Iyalai dubu dari sun koma kwanan otel saboda ƙarancin muhalli a Ingila

- Marubuci, Michael Buchanan and Judith Burns
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
Adadin mutanen da ke zaune a matsugunai ko gidaje waɗanda ba na dindindin ba a Ingila sun yi ƙaruwar da ba a taɓa gani ba cikin shekara 25, a cewar alƙaluman hukumomi na baya-bayan nan.
Iyalai kusan dubu dari da biyar ne ke zaune a gidajen na wucin-gadi, cikinsu har da yara fiye da dubu radi da talatin da daya zuwa ranar 31 ga watan Maris na wannan shekarar.
Wannan adadi ya ƙaru da kashi 10 cikin 100 idan aka kwatanta da irin wannan rana a shekarar da ta gabata, kamar yadda alƙaluma daga Sashen Kula da Matsuguni da Al'umma suka nuna.
A Plymouth, wani mutum ya faɗa wa BBC irin mawuyacin halin da suke ciki yayin da suke zaune a otel.
Wannan adadi ya zarta mafi yawa da aka samu a baya na 101,300 a 2004, kuma shi ne mafi yawa tun daga lokacin da aka fara adana alƙaluman a 1998.
Kazalika, adadin ya nuna akwai iyalai kusan 14,000 da ke zaune a otel-otel daga wata kafin Maris.
Tsarin ya 'lalace'
Zaune a ƙofar wani otel da ke Plymouth, mun ga marasa muhalli da yawa a farkon watan nan suna hira da juna.
Chantelle Walton ce ta fi kowa hada-hada, inda take zaune tare da 'ya'yanta biyu.
Jack wnada aka haifa mako biyar da suka wuce, bai san ko'ina ba sai ɗakin otel da yake zaune tare da iyayensa da kuma 'yar uwarsa, Lily, mai wata 17 da haihuwa.

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Chantelle ta ce an fitar da su daga gidansu ne bayan an kai musu takardar wa'adin tashi bisa sashe na 21 na doka.
"Abu ne mai wuyar gaske," a cewar mai shekara 21 ɗin. "Sai ya tashi yana neman roba kuma ya farkar da ita, ita kuma sai ta zaci safiya ce ta yi kuma ta miƙe."
Akwai wani ƙaramin firji a ɗakinsu da kuma na'urar ɗumama abinci, "saboda mu dinga tsaftace mazubin ruwansa". Ƙarancin kayan girki a ɗakin nasu na nufin dole sai dai su sayi abinci a waje.
Duk da cewa saurayinta na da cikakken aikin yi a matsayin injiniya, ƙarancin shekarunsu na ba su matsala, in ji Chantelle.
"Saboda ba mu da shekaru da yawa, babu wanda zai ba mu aiki sai an samu wanda zai tsaya mana, mu kuma ba mu da wanda zai tsayama mana."
Akwai iyalai fiye da 200 da ke zaune a otel da kuma ɗakunan kwana a yankin Plymouth, kuma gwamnatin ƙaramar hukumar ta yi ƙiyasin cewa za ta kashe fan miliyan 6.8 wajen tallafa musu a shekarar nan.
Kuɗin ya ninka sau 10 na abin da aka kashe a shekara biyar da suka wuce.
"An lalata tsarin gaba ɗaya," in ji Chris Penberthy, wani jami'in hukumar samar da gidaje.
"Ba mu da tsarin mallakar guidaje mai sauƙi ga mutanen da ke buƙata. Saboda haka mutanen da ke kan layi sun ƙaru daga 8,000 zuwa 12,500 cikin shekara uku.
"Hakan na nufin idan jama'a na zaune a matsugunan wucin-gadi, ba su da inda za su koma, kuma ke nan ko a ɗakunan kwanan babu wuri."
Tsadar kuɗin haya
Haka nan, alƙaluman sun nuna hauhawar adadin marasa matsugunin a tsakanin dattijai, inda aka samu ƙarin kashi 33 cikin 100 cikin tsofaffin da ke da rauni.
Masu fafutika na cewa ƙarancin gidajen ne babbar matsala, wadda ta ƙara tsananin sakamakon matakin ministoci na dakatar da asusun samar da gidaje cikin shekara uku da suka wuce.
Yayin da ake fama da hauhawar kuɗin haya, matakin ya sa mutane da yawa da ke neman tallafi kafin su kama haya sun kasa samun matsugunin.
A wasu wuraren da yawa kuma, masu gidajen hayar na barin sana'ar.
'Saka iyalai cikin tsaka mai wuya'
Ƙungiyar Sheltar na ganin rashin daidaito a harkar haya ce babbar matasala wajen kasa samun matsuguni.
Ƙungiyar na bai wa ministoci shawarar ci gaba da matsa lamba wajen tabbatar da kafuwar dokar Renters (Reform) Bill, wadda za ta haramta tashin ɗan haya ba tare da ya yi wani laifi ba (no-fault eviction).
"Dole ne a saka shi cikin doka da zarar an samu dama," a cewar shugaban ƙungiyar, Polly Neate.
Wani jami'in gwamnati ya ce sun "ba da fan biliyan biyu cikin shekara uku don taimaka wa ƙananan hukumomi wajen shawo kan matsalar rashin matsuguni da kuma barci a kan titi, musammana a inda aka fi buƙata".
"Kuma gwamnati na ƙara ƙoƙarin samar da gidaje," a cewar jami'in.
"Mun himmatu wajen samar da sabbin gidaje 300,000 duk shekara kuma mun zuba biliyan 11.5 don gina gidajen da ƙasar nan ke buƙata."











