Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Mece ce makomar masarautar Kano a nan gaba?
Tun bayan da gwamna Abba Kabir Yusuf na Kano ya sake naɗa Muhammadu Sanusi II a matsayin Sarkin Kano na 16 bayan shekaru huɗu da tuɓe shi, al'umma da masana ke ta sharhi da yin tambayoyi dangane da makomar sarakunan masarautar ta Kano a nan gaba.
A ranar Juma'a ne dai aka miƙa wa Sarki Sanusi II shaidar komawa karagar masarautar Kano a matsayin sarki na 16 a jerin sarakunan Fulani.
A shekarar 2020 ne dai gwamnatin tsohon gwamna Abdullahi Umar Ganduje ta ƙirƙiro ƙarin sabbin masarautu huɗu sannan daga bisani aka tumɓuke Muhammadu Sanusi II daga karagar Sarkin Kano.
Me ya sa sarakuna ke shiga siyasa?
Dakta Nasiru Wada, wani masanin sarautar gargajiya kuma mai nazari kan masarautar Kano, ya shaida wa BBC cewa sarakuna ba su banbanta da sauran 'yan Najeriya ba wajen shiga al'amuran siyasa.
"Ai ba za ka raba sarakuna da siyasa ba domin ko ma ba su shige ta ba to su 'yan siyasar ne da kansu ke tsunduma su. Sarakuna suke da jama'a da talakawa. Su kuma 'yan siyasa abin da suke nema ke nan.
Saboda haka babu wani sarki da ba ya siyasa domin ai gwamna ne ke naɗa sarki. Tun a jamhuriya ta farko mun ga yadda idan ba ka jam'iyyar gwamnati ma ai ba za a naɗa ka sarki ba." In ji Nasiru Wada.
Sai dai masanin ya ce akwai buƙatar sarakunan su yi siyasar sama-sama ta yadda 'yan siyasar ba za su ɗauke su a matsayin masu yaƙarsu ba.
To sai dai Malam Kabiru Sufi wanda masanin kimiyyar Siyasa ne a Kano, ya ce ba yanzu aka fara samun rashin fahimta ba ta siyasa tsakanin masu gwamnati da masarautar Kano.
"An samu irin wannan a jamhuriya ta ɗaya lokacin da Sarki Sanusi na ɗaya ya yi murabus. Sannan an so a samu irin wannan a jamhuriya ta biyu amma al'amarin ya tsaya ne a kan takardar gargaɗi.
Amma wannan ya fi muni inda aka samu sauye-sauye a tsawon shekaru huɗu kawai." In ji Malam Kabiru Sufi.
Komawar Sarki Muhammadu Sanusi II na nuni da makomar sarautar
Malam Kabiru Sufi ya ce lallai masarautar Kano za ta ci gaba da ɗorewa a matsayin babbar masarauta a arewacin Najeriya idan dai har 'yan gwamnati da kuma gidan sarautar kansa suka ɗauki darasi.
"Makomar masarautar na hannun ɓangarorin biyu - misali idan abin da aka yi yanzu haka na komawa sarki ɗaya kuma su 'yan gwamnati na yanzu da na gaba suka ɗauki haƙuri suka ci gaba a haka to lallai masarautar ta Kano za ta ci gaba a matsayin mai kwarjini."
Shi ma dakta Nasiru Wada ya ce yana da ƙwarin gwiwar cewa masarauta da sarakan Kano na gaba ka iya ɗorewa kamar yadda suke a yanzu bayan mayar da Sarki Muhammadu Sanusi II.
"Kasancewar idan gwamnati za ta sauya sarki kuma ta san cewa bayanta za a sake komawa gidan jiya to ba za ta yi ba. Haka ma su waɗanda za a bai wa sarautar, idan sun san cewa daga baya za a sauya su to lallai ba za su karɓi sarautar ba. Saboda haka ina da ƙwarin gwiwar cewa gaban masarautar na da haske sosai."
Ya kamata masu sarauta su 'rike bakunansu'
To sai dai masanan biyu duk da sun yi ittifaƙin cewa siyasa a tsakanin sarakuna dole ce amma sun amince cewa ya kamata sarakuna a matsayinsu na iyayen ƙasa su kame bakunansu ta yadda ba a kan kowane batu za su rinƙa magana ba.
Masanan sun ce su 'yan gwamnati kasancewar su ne masu riƙe da madafun iko, ba su cika son katsalandan ba musamman a kan abin da ya shafi yadda suke tafiyar da mulki.
"Ka ga ai idan ban da sau biyu a jamhuriya ta ɗaya da ta biyu ba a taɓa samun irin wannan saɓata juyatar ba. Kuma a jamhuriya ta biyu ai takardar gargaɗi kawai aka bai wa Sarki Ado Bayero lokacin Abubakar Rimi".
Babban dalilin da wasu ke alaƙantawa da cire sarki Muhammadu Sanusi II da gwamnatin tsohon gwamna, Abdullahi Umar Ganduje ta yi shi ne "sukar muradan gwamnati", duk da dai gwamnatin ta sanya zarge-zargen rashawa da cin hanci.