Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Me ya sa mawaƙa ke adawa da juna?
Yadda batun mallakar mota mafi tsada ya dawo da batun tsama tsakanin fitattun mawaƙan Hausa, Nazir Ahmad da aka fi sani da Sarkin Waƙa, da Dauda Kahutu Rarara ya sa an fara dawo da tambayar me ya sa suke tsama ne.
Mawaƙan biyu sun daɗe sun jan zarensu a masana'antar waƙoƙin Hausa, sannan a gefe guda kuma magoya bayansu suke ƙodawa tare da nuna cewa gwanayensu sun fi ƙwarewa.
Sai dai batun yana wuce maganar iya waƙa, inda ake komawa gasar nuna arziki da gidaje da sauran abun duniya.
Ana kuma ganin yadda magoya bayansu kan fito a shafukan sada zumunta suna korantawa juna arziki da wasu kadarori da kaifin fikirar da kowanne mawaki ya mallaka ko nasibi.
Sai dai ba tun yanzu ba ne aka fara samun irin wannan takun-saƙar a tsakanin mawaƙan Hausa, tun shekaru aru-aru ake samun rigima, inda a wasu wuraren ma ake zargin yunƙurin illata juna, ko neman rayuwar juna.
Amma ba a tsakanin mawaƙan Hausa ba ne kaɗai lamarin ya tsaya, domin duk mawaƙan duniya ana samun irin wannan, kamar yadda aka samu fitacciyar adawa da tsama tsakanin 2Pace da BIG da sauran su da ma wanda ake tunanin an samu tsakanin Wizkid da Davido na kudancin Najeriya.
Wannan ya sa BBC ta waiwayi baya domin tattaro wasu fitattun takun-saƙa da aka yi a tsakanin mawaƙan Hausa.
Shata da Mammalo da Ɗan Bade
A game da irin takun-saƙa da aka a zamanin baya, Malam Ibrahim Sheme, wanda masani ne kuma marubucin littafin tarihin Alhaji Mamman Shata, ya ce an samu saɓani tsakanin Shata da wasu mawaƙan, ciki har da yaransa.
"Ka ga ai akwai lokacin da Shata ya kai ƙara wajen ƴansanda har aka kama su Ɗanƙwairo da Amadun Doka aka kai su Kano aka tsare.
Haka kuma Sheme ya ce akwai akwai takun-saƙa da aka ce an yi tsakanin Alhaji Musa Ɗan Bade da Mamman Shata.
"Amma Shata ya fada min cewa bai san Ɗan Bade ba. Asali saɓani ne tsakanin Shata da wani tsohon maroƙinsa Alhaji Bature Sarkin Magana sai Ɗan Bade ya shiga."
Sheme ya kuma ce akwai takun-saƙa tsakanin Shata da Mammalo. "Shi ma Mammalo tsohon yaron Shata ne, amma da suka samu saɓani sai ya masa zambo a cikin waƙa yake cewa, "Idan ka ce mana Allah ya yarda gare ka, muma Allah ya yarda."
"Wannan ne ya sa a lokacin da Musa Ɗan Bade ya zo Kaduna daga Jos, sai ya auri Hajiya Hauwa, babbar ƴar Alhaji Mammalo, amma a lokacin shi Mammalo ya riga ya rasu. Daga baya ne sai aka naɗa Ɗan Bade a matsayin Sarkin Yaƙin Mawaƙan Hausa, kuma shi Bature Sarkin Magana ne ya jagoranci naɗa shi. Shi ne har ya yi wa Shata waƙar "Mai tafarnuwa."
Sani Ɗan Indo da Haruna Uji da Ali Makaho
A game da takun-saƙar da ta yi fice a baya tsakanin Ali Makaho da San Ɗan Indo, Malam Sheme ya ce asali rigima ce tsakanin Haruna Uji da Sani Ɗan Indo, sai Ali Makaho ya shiga.
"Shi Ali Makaho ya shiga ne, inda ya faɗa a waƙa cewa, "don na ce ka daina taɓin ƴan gurmi, shi ne ka zo kana zagina."
"Shi ne Ɗan Indo ya mayar masa da martani, ya ce makaho ne ba ya gani, shi ne shi ma Ali Makaho ya mayar da martani mai zafi".
Rarara da Naziru
Magoya-bayan Dauda Kahutu Rarara kan nuna cewa mawaƙin ya fi Naziru iya waƙa, haka zalika shi ma Naziru Sarkin Waƙa magoya-bayansa na fitowa suna cewa ya fi Rarara iya waƙa.
A wasu lokutan ma akan ɗau waƙoƙin nasu ana fashin-baƙi da martani tsakanin masoya waɗannan mawaƙa na ƙasar Hausa.
Duk da cewa waɗannan mawaƙa ba kasafai suke fitowa suna bayyanawa ko nuna abin da ke shiga tsakaninsu ba, a wasu lokutan suna yi wa juna hannunka mai sanda, kamar yadda Naziru Sarkin waƙa a kwanan baya ya fito yana martani kan motar da Rarara ya mallaka.
Naziru a wannan lokaci ya fito yana shaidawa mabiyansa a shafukan sada zumunta cewa shi ba mai bayyana dukiya ba ne, amma motar da ya mallaka wata marsandi ƙirar Gbox za ta saye motar wani wanda ya bayyana da wancan - wanda ake tunani da Rarara yake - yake nunawa a shafukan sada zumunta wato Avatar sau uku da ɗauriya.
Wannan batu ya rinƙa haifar da muhawara da ce-ce-ku=-e a shafukan sada zumunta.
Me ya sa haka?
Game da yadda ake yawan samun takun-saƙa tsakanin mawaƙa, Malam Ibrahim Sheme, masani a kan waƙoƙi da fina-finan Hausa, ya ce lamari ne da ya samo asali a harkar tun a shekarun baya.
Ya ce ko a tsakanin mawaƙan shekarun baya, "masu amfani kayan kiɗi da waƙa na zamanin baya irin su Alhaji Mamman Shata ana samun takun-saƙai sosai, kamar yadda ake samu a yanzu."
Sheme ya kuma ce dalilan da suke jawo takun-saƙa a zamanin baya, su ɗin ne dai suke jawo matsalar a yanzu.
"Babbar matsalar ita ce gasa a tsakanin mawaƙan. Gasar ce take riƙeɗewa zuwa gaba saboda kowa na son shahara. Wane ne ya fi shahara? wane ne ya fi ɗaukaka? wane ne mutane suka fi so? da sauran su."
Ya ce lamarin na naso zuwa iyayen gida, "misali ai kowa ya san a wancan lokacin, babban ubangidan Mamman Shata shi ne Sarkin Daura na wancan lokacin," wanda Sheme ya ce Shata ba zai bari ya raɓe shi ba.
"Haka yanzu Dauda Kahutu Rarara da Naziru Sarkin Waƙa, suma siyasa ta taka rawa, kamar yadda shi Naziru ya faɗa akwai inda suka haɗu a baya, amma yanzu sun rabu. Ka ga ke nan siyasa da samun gindin zama sun taka rawa."
Haka kuma Sheme ya ce nuna isa wajen abun duniya na taka rawa, "ina da babban gida ba ka da shi misali. A baya an yi, yanzu ma ana yi kamar yadda aka yi na motar Rarara da Naziru. Sannan akwai masu gasa wajen neman aure duk da a tsakanin Rarara da Naziru babu wannan."
Alheri ne?
Sai dai a daidai lokacin da wasu ke cewa gasa na haifar da alheri a wasu abubuwa, Malam Sheme ya ce gasa a tsakanin mawaƙan ba alheri ba ce.
"Babu alheri a ciki domin tana kawo rarrabuwar kai a tsakanin mawaƙan. Akwai lokacin da Mamman Shata ya sa ƴansanda suka kama wasu manyan mawaƙa irin su Ɗanƙwairo da su Amadun Doka aka tsare su a Kano suka daɗe."
Sheme ya ƙara da cewa gasar tana sa mawaƙan suna jifar juna da maganganu na gugar-zana marasa kyau, "kuma takan raba tsakanin masoyansu ma, har ta kai suna gaba."
"Akwai lokacin da aka yi wani biki a Garki a gidan Hajiya Laila Dogon Yaro, Ɗanb Bade ya zo, amma su Shata sun zo, sai ta ce lallai Ɗan Bade ya yi haƙuri ya tafi, ta ba shi kaya da kyaututtuka, amma ta ce ba zai yi wasa ba."