasara.

Sai dai Elea ba ta yi na'am da batun sosai ba.

"Kashi uku na ma'auratan da suka amince da yin soyayya da wasu mutane na daban na zuwa karshe daga baya," in ji ta. "Sai dai hakan ba wani abun damuwa ba ne. Don haka yana da kyau a zabi abin da ya fi dacewa."

Amincewa da soyayya da wasu mutane na daban

Eleá ta amince da batun soyayya da wasu mutane na daban duk da aurenta. Lamarin na kai wa har da jima'i da mutanen muddin ma'auratan biyu sun amince da shi.

Kan wannan dalili ne ya sa kwararru ke kiransa da abin da aka amince da shi, ba kamar yadda wasu ke kallonsa ba.

"Wannan na nufin duk wata alaka wadda wadanda ke cikinta suka amince da juna, inda suke cin moriyar juna ta kowace hanya," in ji Elea.

Sai dai, ta bambanta soyayya da wasu mutane na daban da kuma alakar fiye da mutum biyu.

"Yin soyayya da wasu mutane na daban so tari na bai wa juna yin jima'ai ba tare da wani soyayya mai karfi ba. Yayin da alakar fiye da mutum biyu kuwa ta fi mayar da hankali kan shakuwa da soyayya."

Ita kanta Elea na dabbaka abin da ake kira "soyayya, nuna kauna, soyayyar jima'i da sauransu".

"Kafa ta daya na bangaren alakar mutum fiye da biyu," in ji ta. "Ba duka kafafun ba, sai dai batun shi ne ana iya yin soyayya zalla da kuma wadda za a yi don samun jima'i da mutum fiye da daya. Mijina ya fi son irin wannan salon soyayya. Muna yawan magana kan haka."

Tunani kan soyayyarka

Elea ta ce abin da ya fi dacewa ga ma'auratan da suka amince da yin soyayya da wasu mutane na daban, shi ne kada a tambayi juna ko fada wa juna wani abu kan batun.

"Ba na son sanin abin da yake ciki. Kada ka fadamin, ba zan tambayeka ba," in ji Elea.

Ta yi gargadin cewa so tari irin wannan abu na samun gaza wa ne saboda babu gaskiya a tsakanin ma'aurata. "Abin da ya kamata ya hada kan mutane ya koma shi ne yake raba su," kamar yadda ta yi gargadi.

Kafin ma'aurata su tambayi juna kan batun fara salon soyayya da wasu mutanen na daban, Elea ta ce ya kamata su dubi kansu.

"Ku yi tunani kan soyayyarku. Me kuka rasa? Me kuke so da abin da ba ku so? Ku rubuta abubuwan da suka fi ba ku sha'awa. Babu wanda zai ga hakan - sai ku kanku," in ji ta.

Batun yana kuma son tattaunawa ta tsanaki.

"Lokaci ne mawuyaci... musamman ga wadanda suka girma da sanin rayuwa da miji ko mata daya shi ne hanyar nuna kauna da mutunta juna tsakanin mutanen da ke son juna," in ji Elea.

"Ana amincewa da abubuwa ne ta hanyar zama don tattaunawa. Wane tsawon lokaci za ku dauka? Tare da waye za ku kasance? Kuma yana da kyau kada a iyakance zabi, illa a fahimci juna," a cewar Elea.

Samun abokin shawara yana da muhimmanci, in ji ta. "Ka je ka yi bincike da karance-karance kan batun, ka saurari ra'ayoyin mutane kan abin da kake son yi," in ji Dr Elea.

"Tsangwama gaskiya ce. Ka nemi shawarwari daga wajen kwararru wadanda suka san hanyoyin da suka fi dacewa na more soyayya," kamar yadda ta ba da shawari.

Ta kara da cewa komawa soyayya da wasu mutanen na daban don magance wata matsala da aka samu, yawanci hakan bai cika aiki ba.

"Ka manta da batun," in ji ta. "Ba shawara bace ko kuma dogaro na karshe. Ana yin batun tare da amincewa da juna lokacin da alaka take da kyau, kuma kowane bangare na son inganta shi."

Tsana da fata

Lokacin da Eleá ta fito bainar jama'a karon farko ta yi magana kan sauyi a cikin aurenta, ta samu dubbanin sakonnin tsana da tsangwama.

"Wasu kalamai ba su cancanta ba: 'Kana yin abin ne don kada ka rasa mijinka," in ji ta.

Sai dai, ta kuma samu sakonnin goyon baya, ciki har da wasikun wasu ma'aurata da suka nuna sha'awar yin abin da Elea da mijinta ke yi.

"Babu wanda aka haifa shi kadai," in ji Elea. "Babu wanda ta tambayeka kan haka. Dokoki, yin imani, tatsuniyoyi da kuma abin da iyalinka ke son ka yi - wadannan duka sun nuna cewa soyayya tana samuwa ne tsakanin mutane biyu. A tarihi, maza na da yanci yayin da ake gallazawa mata," a cewarta.

Wannan tsari, yana shafi rabon gado, addini da kuma dangi.

"Ana tilasta soyayya da mutum daya ne don cewa yana da kyau kuma shi ya fi, amma sai a rika tsangwamar duk wanda ya ki batun."

Shin Eleá na cikin farin ciki ne a yanzu? "Kwarai kuwa," in ji ta.

"Sai dai lamarin ya danganta da waye ni a yanzu. Shekaru 15 da suka wuce, bayan shan wahala da kuma yaudara, ba zan taba kasancewa a haka ba. Kadaice wa ya taba saka ni farin ciki. Bayan lokaci, bukatar son abu ya fita daga raina. Bayan tsawon lokaci batun jima'i na fita cikin ran ma'aurata."

Gare ta, shiga soyayya da wasu mutane na daban ya faru ne sakamakon gaskiya da kuma yanci tsakaninta da mijinta.

"Me ya sa soyayya za ta kare saboda kawai wasu mutane na tunanin hanya daya ce kadai ake soyayya?" ta tambaya.