Mene ne 'sinadarin' Thallium sulphate da El-Rufai ya zargi ofishin Ribadu da shigarwa Najeriya?

    • Marubuci, Adebola Ajayi
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Journalist
    • Aiko rahoto daga, Lagos
  • Lokacin karatu: Minti 4

Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya rubuta wasiƙa zuwa ga mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan tsaro Nuhu Ribadu, inda ya buƙaci ofishin ya yi masa cikakken bayani kan shigar da kilo 10 na sinadarin thallium sulphate.

Sinadarin yana da matuƙar illa da haɗari, kuma ba kasafai hukumomin ƙasar ke yarda ana shiga da shi ba.

El-Rufai ya bayyana a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na X, inda ya saka wasiƙar da ya aika wa Ribadu, inda ya ce ya rubuta wasiƙar a ranar 11 ga watan Fabarairu ne a matsayinsa na ɗan ƙasa.

A cewarsa, ba don wani abu ya rubuta wasiƙar ba, face don kawai yana neman ƙarin bayani, da kuma neman a fayyace komai.

Ya kara da cewa yana so a yi cikakken bayani kan sinadarin, da kuma bayani kan zargin da yake yi cewa daga wani ɗan ƙasar Poland aka shigar da sinadarin zuwa Najeriya.

Ya ce akwai buƙatar mai bai wa shugaban ƙasar shawara kan tsaro ya fayyace abin da za su yi da sinadarin, a bayyana daga wajen wanda aka sayo, da kuma ko hukumomin Najeriya sun sahhale a shiga da sinadarin.

Wannan na zuwa ne dai a daidai lokacin da ake cigaba da tafka muhawara a siyasar Najeriya, inda takun-saƙa tsakanin Nasir El-Rufai da tsohon abokinsa Nuhu Ribadu ke ƙara rincaɓewa.

A wata tattaunawa da El-Rufai ya yi da BBC Hausa, ya bayyana cewa mai ba shugaban Najeriya shawara kan tsaro ne ya bayar da umarni a kama shi.

Sannan a wata tattaunawa da ya yi da tashar Arise mai zaman kanta a Najeriya, ya yi zargin cewa Ribadu ya bayar da umarnin, sannan ya yi iƙirarin cewa wani ne ya naɗi bayanin, sai ya faɗa masa, lamarin da ya tayar da ƙura matuƙa a ƙasar.

Haka kuma El-Rufai ya buƙaci a masa cikakken bayani kan adadin sinadarin da aka shigar ƙasar, da yadda za a adana shi da ma hanyoyin da za a tabbatar da tsaronsa.

Ya ce yana so a bayyaa masa rawar da hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta ƙasar wato Nafdac da kuma hukumar kula da cututtuka masu yaɗuwa NCDC suka taka wajen shigar da sinadarin.

"Na rubuta wannan wasiƙa ce a matsayin ɗan ƙasa domin nemam bayani da tabbaci game da bayanan da muka samu cewa ofishinka na mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan tsaro ya sayo kilo 10 na sinadarin Thallium Sulphate da ofishin ya sayo daga wani dila a ƙasar Poland," in ji El-Rufai.

Tsohon gwamnan na Kaduna ya ƙara da cewa, "sinadarin Thallium yana ɗauke da guba mai hatsari, kuma sinadari ne da hukumomi ke matuƙar sa ido a kansa a Najeriya. Wannan ya sa nake ganin yana da kyau, ko domin lafiyar al'umma da haƙƙinsu da tabbatar da amince a yi bayani cikakke."

Bayanan da El-Rufai ya buƙata

A cikin wasiƙar, Nasir El-Rufai ya buƙaci ofishin na mai ba shugaban ƙasa shawara kan tsaro ya bayani kan abubuwa kamar haka:

1. Me ya sa aka sayo sinadarin thallium sulphate?

2. Daga wajen wa aka sayo?

3. An samu lasisin shiga da sinadaran?

4. Adadin sinadarin da aka sayo ɗin da yanayin ƙarfinsa

5. Tsarin da za a bi wajen adana shi

6. Wace rawa hukumomin NAFDAC da NCDC suka taka wajen sayo sinadarin?

7. An auna yanayin illolinsa da yadda za a guje wa matsalolin?

Mene ne sinadarin Thallium Sulphate?

Thallium Sulphate wani sinadari ne mara kala wanda kuma yake da tsananin haɗari, sannan hukumomi a Najeriya suke matuƙar sa ido kansa, kamar yadda bincike ya nuna.

Ana amfani da Thallium wajen haɗa maganin ɓera, kuma yana ɗauke da guba duk da cewa har yanzu ba a iya tantance asalin ƙarfin gubar da ke cikin sinadarin ba.

Duk da cewa ana samun shi a cikin maganin ɓera da wasu magungunan ƙwari, tun a tsakankanin shekarun 1970 ne ƙasashe da dama suke sanya ido kan sayar da shi saboda illolin da yake da su.

Sinadari ne da ba shi da launi, ba shi da ɗanɗano kuma ba shi da ƙamshi ko wari, kuma yana narkewa a cikin ruwa.

Idan ya shiga cikin jikin ɗan'adam, yana janyo amai da gudawa. Wannan ya sa farko-farkon alamunsa ke kama da wasu cututtuka da zazzaɓi, wanda ke janyo jinkirin gano shi.

Bayan kimanin kwana uku da cin sinadarin, mutum zai fara jin ciwon kai da raɗaɗi a gaɓoɓi da fara jijjiga da suma, da ma shiga ruɗani.

Lokutan da aka yi amfani da gubar thallium

Shafin cibiyar kula da cututtuka masu yaɗuwa ta Amurka CDC, ya ruwaito cewa hukumar lafiya ta duniya wato WHO ta yi gargaɗin amfani da sinadarin thallium sulphate wajen haɗa magungunan ɓera saboda illolinsa.

Amma duk da wannan gargaɗin, har yanzu ana amfani da shi a wasu ƙasashe da dama. A wasu ƙasashen kuma ana amfani da sinadarin ne wajen haɗa gilashi da sinadarin rini da sauran su.

A watan Maris na 2023 ne masu gabatar da ƙara a Osaka suka gabatar da wani mutum da zargin kashe abokiyar zamansa da gubar Thallium.

An zargi Kazuki Miyamoto mai shekara 37 da kashe budurwar mai shekara 21 mai suna Hinako Hamano bayan saka mata gubar a cikin ruwa.

Haka kuma an gano gubar Thallium a jikin wata ƴar'uwarsa, wadda take sume tun a shekarar 2020.

A 2022, wata kotu a Ingila ta kama wani likita ɗan Bulgaria da laifin amfani da Thallium wajen kashe mahaifin matarsa a 2012 a sanadiyar rikici game da riƙon ɗansa.

Kotun ta kama shi da laifin saka gubar ne ga mutum uku a cikin shayinsu a lokacin da suka je bulaguro.

A ranar 21 ga Disamban 2018, wani ɗalibi ɗan asalin China da ke karatu a Amurka ya yi yunƙurin saka gubar Thallium a abinci ko abin sha na abokin zamansa, kamar yadda masu gabatar da ƙara suka bayyana.

An zargi ɗalibin mai suna Yukai Yang da yunƙurin saka gubar ta Thallium a abincin da abin shan Juwan Royal.

Daga baya Yang ya ce ya sayo sinadarin ne domin ya yi amfani da shi, amma ba domin ya illata abokin karatunsa ba.