Henry ya yi ritaya daga kocin Faransa ƴan kasa da shekara 21

Therry Henry

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 1

Thierry Henry ya ajiye aikin horar da tawagar Faransa ta matasa ƴan kasa da shekara 21, bayan lashe lambar azurfa a Olympic a birnin Paris a bana.

Tun farko mai shekara 47 ya amince da ƙunshin yarjejeniyar kaka biyu tun daga 2023.

Henry ya ja ragamar kasar ta matasa ƴan kasa da shekara 23, inda suka yi na biyu, bayan da Sifaniya ta yi nasara da cin 5-3 a wasan karshe a Olympic.

Sai bayan gasar cin kofin nahiyar Turai ta matasa ƴan kasa da shekara 21 ya kamata yarjejeniyar Henry za ta kare.

To sai dai tsohon ɗan wasan Arsenal da Barcelona ya amince ya ajiye aikin, wanda ke sharhi da bayanan wasanni a talabijin.

Henry ya lashe wasa huɗu daga shida da ya ja ragama a matasa ƴan shekara 21, ya kuma ci karawa takwas daga 11 a tawagar da ta buga Olympic, wadda ta ƙunshi Alexandre Lacazette da Jean-Philippe Mateta, waɗanda shekaraunsu suka haura ka'ida.

Faransa ce ta ja ragamar rukuninta, bayan doke Amurka da Guinea da New Zealand, sannan ta yi nasara a kan Argentina da Masar daga baya Sifaniya ta lashe lambar yabo ta zinare.

Henry ya buga wa tawagar Faransa wasa 123 da cin ƙwallo 51 da lashe kofin duniya a lokacin da ya taka leda.