Yadda ake rusawa da ƙona unguwar marasa galihu a Legas

Asalin hoton, Gift Ufuoma/BBC
- Marubuci, Chiamaka Dike
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Africa
- Aiko rahoto daga, Makoko, Lagos
- Lokacin karatu: Minti 5
Anna Sobie, mahaifiyar yara biyar na cikin waɗanda suka rasa gidajensu bayan hukumomin jihar Legas sun ruguza gidajen katako na mutanen da suke rayuwa a saman ruwan teku.
Tuni dai wasu suka soki matakin, inda suka zargi gwamnatin jihar da "ƙwace musu muhalli".
Sai dai jami'an gwamnatin Legas sun ƙaryata zargin, inda suka ce suna rusa wani ɓangare ne na Makoko saboda garin ya fara faɗaɗa zuwa ƙarƙashin layin lantarki, wanda hukumar ta ce yana da illa ga lafiyarsu.
Yanzu Sobie da yaranta suna rayuwa ne a cikin ɓaraguzan katakai suna jiran ganin yadda za a yi.
Makoko ne babba a cikin garuruwa 10 da ke saman ruwa a Legas, wanda a sanadiyar cunkoso, yake fama da ƙarancin gidaje, kuma rayuwa ke ƙara tsada saboda ƙaruwar mutane.
A lokacin da Sobie ke zantawa da BBC, tana cikin kwale-kwale ne tana tafiya a cikin rafin a tsakanin itacen bamboo, ɗauke da katifa da jakunkunan kayan sakawa da sauran su.
Mazauna garin sun ce an fara rushe-rushen ne kwana biyu kafin Kirsimeti, lokacin da jami'an rusau ɗin suka isa garin tare da rakiyar ƴansanda.
A wata sanarwa da da suka fitar a watan jiya, ƙungiyoyin sa kai guda 10 sun ce "ɓatagari da jami'an tsaro da jami'an rusau sun isa garin da katafiloli suka fara rusau, sannan suna ƙonawa.
"Sun rusa gidaje da dama, sun ƙona wasu ba tare da bayar da lokaci ba, inda a wasu wurare ma mutane suna ciki a lokacin da aka fara rusau ɗin," in ji ƙungiyoyin.

Asalin hoton, Gift Ufuoma/BBC
Lokacin da BBC ta ziyarci Makoko, hayaƙi na ci gaba da tashi daga ɓaraguzan gidajen da aka rusa.
Masu kamun kifi ne suka ƙirƙiri garin Makoko a ƙarni na 19, waɗanda suka kasance suna rayuwa tun lokacin tare da wasu masu ƙaramin ƙarfi da ma baƙi da suka je Legas domin neman abinci.
Har yanzu ana muhawara kan mallakin garin. Gwamnatin jihar na iƙirarin mallakar garin a ƙarƙashin dokar mallakar fiyale ta tarayya, inda ta ce an gina Makoko ne ba tare da izini ba, kuma babu haƙƙin mallaka.
Sai dai tsofaffin mazauna garin suna cewa sun fara zama ne tun kafin a samar da jihar Legas, inda suke cewa suna da izinin zama na tun asali.
Ana ƙiyasin mazauna Makoko sun kai tsakanin 80,000 zuwa 200,000.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Ƙungiyoyin sun ce rushe-rushen ya raba sama a mutane 10,000 da muhallansu bayan rusa sama da gidaje 3,000 da makarantu da asibitoci da coci-coci. Gwamnatin jihar dai ba ta bayyana adadin gidaje da mutanen da abin ya shafa ba.
Gidan Sobie na cikin waɗanda rusau ɗin ya rutsa da su.
"Ina cikin gida muna zaune ne aka fara rusau ɗin," in ji ta. "Hayaniya ce ta yi yawa sai muka fito kawai muka ga katafila," in ji ta, inda ta ƙara da cewa ba ta samu isasshen lokacin kwashe kayayyakinta.
Haka kuma makarantar da ɗanta Solomon yake zuwa na cikin gine-ginen da aka rusa.
Sai Sobie da iyalanta suka koma wani gini da ke kusa da su, amma shi ma sai rusau ɗin ya kai kan shi.
"Muna rayuwa ne yanzu a fili a ƙarƙashin ruwa da rana, kuma yanzu haka sun fara ƙona kayayyakin mutane," in ji Sobie, sannan ta ƙara da cewa, "ba mu da wani wajen da za mu koma."
Kamar sauran yaran makarantar, yanzu Solomon ba ya zura makaranta. Inda yanzu yake zama da mahaifiyarsa yana taya aikace-aikace.
Sai dai ko a lokacin da ake ci gaba da rusau ɗin, wasu a can gefe kuma suna ci gaba da gudanar da harkokinsu na yau da kullum.

Asalin hoton, Gift Ufuoma/BBC
Sama da mutum 1,000 ne suka gudanar da zanga-zanga a makon jiya zuwa majalisar jihar, sannan suka buƙaci ganin gwamnan jihar, Babajide Sanwo-Olu, wanda ofishinsa ke kusa da majalisar.
Sai dai ƴansanda sun tarwatsa su ta hanyar amfani da hayaƙi mai sa hawaye.
Mazauna garin sun ƙara da cewa an yi amfani da hayaƙin ma a lokacin da ake rusau ɗin, inda suka ƙara da cewa lamarin ya yi sanadiyar mutuwar mutum biyar, ciki har da ƙananan yara.
Amma gwamnatin jihar Legas ta ce ba ta da masaniyar jami'anta sun yi amfani da hayaƙi mai sa hawaye.
A zantawarsa da BBC, kwamishinan watsa labarai, Gbenga Omotoso ya ce za su bincika zargin.
Ƴan majalisar dokokin jihar Legas sun ce sun gayyaci jagororin garin domin tattaunawa.
Sai dai gwamnatin jihar ta kare matakin da ta ɗauka na rushe-rushe, inda suka an yi gine-gine a ƙarƙashin layin lantarki.
"Babu gwamnatin da ta san aikinta da za ta bar mutane su zauna a ƙarƙashin layin lantarki ko kuma su yi gine-gine a hanyar ruwa," in ji mai ba gwamna shawara kan cigaban birane, Olajide Abiodun Babatunde a wata sanarwa da ya fitar.
Gwamna Sanwo-Olu ya ce za su biya diyya ga iyalan da rushe-rushen ya shafa, sannan ya ce ba daidai ba ne a zargi da tarwatsa Makoko.

Asalin hoton, Gift Ufuoma/BBC
Fitaccen mai kasuwancin gidaje a Legas Peacemaker Afolabi ya shaida wa BBC cewa buƙatar filaye a Legas na ƙaruwa.
Wasu mazauna kuma sun yi zargin cewa ana musu rusau ne domin gina kasuwar zamani da gidaje na alfarma.
Sai dai gwamnatin jihar ta sha musanta irin waɗannan raɗe-raɗin a baya, amma ana ci gaba da yaɗa zargin.
A sanarwar a ƙungiyoyin suka fitar, sun ce rushe-rushe da ake yi a Makoko da wani garin da aka yi a bara na cikin yunƙurin gwamnati na ƙwace "garuruwan mutane."
"Wannan matakin na gwamnati ya shafi dubban mutane, jajirtattu masu neman na kansu. Don haka wannan wani yunƙuri ne na tauye haƙƙin talakawa domin ƙara wa masu ƙarfi ƙarfi."
Ƙaruwar mutane a birnin, da hauhawar kuɗin haya na cikin abubuwan da suka mutane da dama suke komawa rayuwa a ƙananan garuruwa, musamman bakin tekuna da kusa da manyan hanyoyi.
A lokacin ziyarar BBC a Makoko, mun ga matasa a zaune suna gyara komar kamun kifinsu.
Elizabeth Kakisiwe ta ce a yanzu tana rayuwa ne a wani waje da ke kusa.
A duk yammaci takan jere katakai ne domin yaranta su samu inda za su kwanta.
"Muna kasuwa ne lokacin da aka fara rushe-rushen," in ji ta. "Ko da na koma sai na samu an riga an rusa gidana."
Ta ce ba a ba su isasshen lokaci ba, kuma ba a faɗa musu lokacin da za a yi rusau ɗin ba, ballantana su samu damar kwashe kayayyakinsu.
"Yanzu idan dare ya yi, a cikin sanyi muke zama," in ji ta. "Sannan idan yaranmu na zazzaɓi sai dai mu ba su maganin paracetamol."
"Dafa abinci ma ya yi wahala, saboda ruwan sama ya sa ko'in ya jiƙe. "Jiya ma garin kwaki kawai muka sha," in ji Kakisiwe.
Da ƙarin bayani daga Gift Ufuoma











