Halin da wani ɗan Senegal ya tsinci kansa a ƙoƙarin tafiya cirani tsuburin Canary

Mouhamed Oualy
    • Marubuci, Blanca Munoz, Chris Alcock & Mame Cheikh Mbaye
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, For BBC Africa Eye
  • Lokacin karatu: Minti 6

Wani manomin Senegal, Mouhamed Oualy bai taɓa tafiya ta teku ba amma zai yi wata tafiya mai tsarin gaske ta ruwa - tafiyar da ta mayar da tekun Atalantik makeken kabari.

"Matuƙa jirgin ruwan sun kira ni - sun ce na shirya. Ina neman ku yi mani addu'a - lokaci ya zo," in ji shi.

Sashen binciken ƙwaƙwaf na BBC ya samu wata dama ta ganin halin da ƴancirani ke ciki a yunƙurinsu na isa Turai ta hanyar mai haɗarin gaske da ke tsakanin yammacin Afirka da tsibiran Canary na Sifaniya.

Sannan Mista Oualy yana son zama ɗaya daga cikin ƴanciranin da za su isa tsibiran - da adadinsu ya kai ƙololuwa.

Gwamnatin yankin na gargaɗi cewa abin da ke jiran su a tsibiran wani tsari mai cike da ƙalubale amma babu abin da zai hana Mista Oualy tabbatar da ƙudirinsa.

Yadda ake cunkusa su cikin jirgin ruwa na katako maƙare da mutane bai tsorata Mista Oualy ba wanda yake iya shafe kwanaki ko ma makonni cikin tekun.

Daga Senegal, tafiya ce ta kusan tsakanin kilomita 1,000 da kilomita 2,000 a tekun - sai dai ya danganta daga inda ka taso, kusan nisan ninki 10 na sauran hanyoyin da ƴancirani ke bi wajen tsallaka wa tekun Mediteriya.

Ƴancirani lokuta da dama suna rasa ruwan sha yayin da suke shiga yanayin rashin lafiya da tsananin fargaba gami da fama da kaɗawar iska mai ƙarfi da rugugin igiyar ruwa.

A lokacin dare kuma, mutane sukan shiga ruɗani da kuma fargaba har ma da rasa ruwan jiki.

Migrants arriving by night on boats in El Hierro in the Canary Islands
Bayanan hoto, Adadin ƴanciranin da suka isa El Hierro tun farkon 2023 ya ninka yawan al'ummar tsibirin fiye da sau biyu
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A yankin Tambacounda da ke gabashin Senegal, ƴaƴan Mista Oualy da ƴanuwansa sun dogara ne kan ɗan kudin da yake samu daga noma.

Oualy ɗan shekara 40 ya shafe kusan shekara ɗaya bai ga iyalinsa ba bayan da ya koma kusa da ɗaya daga cikin cibiyoyin tafiya Turai.

A can yana aiki a matsayin direban babur na haya kuma yana karɓar bashi daga hannun abokai don tara dala 1,000 kuɗin ɗaya daga cikin jiragen da za su tafi tsibirin Canary.

Fargabar kar ya fada hannun ƴandamfara ya sa ya amince da masu safara cewa zai cika masu kuɗinsu ne kawai idan jirgin ya iya kai wa madakata.

"Babu wanda ya san abin da zai faru da ni a cikin ruwa. Ina iya rasa raina," kamar yadda ya faɗa wa BBC.

"Jirgin na iya kifewa, ya kashe kowa. Idan ka faɗa ruwa, me za ka riƙe don tsira? Mutuwa ce kawai abin da ka iya faruwa, amma dole ne ka ɗauki kasada."

Jiragen ruwa da dama sun ɓace da ɗaruruwan mutane. Idan Mista Oualy ya iya tsalle wannan tsiratsi, yana fatan samun aiki domin kula da danginsa, amma ya ɓoye tanadin da ya yi domin kada su shiga damuwa.

.
..

Yayin da Senegal ta samu tagomashi a tattalin arzikinta daga 2010, fiye da kashi ɗaya bisa uku na ƙasar har yanzu na fama da ƙangin talauci, a cewar bankin duniya.

"Babu aikin da ban yi ba, amma abubuwa ba su gyaru ba. Idan ba ka da kuɗi, ba ka da muhimmanci. Ni kaɗai ne wanda suke dogaro da shi kuma ba ni da kuɗi," in ji shi.

Kamar Mista Oualy, galibin ƴancirani da ke bin wannan hanya yan Afirka ne daga kudu da hamadar sahara da ke tserewa talauci da yaƙi da sauyin yanayi ke ƙara ta'zzarawa.

Tsibiran Canary sun zama manyan hanyoyin da ƴancirani ke bi a fatansu na tsallakawa Turai musamman bayan ƙasashe kamar Italiya da Girka sun bijiro da matakan toshe wasu hanyoyin na tsallaka tekun mediteriya daga Libya da Tunisiya.

Kusan mutum 40,000 sun isa 2023, adadi mafi yawa cikin shekara 30. Zuwa yanzu a wannan shekarar, tuni fiye da mutum 30,800 suka isa wuraren buɗe ido, fiye da ninki biyu na adadin da aka samu a bara.

Yayin da aka samu ingantuwar yanayi a Atalantika, gwamnatin tsibiran Canary na fargabar zuwan makoma mai muni.

Cikin wata hira da BBC Afirca Eye, Fernando Clavijo, shugaban gwamnatin tsibiran Canary, ya bayyana cewa masu aikin agajin gaggawa da masu ceto da ƴansanda da jami'an Red Cross na aikin da ya fi ƙarfinsu.

“Sakamakon shi ne ƙarin mutane za su mutu, ba za mu iya taimaka wa ƴancirani da taimakon da suke so ba," in ji Mista Clavijo.

A halin yanzu, Turai ta rufe tekun Mediteriya abin da ke nufin cewa hanyar atalantika da ta fi haɗari, ta zama hanyar tsira."

BBC ta yi magana da jami'an hukumar agajin gaggawa ta Sifaniya, da suka buƙaci a ɓoye sunansu, yayin da suke bayyana irin gajiyar da ke tattare da su.

A El Hierro, adadin ƴancirani da suka isa yankin tun 2023 tuni suka ƙaru fiye da ninki biyu na al'ummar tsibirin su kusan 30,000.

Mista Clavijo ya ce ƴan tsibirin ba sa amfani da motocin bas saboda ƴancira ni ne ke amfani da su, abin da yake fargabar ka iya rura matsalar wariyar launin fata da kuma janyo rashin kwanciyar hankali.

A watannin baya-bayan nan, ƙaruwar ƴancirani ya janyo zazzafar muhawara a Sifaniya game da yadda za a magance tafiye-tafiye ta ɓarauniyar hanya, inda gwamnatin Canary ke kiran a samar da ƙarin tallafi ga mutanen da ke zuwa tsibirin musamman yaran da ba sa tare da kowa.

A can Senegal, a ƙarshe masu safara sun yi sammacen Mista Oualy domin ya bi sauran ƴancirani a wata ɓoyayyiyar tafiya. A yanzu sune ke riƙe da ƙaddararsu.

"Muna da yawa, mun cika gidan. Akwai mutane daga Mali da Guinea. Suna ɗaukanmu a a ƙananan jirage na mutum 10 zuwa 15 har mu isa babban jirgi, sai mu tafi," in ji shi.

Mista Oualy ya tafi da robobin ruwa da kuma biskita da zai rika ci iya zangon tafiyar.

Ya kasance yana rashin lafiya a farkon kwanaki biyun tafiyar. Tsawon tafiyar, ya kan tashi tsaye saboda rashin wuri sannan kuma yana kwana cikin teku haɗe da mai.

Ya kuma fuskanci ƙarancin ruwa abin da ya sa shi dole shan ruwa daga teku.

Wasu mutane a cikin jirgin sun soma ihu tare da shiga ruɗani.

Bayanan bidiyo, Bidiyon kwale-kwalen da ke ɗauke da Mouhamed Oualy da sauran ƴancirani zagaye da manyan igiyoyin ruwan teku

Wata ƙididdiga daga hukumar kula da ƴangudunhijira ta Majalisar Ɗinkin Duniya, IOM, ta ce hanyar Atalantika na ƙara zama hanyar ci-rani mafi muni a duniya.

An ƙiyasta cewa mutum 807 ne suka mutu ko suka ɓace a 2024 - ƙarin kashi 76 cikin 100 na adadin da aka samu a irin wannan lokaci a bara.

Sai dai adadin na iya ƙaruwa saboda rashin bayar da rahoto kan haɗarurrukan da ke faruwa a kan hanyar wanda kuma ke ajalin mutane.

"A duk minti 45, ɗan cirani guda na mutuwa a kaƙarinsa na kai wa ga tsuburunmu. Hakan na nufin masu safarar na ƙara ƙarfi," in ji Mr Clavijo, inda yake nuni da alƙaluma da ga kungiyar kare hakkin bil'adama ta ƙasar Spaniya ta Walking Borders.

Ofishin Majalisar Ɗinkin Duniya kan ƙwaya da ayyukan laifi ya ƙiyasta cewa ɓatagari na samun kimanin dala miliyan 150 a kowace shekara daga wannan aiki.

Domin fahimtar yadda ƙungiyoyin masu safarar ke aiki, BBC ta tattauna da wani mai safarar ɗan ƙasar Senegal wanda ba ya son a amabci sunansa.

“Idan ka hau jirgin ruwa, wanda ke ɗauke da mutum 200 ko 300 sannan kowane mutum ya biya dala 500 ka ga kenan an samu kuɗaɗe da yawa," In ji shi.

Mista Oualy dai ya samu ya kai ga tsuburin Canary, amma ya samu raunuka da kuma matsalar lafiya a yayin tafiyar tasa.

Yana fama da matsananci ciwo a koyaushe sannan ba ya iya tafiya da sauri.

Bayan kwashe shekara guda ana tsara tafiyar, yanzu mista Oualy ya koma kamar bai yi tafiyar ba, inda ya koma ga iyalansa sannan yake ta faman tara kuɗi masu yawa domin sake wata tafiyar.

“Ina fatan sake komawa domin gwada sa'ata. E, zancen gaskiya wannan shi ne abin da ƙudurce. Ya fi min. Idan na mutu kuma to haka Allah ya ƙaddara."

Idan mista Oualy ya samu nasarar kai wa ga Turai, akwai yiwuwar sake yin idanu biyu da iyalansa. Idan kuma ya mutu a cikin teku, to ba shi babu sake yin tozali da iyalansa har abada.