Zanga-zanga a Najeriya: 'Har cikin gida suka yo harbi suka kashe ɗana'

Lokacin karatu: Minti 4

Iyalan matashi Isma'il Muhammad sun bayyana kisan da ake zargin sojoji da yi wa ɗansu da "ba zato ba tsammani" yayin zanga-zanga kan tsadar rayuwa a unguwar Samaru da ke garin Zariya na jihar Kaduna.

Ya zuwa safiyar Talata, lokacin da BBC ta tattauna da Muhammad Hussain - wanda shi ne mahaifin Isma'il - bai gama farfaɗowa daga kaɗuwar rasuwar ɗan nasa mai shekara 16 ba.

"Harbi na farko da (soja) ya yi, ya same shi a wuya, ya sake yin harbi na biyu ya same shi a baya, nan take Isma'il ya mutu," in ji mahaifin Isma'il.

Wannan ɗaya ne daga cikin labaran da ke fitowa na mutanen da suka rasa rayukansu a Najeriya tun bayan fara zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa da manufofin gwamnatin Shugaban Ƙasa Bola Tinubu.

Sai dai akasin sauran kashe-kashe da ake zargin jami'an tsaro da aikatawa a lokacin zanga-zangar, a wannan karo sojojin Najeriya sun ɗauki alhakin kisan, inda suka fitar da sanarwa suna bayyana takaici kan faruwar lamarin.

Tun bayan fara zanga-zangar a ranar 1 ga watan Agusta, lamarin ya rikiɗe zuwa tarzoma a jihohi da dama na arewacin ƙasar.

Wannan ne ma ya haifar da sanya dokar hana fita a jihohi bakwai; wato Borno, Kano, Yobe, Jigawa, Katsina, Filato, Kaduna.

A jihar Kaduna, an sanya dokar ce a babban birnin jihar da kuma Zariya, garin da aka bayyana cewa zanga-zangar ta so ta ƙazance.

Hotunan bidiyo da aka riƙa yadawa a intanet sun nuna yadda dandazon mutane suka mamaye tituna a garin na Zariya, yayin da wani bidiyon ya nuna wasu mutane na fasa wurin ajiye abinci, wanda aka ce a birnin na Zariya ne.

Sai dai a cewar mahaifin marigayi Isma'il, duk da zanga-zangar da ta wakana a Zariya har aka sanya dokar hana fita ta sa'a 24, babu wata tarzoma da ta tashi a unguwar Samaru.

Ya ce: "Babu wata zanga-zanga a Samaru, gaba ɗaya mu ba a samu zanga-zanga a Samaru ba tun bayan da aka fara wannan abu (zanga-zanga).

Wannan tsautsayi ya faɗa kan Isma'il ne a daidai lokacin da ya kammala karatunsa na ƙaramar sakandare, yana shirin zuwa aji ɗaya (SS I) na babbar makarantar sakandare.

A lokacin da yake bayyana halin ɗan nasa, Muhammad Hussain ya ce "yaron kirki ne, ba shi da hayaniya, ba a faɗa da shi kuma yana da saurin kuka".

Martanin sojoji

Wata sanarwa ɗauke da sa hannun mai magana da yawun shalkwatar sojojin ƙasa ta Najeriya, Manjo Janar Onyema Wachukwu, ta ce: "A ranar 6 ga watan Agustan 2024 jami'anta sun samu kiran gaggawa domin kai ɗauki sanadiyyar toshe hanya da ƙona tayoyi da kuma jifan jami'an tsaro da wasu gungun matasa ke yi a unguwar Samaru.

"Sanadiyyar haka ne jami'anta suka isa unguwar a ƙoƙarin tarwatsa masu zanga-zanga domin tabbatar da dokar hana fita da gwamnatin jihar ta kafa.

Sai dai a cewar sanarwar "lokacin da jami'an suka isa, gungun matasan sun yi yunƙurin far masu, lamarin da ya sanya ɗaya daga cikin jami'an sojin ya yi harbin gargadi, wanda a bisa kuskure ya yi sanadiyyar rasuwar wani matashi ɗan shekara 16 mai suna Isma'il Mohammed."

Sanarwar ta ce a yanzu haka ana tsare da jami'in sojan inda ake yi masa tambayoyi, sannan kuma babban hafsan sojin ƙasar, Taoreed Lagbaja, ya tura tawaga wadda ta ziyarci iyalan mamacin domin yi masu ta'aziyya.

'Sai an bi mana haƙƙinmu'

Muhammad Hussain ya tabbatar wa BBC cewa rundunar sojin ƙasar ta tuntuɓe shi, kuma ta buƙaci su shiga cikin binciken da za a yi kan kisan ɗansa ta hanyar bayar da shaida kan abin da ya faru.

Sai dai baya ga haka, ya ce zai tsaya kai da fata har sai an yi masa adalci game da kisan Isma'il.

"Gaskiya muna so mu ɗauki mataki, dole ne a bi mana haƙƙinmu...duk iyalinmu sun ce ba za mu yarda ba, za mu ɗauki mataki. Idan ya zama dole har kotu za mu je," in ji Hussain.

Kashe-kashe a Zariya

Zariya, ɗaya daga cikin birane masu daɗaɗɗen tarihi a ƙasar Hausa ba baƙo ba ne ga rikici da ya jiɓanci kashe-kashe tsakanin fararen hula da jami'an tsaro.

A watan Disamban 2015, an samu arangama tsakanin mabiya mazhabar shi'a, masu biyayya ga Sheikh Ibrahim Zakzaky da tawagar babban hafsan sojin ƙasa na wancan lokaci, Tukur Buratai.

A wannan lokacin an yi ƙiyasin cewa sama da mutum 100 ne suka rasa rayukansu sa'ilin da tawagar sojojin suka faɗa wa dandazon mabiya Sheikh Zakzaky da ke taro a cibiyarsu a cikin garin na Zariya.

Sai dai sojojin sun ce sun mayar da martani ne bayan wani yunƙuri na kashe babban hafsan sojin na Najeriya.