Waɗanne abubuwa mutumin da ya fara zagaya duniya a keke ya gani?

Lokacin karatu: Minti 5

Shekara goma bayan da Jules Vernes ya wallafa shahararren littafinsa na 'A faɗin Duniya cikin kwana 80', wani matafiyi ɗan Ingila ya fita domin shi ma ya zagaya.

Sai dai, ba kamar tauraron da ke cikin littafin Vernes ba wanda ya yi tafiya da jirgin ƙasa, Thomas Stevens ya yanke shawarar zagaya duniya a kan keke.

Ya fara tafiyarsa ne a 1884 kuma ya shafe sama da shekara biyu. Bayan komawarsa gida, ya rubuta wani littafi mai suna 'Zagaya Faɗin Duniya da a kan Keke'.

A cikin littafinsa, wanda ya ja hankalin duniya, ya bayyana daki-daki abin da ya gani a kan hanyarsa zuwa a Arewacin Amurka da zuwa Turai da yankin Asiya.

Yada zango a Arewacin Amurka

An haifi Stevens ne a Ingila, amma ya zauna a Amurka a shekara ta 1871 lokacin yana da shekara 17.

Duk da cewa shi ba ɗan wasan guje-guje ba ne, yana da sha'awa hawa da wasan keke, wanda aka fi kallo a matsayin abin hawan masu kuɗi a lokacin.

A cewar wani mawallafi kuma ɗan fim a Amurka, Robert Isenberg, ya ce abin da ya sa Stevens ya shahara shi ne "shi na kowa ne wanda ya ci gaba da jajircewa don ganin abubuwa sun faru."

Tun da farko, burin Stevens shi ne tsallakawa zuwa Arewacin Amurka - kuma ya samu nasarar yin haka ta hanyar amfani da keke daga San Francisco zuwa Boston a cikin watanni biyar.

Bayan yin tafiyar, wata mujalla kan mahaya kekuna ta ɗauki nauyin Stevens, kuma ya yanke shawarar faɗaɗa balaguronsa zuwa faɗin duniya.

Ya hau kwale-kwale daga Chicago zuwa Ingila a watan Afrilun, 1884. Bayan tsallakawa zuwa Turai, ya hau kekensa ya ratsa Turkiyya da Iran da Indiya da China da kuma Japan.

Keken Stevens daban yake da irin wanda ake da su a yau. An ƙera keken cikin yanayi mai kyau, kuma yana da madafa masu tsawo da karamin wheel.

An ruwaito cewa ya ɗauki abin gyara kaɗan ne kawai tare da shi.

Abin da ya gani a birnin Istanbul

Stevens ya isa Istanbul a lokacin bazara a shekara ta 1885, inda ya zauna a wani otal mai suna Galata na wata ɗaya lokacin azumi, a wani ɓangare na birnin mai cike da tarihi.

Ya kwatanta Istanbul a matsayin "ɗaya daga cikin birane masu ɗadin zama" a duniya, inda ya ce akwai mutane daga al'adu daban-daban, tituna masu kyau da kuma kayan ƙawa. Ya kuma ji daɗin yadda hasken shagunan shan gahawa ya ƙawata tituna, inda mutane ke tafiya riƙe da fitilu a hannunsu.

Ya kuma rubuta kan matan da ke cire gyalensu da kuma shan taba a wurare na musamman.

Steven ya tsara yadda zai yi tafiya a cikin birnin.

"Ya kai ziyara wuraren adana kayan tarihi, masallacin Hagia Sohia, kabarin Sultan Mahmut, Galata tower da kuma kabarin Sultan Sulaiman I."

Rubuce-rubucensa sun kuma yi magana kan masu rawa a birnin da kuma yadda iyalai ke rayuwa.

Yayin da yake kan hanya, Steven ya kuma haɗu da Sultan na wancan lokaci a birnin, Abdul Hamid II - wanda a yau ake gani a matsayin jagora da ke ra'ayi na daban a tarihin Turkiyya.

"Na cimma burina na ganin sultan; sai dai na ɗan lokaci kaɗan ne."

A mashigar Izmit, ɗaya daga cikin babban yankin Turkiyya mai masana'antu, ya rubuta cewa "ƙauyuka da aka ƙawata da fenti suna da kyawun gani da daddare."

A kan hanyar zuwa yankin Anatolia, ya haɗu da sansanin wasu Kurdawa. Ya ji sha'awar al'ummar can saboda sun tarbe shi yadda ya kamata.

Ya kwatanta shugaban al'ummar da ya tarbe shi a matsayin "mutum mai mutunci da kasance yana shan shisha". Ya yi rubutu kan abincin da aka ba shi, da kuma gadon da aka tanada masa ba tare da ya tambaya ba.

Balaguro zuwa gabashi

A Iran, Steven ya shafe wani lokaci a Tehran a matsayin baƙon shah, Naser al-Din.

A wajen birnin Tehran, ya tsaya domin ganin kyawawan wurare har da Zoroastrian tower - wani wurin mai tarihi inda ake barin gawawwakin mutane don tsuntsaye su cinye, saboda an ce binnesu zai gurɓata ƙasa.

Ya bayyana cewa an daɗe da kashe wutar Zoroaster, kuma wurin ya kasance a matsayin wurin tarihi na addini.

Bayan Iran, Steven ya zarce zuwa Afghanistan. Sai dai ya kasa shiga ƙasar, don haka ya tsallake tekun Capsian da kwale-kwale zuwa Baku - wanda a yau ya zama babban birnin Azerbaijan - daga can ya wuce zuwa Batumi da ake kira Gerogia a yanzu ta hanyar amfani da jirgin ƙasa.

Sannan ya isa birnin Calcutta na Indiya a jirgin ruwa.

A Indiya, rubuce-rubucensa sun yaba wa wurin tarihi na Taj Mahal mai tarihin gaske. Duk da cewa ya yi ƙorafi a kan zafi, ya bayyana cewa wurin shi ne ya fi so a cikin wurare da ya ziyarta yayin balaguronsa. Daga can ya nausa zuwa Hong Kong sannan ya isa China. Wuri na ƙarshe da ya ƙarƙare tafiyarsa shi ne birnin Yokohama a Japan.

A can Steven ya haɗu da ƙauyawa waɗanda ya kwatanta a matsayin "masu annashuwa". Ya rubuta cewa, "Suna da haɗin kai don shawo kan matsalolinsu domin zama lafiya fiye da kowace ƙasa." Ya kuma yaba da yadda yara a can ke son neman ilimi.

A nan ne ya kammala tafiyarsa a shekara ta 1886, wadda ya shafe shekara biyu da watanni takwas.

A lissafinsa, ya ce ya yi tafiyar kilomita 22,000 da kekensa, inda ya zama mutum na farko da ya zagaya duniya da keke. Ya fara wallafa labari kan tafiyarsa a wata mujalla, sannan a matsayin littafi a 1887.

An yi ta nuna buƙatar son littatafansa a faɗin Ingila da Amurka, bayan kasancewa mutum na farko da ya zagaya duniya kan keke. Labaransa a cewar masana, ya sauya yadda Amurkawa da dama ke kallon sauran duniya a wanan lokaci.

Rayuwar Steven ta zama abin koyi ga matasan Amurka da ke son yawon buɗe ido Willian Sachtleben da Thomas Allen, waɗanda su ma suka yi tafiya zuwa Istanbul a kan keke.