Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Amurka da China sun dakatar da harajin da suka lafta wa juna
Amurka da China sun tsawaita wa'adin sasanta dambarwar kasuwancin da ke tsakaninsu har zuwa ranar 10 ga watan Nuwamba, 2025, bayan da 'yan sa'o'i ya rage kafin karin harajin da suka lafta wa junansu ya fara aiki.
A wata sanarwa ta hadin gwiwa da suka fitar, kasashen biyu da suka fi karfin tattalin arziki a duniya sun ce harajin da suka ninninka a kan hajojin da suke shigarwa kasashen juna da suka sanar a farkon shekaran nan, a yanzu sun dakatar da karin kwana 90.
A tattaunawar da manyan kasashen biyu suka yi a watan da ya gabata dukkaninsu sun kira zaman da cewa ya yi fa'ida.
Babban mai shiga tsakani na China a lokacin ya ce kasashen biyu za su yi kokarin ganin sasanton ya dore, yayin da jami'an Amurka a lokacin suka ce suna jiran matsaya ta karshe daga Shugaba Donald Trump.
Sai kuma kwatsam a ranar Litinin Shugaban na Amurka ya sanya hannu kan wata doka ta tsawaita wa'adin sasanton harajin.
Wannan na nufin Amurka za ta kara jinkirta harajin kashi 145 cikin dari da ta lafta wa kayan China, ita ma kuma China za ta jinkirta nata karin harajin da ta yi wa kayan Amurkar na kashi 125 cikin dari.
A karkashin yarjejeniyar Amurka za ta tsayar da harajin da ta sanya wa hajojin da China ke shigarwa kasarta a kan kashi 30 cikin dari yayin da China za ta ci gaba da kashi 10 cikin dari da ta sanya wa kayan Amurka da ake shigar mata.
Tsawaita wa'adin sasanton a tsakaninsu zai bayar da damar karin tattaunawa domin lalubo bakin zaren magance bambance-bambancen kasuwancin da babakeren da gwamnatin Amurka ke zargin China na yi mata a harkokin kasuwancin da ke tsakaninsu.
Amurkar ta bayar da misalin gibin kasuwanci na kusan dala biliyan 300 a tsakaninta da China a shekarar da ta wuce – 2024 – wanda wannan shi ne gibi mafi girma a tsakaninta da duk wata kasa abokiyar kasuwancinta.
Sanarwar ta hadin gwiwa da manyan kasashen biyu suka fitar ta kuma ce tattaunawar da za su ci gaba da yi za ta yi kokarin ganin Amurka ta samu damar shigar da karin hajojinta China tare da magance batutuwan tattalin arziki da na tsaron kasa da Amurkar ke nuna damuwa a kansu a alakarta da China.
Mai magana da yawun ofishin jakadancin China a Washington ya ce hanyar da ta fi dacewa a tsakanin China da Amurka – ita ce ta cudan-ni-in-cude-ka, danniya da barazana ba wani alfanu da za su haifar.
Da kasashen biyu sun ci gaba da batun lafta wa junansu harajin da lamarin ya kara ta'azzara harkokin kasuwanci da haifar da rashin tabbas a fannin kasuwancin kan yadda zai iya tayar da farashi sosai da kuma illa ga tattalin arziki.
Dambarwar kasuwanci tsakanin Amurka da China ta kai kololuwa a watan Afirilu, bayan da Shugaba Trump ya sanar da karin haraji a kan kayayyakin da kasashe ke shigarwa Amurka, inda ya fi lafta wa China a kan wasu kayayyakin.
Lamarin da ya sa ita ma China ta zaburo domin rama wa kura aniyarta – ita ma ta lafta wa Amurkar haraji, abin da kusan ya janyo dakatar da kasuwanci a tsakanin kasashen biyu.