Lokuta biyar da jirgin ƙasan Abuja-Kaduna ya samu matsala

Lokacin karatu: Minti 3

Hukumar kula da sufurin jiragen ƙasa ta Najeriya NRC ta ce ta kammala gyare-gyare a hanyar dogon Abuja-Kaduna, inda ta ce jirgin zai koma aikin jigilar fasinja a hanyar cikin mako zuwa.

A wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar, Callistus Unyimadu ya fitar a ƙarshen mako ya ce hukumar ta yi ƙoƙarin kammala gyare-gyaren cikin tsanaki.

Sai dai sanarwar ba ta fayyace haƙiƙanin ranar da jirgin zai koma aiki ba, inda ya ce, "nan da kwanaki kaɗan za mu bayyana ranar da za mu fara jigila''.

A ranar 26 ga watan Agusta ne dai jirgin ƙasar da ya tashi daga Abuja zuwa Kaduna ya faɗi jim kaɗan bayan barinsa Abuja.

Hatsarin ya haifar da raunuka ga wasu fasinjojin da dama, lamarin da ya sa aka dakatar da aikin jirgin domin a yi gyara.

Ba wannan ne dai karon farko da hanyar jirgin ta samu matsala, har ta kai ga dakatar da jigilar jiragen tsakanin manyan biranen biyu na arewacin Najeriya.

Tun bayan da ƙaddamar da jigilar jirgin ƙasan Abuja zuwa Kaduna a shekarar 2016, an samu lokuta aƙalla biyar da aka samu tsaiko a jigilar jirgin bayan wasu matsaloli da suka auku.

Ga wasu lokuta biyar da aka samu katsewar jigilar jirgin ƙasan.

Agustan 2025

A ranar Talata 27 ga watan Agustan 2025 jirgin ƙasan ya fa din jim kaɗan bayan tashinsa daga Abuja, babban birnin ƙasar.

Jirgin ƙasan ɗauke da fasinja ya goce daga kan layinsa ne, lamarin da ya sa wani ɓangare nasa ya faɗi.

Fasinjoji 21 ne suka ji rauni a cewar hukumar binciken ingancin sufuri ta Najeriya.

Lamarin ya faru ne a ƙauyen Asham da ke hanyar Abuja zuwa Kaduna.

Mayun 2024

Haka a watan Mayun 2024, wani jirgin ƙasan da ya tashi daga tashar Rigasa da ke Kaduna ya goce a daidai garin Jere da ke kan hanyar Abuja.

Jirgin na ɗauke da fasinjoji 685 da ma'aikatansa a lokacin da ya goce.

Sai dai a lokacin wannan hatsari babu wanda ya ji rauni cikin duka fasinjojin.

Satumban 2023

Sannan a watan Satumban 2023, wani jirgin ƙasan da ya tashi daga Abuja zuwa Kaduna ya goce a daidai tashar Kukere.

Ita ma wannan gocewa ba a samu asasar rai ba, amma wasu taragogin jirgin sun lalace.

Shi ma a lokacin an ɗan dakatar da jigilar na yan kwanaki kafin gyara hanyar jirgin.

Oktoban 2023

Kwanaki bayan nan aka ƙara samun wani ɗan ƙaramin hatsarin jirgin ƙasan bayan gocewarsa a kusa da tashar Asham kusa da garin Jere.

A lokacin faruwa lamarin fasinjoji sun maƙale kafin kawo musu ɗauki.

Maris 2022

Wannan shi ne hatsari mafi muni da aka taɓa samu a kan titin jirgin tun bayan addamar da shi.

Lamarin ya faru ne a lokacin da jirgin ke tsaka da gudu a kan hanyarsa ta zuwa Kanduna.

Ƴanbindiga ne suka ƙaddamar da hari kan jirgin bayan da suka buɗe masa wuta, a lokacin da yake tafiya da daddare,lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutum tara tare da yin garkuwa da gomman fasinjoji.

Hatsarin ya ɗauki hankula a ciki da wajen Najeriya, bayan da fasinjojin da aka kama suka kwashe watanni masu yawa a hannun ƴanbindigar da suka sace su.

Inda suka sriƙa sakin kaɗan-kaɗan daga ciki kafin su kamamal sako ragowar gaba ɗayansu.

Tun daga lokacin ne kuma aka dakatar da jigilar jirgin da daddare.

Bayan ƙaddamar da harin, hukumomi sun dakatar da jigilar jirgin tsakanin manyan biranen biyu har na tsawon wata tara, kafin ya koma aiki cikin watan Disamabn 20222.

Me ke haddasa gocewar jiragen?

A lokuta da dama wasu ƴanƙasar kan yi zargin cewa rashin kula da ingancin jiragen ne ke haddasa hatsuran.

To sai dai hukumar kula da ingancin sufuri ta Najeriya ta sha musanta zargin, kodayake a wannan hatsari na baya-bayan nan ta amince cewa sakaci rashin kula da ingancin jiragen ne ke haifar da matsalar.

Bayan samun hatsarin farko na ƴanbindiga hukumomi sun yi tanadin samar da ingantaccen tsaro a kan titin.