Me ya sa rikicin Armenia da Azerbaijan ya ƙi ƙarewa?

Jerin fadan da ake samu a kan iyaka tsakanin sojojin Azerbaijan da Armenia na kara sanya fargabar cewa sabon yaki zai iya barkewa tsakaninsu.

Tun a karshen shekarun 1980, tsoffin kasashen Tarayyar Soviet din suka yi fada a kan iyakar Nagorno-Karabakh, abin da ya janyo mutuwar dubban mutane da kuma raba wasu dubbai da muhallansu.

Ina Armenia da Azerbaijan suke?

Kasashen biyu na a yankin kudancin Caucasus, wato wani yankin da ke da tsaunuka a Gabashin Turai da Asiya wanda kuma ke tsakanin Tekun Baharul Aswad da kuma Tekun Caspian.

Azerbaijan na da yawan mutane 10.1m, wanda yawancinsu Musulmai ne.

Armenia kuwa na da yawan mutane miliyan uku, kuma yawancinsu Kiristoci.

Azerbaijan na da kyakkyawar alaka da Turkiyya, Armenia kuwa da Rasha take da kyakkyawar alaka, ko da yake akwai fahimta mai kyau tsakanin Rasha da Azerbaijan ma.

A 1923, Tarayyar Soviet ta mayar da yankin Nagorno-Karabakh, wanda ke da yawan Armeniyawa cikin jamhuriyar Azerbaijan.

Yawancin mutanen yankin da suka kai dubu 150, har yanzu 'yan Armenia ne.

Ta yaya aka fara rikici tsakanin Armenia da Azerbaijan?

A 1988, kabilun Armenia da ke Nagorno-Karabakh suka fara nuna damuwa a kan yakamata yankin yakasance Armenia ce ke iko da shi.

Wannan dalili ne ya haifar da zaman dar-dar sannan a lokacin da aka ayyana yankin a matsayin mai cin gashin kansa a 1991 a hukumance, sai yaki ya barke tsakanin Armenia da kuma Azerbaijan.

Yakin ya janyo mutum dubu 30 sun jikkata sanann wasu dubbai sun yi gudun hijra.

A 1993, Armenia, ta karbe ikon yankin Nagorno-Karabakh da kuma yankunan Azerbaijan da dama.

A 1994, Rasha ta wargatsa yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cimma.

Yankin Nagorno-Karabakh, yakasance bangaren Azerbaijan, to amma tun bayan da yawancinsa 'yan aware ke iko da su, suka ayyanata a matsayin Jamhuriya, kuma Armeniyawan yankin da gwamnatin Armenia ke goyon bayansu ne iko da wajen.

Yaki ya sake barkewa tsakanin Armenia da Azerbaijan a tsakanin watan Satumba da Nuwambar 2020.

A wannan karon,Azerbaijan wadda ke samun goyon bayan Turkiyya ta samu nasarar kwace ikon yankuna da dama na Nagorno-Karabakh.

A karkashin yarjejeniyar tsagaita wutar da Rasha ta rusa,Armenia ta janye dakarunta daga wajen sannan kusan dakarun wanzar da zaman lafiyar Rasha 2000 ne suke je yankin don sanya idanu a kan yarjejeniyar.

Rikicin ya yi sanadin mutuwar mutane fiye da 6,600.

Shugabannin kasashen biyu sun sha ganawa domin samun maslaha a kan Nagorno-Karabakh, to amma ba bu wani ci gaba da aka samu.

Me yasa ake fada a wajen a baya-bayan nan?

A kwanakin baya bayannan, rikici ya barke a kan iyakar Armenia da Azerbaijan, wanda firaiministan Armenia Nikol Pashinyan, ya ce sojojinsa 49 sun rasa ransu a ciki.

Armnenia ta ce sojojin Azerbaijan sun yi lugudan wuta a garuruwa da dama da ke kusa da iyakar Azerbaijan.

Gwamnatin Armenia ta ce Azerbaijan ce ta fada fadan saboda bata so a cimma matsaya a kan Nagorno-Karabakh.

Yayin da Azerbaijan kuma ta ce Armenia ce ta fara kai hari.

Azerbaijan ta zargi Armenia da yi mata leken asiri a game da ayyukanta na kan iyaka sannan kuma ta kai hari wuraren da sojojinta suke.

Wanne martani sauran kasashe suka mayar a game da sabon rikicin kasashen biyu?

Yawancin kasashe na fargaba a kan barkewar yaki a karo nabiyu a yankunan tsohuwar Tarayyar Soviet da ke gabashin Turai, abin da zai sa a samu kari yaki bayan yakin da ake a Ukraine.

Rikicin da zai sa dole kasashe irinsu Rasha da Turkiyya su shiga cikinsa.

Rasha ta ce tana tattaunawa a kan batun tsagaita wuta tare da Armenia da kuma Azerbaijan, to amma akwai rahotannin da ke cewa an samun fada har yanzu a tsakanin kasashen.

Turkiyya na goyon bayan Azerbaijan sannan ta fada wa Armenia cewa ta mai da wukar.

Faransa wadda a yanzu ke rike da ragamar kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, ta bukaci a tattauna a kan batun rikicin.

Shugaban kwamitin Charles Michel, ya ce yana tuntubar shugabannin kasashen biyu don kare ruruwar rikicin.

Tarayyar turai na son a mayar da Azerbaijan kasa mai zaman lafiya.

A yanzu kasashen tarayyar turan na samun cubic mita na iskar gas biliyan takwas daga kasar a duk shekara.

Sakamakon dai na bawa kasashen iskar gas da Rasha ta yi, a kwanannan Tarayyar Turai ta cimma yarjejeniya tare da Azerbaijan don kara yawan iskar gas din da suke samu daga kasar domin ya kai kubic mita biliyan 12 a 2023 da kuma samun kubic mita biliyan 20 a 2027.

To amma yarjejeniyar ta dogara ne a kan yadda kamfanonin kasashen waje za su zuba jari a Azerbaijan domin tabbatar da cewa tana da damar da za ta fitar da iskar gas din da ake bukata.

A lokacin da shugaba Ilham Aliyev na Azerbaijan ya gana da firaiministan Armenia Nikol Pashinyan Brussels a karshen watan Augusta, a karon farko dukkansu sun gaisa da juna har suka sha hannu, abin da ya sa wasu mutane ke ganin akwai yiwuwar yarjejeniyar zaman lafiya da suka amince da ita zata iya fara aiki.

Babu wanda ya zaci wani rikici zai sake barkewa a nan kusa.

Armenia ta ce Azerbaijan ta kai hari yankunanta da ke kudu maso gabashi, abin da Azerbaijan din ta musanta tana mai cewa duk abin da aka ga sojojinta sun yi martani suka mayar a kan abin da aka yi musu.

Yawancin rikicin da kasashen biyu ke yi tun bayan samun 'yancin gashin kansu a kan Nagorno-Karabakh ne wanda kasashen duniya ke ganin wani bangare ne na Azerbaijan.

To amma rikicin da ya barke a wannan makon ya faru ne a wajen da ke da nisan kilomita 200 daga Karabakh.

Azerbaijan na son bude hanyar da zata ratsa ta yankin Armenia zuwa Nakhichevan ta kuma karasa zuwa Turkiyya, abin da firaiministan Armenia Pashiinyan ya yi watsi da shi.