Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Sa ido kan sarrafa kuɗaɗen ƙananan hukumomi zai daƙile cin hanci da rashawa'
Ƙungiyoyin da ke rajin yaƙi da cin hanci da rashawa a Najeriya sun fara nuna goyan bayansu dangane da matakin da hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta ICPC na fara sanya idani kan yadda kanan hukumomi 774 da ake da su a kasar ke sarafa kudaden su.
Ƙungiyoyin rajin yaki da irinsu CISLAC mai inganta ayyukan majalisu da kuma yaƙi da cin hanci da rashawa, sun ce matakin da ICPC din ta dauka abu ne mai kyau sai dai akwai bukatar ta nuna ba sani ba sabo wajen gudanar da aikin nata, ba tare da nuna bambamcin ba.
Ƙungiyoyin da hukumar ta ICPC na bayana hakan ne yayin da gwamnatin Najeriya ke ƙoƙarin kammala shirye-shiryen fara damƙa kuɗaɗe kai tsaye ga ƙananan hukumomi ƙasar 774.
Awwal Musa Rafsanjani, shi ne Darakta a cibiyar CISLAC mai inganta ayyukan majalisu da kuma yaƙi da cin hanci da rashawa, ya ce 'mun yi maraba da matakin na hukumar ta ICPC, don tabbatar da tsaftace yadda ake kashe kudaden tafi da ƙanan hukumomin a Najeriya', in ji shi.
"Kowa ya san yadda aka yi badakala da kudaden kannan hukumomi, aikace aikace da ya kamata a yi a karkara, da bangarenn noma, da inganta tsaro a matakin ƙanan hukumomin ya hana kawo ci gaban da ya kamata, da samar da ci gaban da ya kamata".
Har ila yau Rafsanjanin ya ce matakin zai sa shugabanin ƙanan hukumomin su mayar da hankali wajen amfani da kudaden da aka basu, wajen aiwatar da ayyukan da suka kamata ba tare da an yi mun almundahana da dunkiyar al'umma ba.
"Za a yi tsarin gaske, musamman samar da adalci wajen tafi da ƙanan hukumomin, sannan zai jefa fargaba a zukanatansu na jin cewar idan har ka saci kudin ƙanan hukumomin, komai girman mukamin da ka ke rike da shi ko da shugaban ƙaramar hukuma ne, za a kamaka, tabbas za ai nasara" in ji Awwal Musa Rafsanjani
Rafsanjanin ya kuma nanata cewar "Sannan idan har aka yi yar gida aka ƙi hukunta shugabanin ƙanan hukumomin da suka futo daga jam'iyyar da ke mulki a jihar, idan sun yi badakalar suka sha, to anan za a fuskacin matsala, amma idan aka hukunta su, hakan zai yi tasiri wajen tabbatar da cewar babu sani babu sabo kann hakan", a cewar sa.
"Kowa ya san yadda aka yi badaƙala da kuɗaɗe ƙannan hukumomi, aikace aikace da ya kamata a yi a karkara, da bangarenn noma, da inganta tsaro a matakin kanan hukumomin ya hana kawo ci gaban da ya kamata, da samar da ci gaban da ya kamata" in ji Rafsanjanin.
Haka kuma Awwal Musa Rafsanjani ya kuma ce za su yi aiki tare da hukumar ta ICPC da su kansu kanan hukumomi, wajen magnace sace kudade a matakin kanan hukumomi a Najeriya tare da bayar da shawarwari d taimakaw kowace karmar hukumar sun yi abubuwan da zasu bunkasa ci gaban al'umma musamman samar da aikin yi a tskanin al'ummar yankin.
An shafe shekaru, ƙananan hukumomi na ƙarƙashin ikon gwamnonin jihohi ta fuskantar tafiyar da kuɗinsu - ta hanyar wani asusu da ake kira na haɗin gwaiwa tsakanin gwamnatin jiha da ƙananan hukumomi - da kuma wurin zaɓen sabbin shugabanni.
Tun 1976 bayan rahoton da Ibrahim Dasuki ya jagoranta, ƙananan hukumomi ya kamata a ce suna cin gashin kansu, da sakar masu mara ta fuskar kuɗaɗensu.
na ganin Kananan hukumomi su suka fi sanin buƙatun al'umma saboda kusancinsu – domin akwai buƙatun al'ummar ƙananan hukumomi da gwamnatin jiha ba za ta mayar da hankali akai ba.
Don haka a cewar Malam Kabiru Sufi, kananan hukumomi suna da damar ƙirƙiro abubuwan da suke ganin za su amfani al'umma.