Abin da ya sa yawancin matan birni a India ke son zaman gida

Manisha, mai shekara 19 na aiki a matsayin ƴar aikin gida a wani gida da ke gefen Delhi, babban birnin Indiya.

Ta bar makaranta ne a garin su Jharkhand kasancewar hanyar zuwa makarantar ba ta da kyau, sannan ana yawan yunƙurin yi wa ɗalibai fyaɗe.

Ta yi hijira zuwa babban birnin Indiya, inda ta samu aiki a wani gida. To amma ko a yanzu mafi yawan lokaci ba ta zuwa ko ina saboda rashin kyawun hanyoyin sufuri da kuma rashin tsaro.

“Ina aiki, amma a wata bai fi na fita sau ɗaya ko sau biyu ba. Ina jin tsoron tafiya ni kaɗai a kan hanya.” In ji ta.

Labarin Manisha ba abin mamaki ba ne ga Rahul Goel, mataimakin farfesa a cibiyar bincike kan fasahar sufuri ta Delhi (IIT).

Ya yi amfani da alƙaluma daga wata ƙididdiga da aka yi, wadda ta yi nazari a kan lokacin da mutane kan kwashe suna gudanar da lamurran rayuwa – domin gano yadda rashin daidaiton jinsi ke tasiri kan yadda mutane ke zirga-zirga.

(A shekarar 2021, masu nazari sun bazu a faɗin India suna tattara bayanai kan yadda mutane suka tafiyar da lamurransu kwana guda kafin ranar da aka tattauna da su.)

Mr Goel ya mayar da hankali kan bayanan da aka tattaro daga mutum 170,000 waɗanda ke rayuwa a birane da garuruwa, waɗanda suna daga cikin waɗanda aka yi binciken a kansu.

Abubuwan da aka gano suna da ban mamaki.

A lokacin da masu tattara bayanai suka ziyarci gidaje, sama da rabin matan da aka tattauna da su (53%) sun ce ba su leƙa koda ƙofar gida ba a jiya.

Amma a ɓangare guda kashi 14% na maza ne kawai suka ce ba su fita daga gida ba a ranar da ta gabata.

Binciken ya kuma gano cewa yara maza sun fi ƴan uwansu mata yiwuwar fita a lokacin da suke tsakanin shekara 10 zuwa 19, sannan akwai ƙarin yiwuwar fita tsakanin mata a lokacin da shekarunsu suka tasa.

Mr Goel ya ce yana da yaƙinin cewar al’adar nan da ke hana mata fita ko zuwa aiki a waje, na farawa ne tun yara suna ƙanana.

Binciken ya bayyana gagarumin banbancin da ake da shi tsakanin jinsi. Mata ne ke yin akasarin ayyukan gida, waɗanda ba sai an biya su ba, yayin da maza kuma ke ayyuka a waje.

Mata daga shekara 25 zuwa 44 na kwashe kimanin awa takwas suna gudanar da aikin gida da kula da yara. Yayin da maza da ke tsakanin waɗannan shekarun kan kwashe ƙasa da awa ɗaya suna gudanar da irin waɗannan ayyukan.

Kahsi 38% na mata da ke tsakanin waɗannan shekaru ne kawai suka ce sukan fita waje domin yin aiki, yayin da kashi 88% na maza ne a tsakankanin waɗanna shekaru suke gudanar da ayyukansu a waje.

Binciken ya kuma gano cewa zaman aure na daga cikin abubuwan da ke ƙara dankwafe mata a cikin gida, yayin da su kuma maza auren ne ke ingiza su fita waje domin yin aiki. Haka nan kuma matan da suka yi aure ko kuma suka haihu sun fi zama a gida fiye da suara, sai dai aure ko haihuwa ba ya tasiri wajen rage yawan yadda maza ke fita waje.

Mr Geol ya ce “waɗannan bayanai da aka gano sun yi daidai da ake samun banbanci kan yadda maza da mata ke gudanar da ayyukan gida.”

A lokacin da suka kai lokacin da za su iya yin aiki, maza da yawa ne kan fita domin samun ayyukan daban-daban fiye da mata.

Yayin da yara suka kai shekara 15, da yawan yara maza kan bar karatu su koma aiki, yayin da mata ƙalilan ne kan yi irin haka.

Kashi 30% ne kacal na mata waɗanda ba su yin aiki a waje suka ce sun fita koda sau ɗaya ne, idan aka kwatanta da kashi 81% na mata waɗanda ke yin aiki ko suke yin karatu.

“Ba wai kawai mata ba su fita domin neman aiki ba ne kawai, yawancin su ba su fita daga gidan kwat-kwata,: in ji Mr Geol.

Wasu daga cikin bayanan da aka tattaro sun bai wa masana mamaki.

Ashwini Deshpande, farfesa a ɓangaren tattalin arziƙi a jami’ar Ashoka, ta ce an samu gagarumin haɓɓaka na yawan yara mata da ke shiga manya da ƙananan makarantu a Indiya, kuma bayanai na nuna cewa suna halartar makaranta sosai.

Hakan na nufin mata na yawan fita, kuma al’ada ba ta dankwafe su a gida ba. “Tabbas matan India ba su zauna jagwaba dakunansu ba, kuma ba a tursasa masu zama a gida ba,” in ji ta.

Farfesa Deshpande na da yaƙinin cewa da alama Indiyawa na fassara batun zirga-zirga bisa fahimta daban-daban, dangane da yarukansu.

Ta ce “a misali zan iya bayyana tafiya zuwa makaranta a matsayin zirga0zirga.”

Haka nan wasu da dama na ganin cewa rashin zirga-zirga ba shi ne ke nufin rashin aikin yi ko kuma ƙuƙumi irin na al’ada ba.

Misali, mata kan saki jiki suna zirga-zirga sosai a kan titunan birnin Pune, inda kuma akwai ruwaito cewa akwai ƙarancin mata masu aiki.

Mr Gole ya ce tabbas akwai banbance-banbance dangane da yankuna daban-daban – akwai mata da dama da ke fita waje a wasu jihohin da dama.

Misali, jihar Goa ce “kaɗai inda ake samun daidaito tsakanin maza da mata dangane da yadda suke zirga-zirga.”

Mat na fita sosai a Tamil Nadu, inda kashi 43% na matan Indiya miliyan 1.6 da ke aiki suke zama, kamar yadda binciken ya nuna.

Ana samun ƙarin mata da ke fita a jihohin Bihar da West Bengal bayan ɓullo da wani shirin gwamnati wanda ke samar masu da kekuna kyauta.

A 2007, bayanin wani bincike a kasashe 15 na Turai ya gano cewa mata sun fi maza fita waje a dukkanin ƙasahen in ban da ƙasa ɗaya 9Lituania).

A London an gano cewa babu banbanci tsakanin mata da maza ta fannin fita, yayin da a Faransa kuma mata sun fi maza fita.

Wani binciken da aka yi a birane 18 na duniya, a yankin Australia da Turai, da Latin America, da ƙasashen Afikr na kudu da hamadar sahara, da kuma ƙasashen arewacin Amurka ya gano cewa kimanin kashi 76% na mata suna fita, idan aka kwatanta da maza kashi 79%.

Hakan na nufin cewa gagarumin banbancin kan fita da ake samu tsakanin maza da mata a Indiya wani yanayi ne da a cika ganin irin shi ba a wasu ɓangarori na duniya,” in ji Mr Geol.

A wani mataki kuwa abubuwan da aka gano ba su zamo masu bayar da mamaki ba.

Akwai gagarumin giɓi ta fannin daidaiton jinsi a Indiya: yawan mata da ke aiki a Indiya na daga cikin mafi ƙaranta a duniya (27%), sannan kuma al’ada tana taƙaita yadda mata suke yin zirga-zirga.

Mafi yawanci ana keɓe mata ba tare da sun yi hulɗa da mutane da dama ba, hakan na hana su cakuɗuwa da sauran mutane ta yadda za su samu gogewar da za su soki matsalar rashin daidaito.

A lokaci ɗaya kuma an samu raguwar mace-macen mata masu ciki, yawan haihuwa ya ragu, sannan sanya yara mata a makaranta ya ƙaru sosai.

Mr Goel ya ce babban ƙalubalen shi ne yadda za a samu mata su fito daga gida. Ɗaya daga cikin ƙalubalen shi ne mata ba su samun sakin jikin yin tafiya a kan hanya, kamar yadda yake faruwa ga yara da tsofaffi.

“Maza ne suka mamaye wuraren hada-hadar al’umma. Ya kamata mu mayar da su yadda mata za su saki jiki,” in ji Mr Goel.

Kusan kowa ya aminta da hakan.