Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda Kotun koli ta tabbatar da hukuncin kisa kan Maryam Sanda
Kotun kolin Najeriya ta kara jaddada hukuncin kisa da aka yanke wa Maryam Sanda wadda aka kama da laifin kisan mijinta a shekarar 2017.
A wani hukunci da alkalai biyar suka zartar, kotun, wadda ita ce mataki na karshe a harkar shari’a a Najeriya, ta ce hukuncin kisa ta hanyar rataya da aka yanke mata na nan daram.
Kotun ta yi watsi da duk wasu hujjoji da Maryam ta gabatar a kokarin ganin an soke hukuncin, sannan kotun ta yi watsi da daukaka karar bisa rashin cancanta.
A cikin kwaryar hukuncin da mai shari’a Moore Adumein ya karanta, kotun kolin ta ce masu gabatar da kara sun tabbatar karara, babu kokwanto kan cewa ta aikata laifin.
Daga nan sai kotun kolin ta ce matakin da kotun daukaka kara ta dauka na amincewa da hukuncin kotun farko ya yi daidai, kuma babu kuskure a cikin shi.
Haka nan kotun ta kara da cewa bai kamata shugaban Najeriya Bola Tinubu ya yi amfani da karfinsa wajen yafe wa wanda aka kama da laifin kisa ba duk da cewa an daukaka kara.
Matakan da aka bi a baya
A watan Oktoban 2025 fadar shugaban Najeriya ta fitar da jerin wadanda shugaba Bola Tinubu zai yi wa afuwa.
Daga cikin sunayen akwai Maryam Sanda, wadda kotu ta yanke wa hukuncin kisa a shekarar 2020 sanadiyyar daba wa mijinta wuka har ya mutu.
Matakin ya janyo zazzafar muhawara a shafukan sada zumunta, inda ‘yan Najeriya da dama suka soki lamirin matakin shugaban kasar na yi mata afuwa.
Lokacin da sukar ta yi yawa, fadar shugaban kasa ta ce an yi wa Maryam afuwa ne sanadiyyar nadama da kuma kyawawan halayen da ta nuna a gidan yari.
Sai dai ci gaba da muhawarar da aka yi a kasar ta sanya shugaban kasar ya yi amfani da karginsa wajen rage tsananin hukuncin da aka yanke mata, daga na kisa zuwa hukuncin daurin shekara 12, duk da cewa ta riga ta shafe shekara shida da wata takwas a gidan yarin garin Suleja.
A watan Nuwamban 2017 ne aka kama Maryam Sanda bayan ta kashe mijinta Bilyaminu Bello ta hanyar daba masa wuka.
Bilyaminu ya kasance da ne ga tsohon shugaban jam’iyyar PDP na Najeriya, Bello Halliru.
Bilyaminu Bello da Maryam Sanda sun kasance tare, inda suke da ‘ya guda daya, sai dai a shekarar 2017 ne wani sabani ya shiga tsakanin ma’auratan inda har lamarin ya kai ga kisa.
A watan Janairun 2020 ne wata babbar kotu a Abuja ta yanke wa Maryam Sanda hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan samun ta da laifin kashe mijin nata.
Mai shari’a Halliru Yusuf na babban kotun birnin tarayya ya bayyana cewa shaidun da aka gabatar sun tabbatar da cewa ita ce ta kashe mijin nata.
Mai shari’a Yusuf ya ce babu hukuncin da ya dace da wanda ya kashe mutum dan’uwansa face kisa.
Ya kara da cewa yadda ake samun matsalar mata na kashe mazajensu a kasar ta Najeriya, abin ya yi yawa, saboda haka ya kamata batun Maryam ya zamanto darasi.
Daga nan ne ya bayar da umarnin cewa a kulle Maryam a gidan kurkukun Suleja har sai ta kammala daukaka kara.