Yadda ake gaya wa ƙudan zumar da Sarauniya ke kiwo batun rasuwarta

By Fernando Duarte, BBC World Service

Rasuwar Sarauniya Elizabeth ta biyu da kuma hawa Gadon Sarautar da danta, Sarki Charles na uku ya yi, sun jaddada a karon farko cikin shekaru masu yawa irin gagarumin bikin da 'yan Gidan Sarauntar ke yi.

To amma wasu daga cikin al'adu da tufafin bikin na iya bai wa hatta wadanda ke tunkahon cewa sun san harkokin Gidan Sarautar mamaki.

Ga misalin wasu daga cikin abubuwa na daban na lokacin hada-hadar.

Gaya wa kudajen zuma labarin rasuwar

(Sakon Twitter daga ainahin shafin iyalan Gidan Sarautar na nuna hoton kudan zuma a Fadar Buckingham Palace)

Duk da yadda aka baza labarin rasuwar Sarauniyar ta kafofi da dama, dole ne a gaya wa wasu ɗaiɗaiku labarin rasuwar ta ta gaba da gaba: kudan zumar da take kiwo na daga cikinsu.

John Chapple shi ne mai kula da gidajen kudan zumar tsawon shekara 15.

Ya sanar da kudajen zumar da ke Fadar Buckinham Palace da kuma wadanda suke a gidan Yarima Charles wato Clarence House, labarin rasuwar.

A tattaunawarsa da jaridar Daily Mail, Chapple ya bayyana cewa ya kuma gaya wa kudajen zumar da su kasance masu biyayya da ɗa'a ga sabon sarki.

Al'ada ce da ake yi ta sanar da su sauyin da aka samu, da cewa idan ba a yi ta ba to kudan zai iya daina yin zuma.

Ya ce za a kwankwasa kejin kowane gidan kudan ta gaya musu cewa ''shugaba ta mutu, amma kada ku tafi. Shugabanku zai rike ku da kyau.''

Shi ma sarkin za a rika yi masa bikin ranar haihuwa biyu?

Daga cikin hukunce-hukunce masu yawa da Sarki Charles zai yanke shawara a kai a game da bukukuwan Fadar, wani daga cikinsu shi ne na bikin tunawa da ranar haihuwarsa.

An san Sarauniya Elizabeth ta biyu da yin bikin tunawa da ranr haihuwarta guda biyu.

An haife ta ne a ranar 21 ga watan Afrilu, amma an santa da yin bikin tunawa da haihuwar a hukumance a duk ranar Asabar ta biyu a watan Yuni, inda ake yin gagarumin biki da ake kira 'Trooping the Colour'.

Ko me ya sa take yin haka? Dalili shi ne, watan Afrilu a Birtaniya lokaci ne da ake tsananin sanyi saboda haka ba zai dace ba da biki, yayin da shi kuma watan Yuni lokaci ne da bazara ke somawa.

An daɗe da wannan al'ada wadda Sarki George na biyu ya fara a 1748.

Ba a dai sani ba zuwa yanzu ko Sarki Charles zai ci gaba da wannan al'ada.

An dai san cewa an haifi sarkin ne a watan Nuwamba, wanda wata ne da ba lalle ake samun hasken rana da dumi ba a lokacinsa.

Masanin tarihin Gidan Sarautar, Richard Fitzwilliams, ya gaya wa BBC cewa, ba ya jin Sarkin zai sauya wannan al'ada, musamman ganin yadda wannan biki da ake yi a lokacin bazarar yana da farin jini sosai a wurin jama'a.

Sai dai kuma wani abu da masanin ya kara a kai shi ne cewa yanayi a Birtaniya ba bu ne da yawanci za a iya hasashe a kai ba sosai. Abu ne da ba shi da tabbas.

Inda ya ce saraki ba za su iya sauya yanayi yadda suke so, inda ya bayar da misalin bikin nada Sarauniya Elizabeth ta biyu a watan Yuni na na 1953.

Karfin mutum ya danne na doki

Tun 1901, ana yin jana'izar Gidan Sarautar Birtaniya, inda sojojin ruwa ke amfani da igiya wajen jan akwatin gawar a tsanake a kan keken da ke dauke da bindiga mai makon dawaki su yi hakan.

Za a yi mamakin yadda aka zabi mutane su yi hakan maimakon dawaki, to amma haka al'ada ta gada tun 1901 a lokacin jana'izar sarauniya Victoria.

A wanan lokaci an saba dawaki ne ke jan akwatin gawar. To amma a wannan lokacin ana tsananin sanyi sai ya kasance dawakin sun bijire har kusan ma akwtin gawar Sarauniyar ta kusa faduwa, in ji masanin tarihin masarautar Kelly Swab.

Daga nan ne Sarki Edward na bakwai, wanda ya gaji Victoria, ya bayar da umarnin sojojin ruwa su rika yin wannan aiki.

A lokacin jana'izar Sarki George na shida a1952, - lokaci na karse da aka yi wannan jana'iza, sojojin ruwa 138 suka yi aikin jan akwatin gawar.

Al'adar karya sanda

Daga cikin abubuwan da ake yi a lokacin jana'izar, akwai abu ɗaya wanda mutane suka taɓa ji watakila.

A bisa al'ada mutum mafi matsayi a cikin ma'aikatn Gidan Sarautar wanda ake yi wa lakabi da Lord Chamberlain, wanda daga cikin aikinsa shi ne raka sarki ko sarauniya ziyarar da take kaiwa duk shekara majalisar dokoki, zai karya farar sandar girmansa a kan kabarin sarakin da ya mutu.

Zai yi hakan ne a matsayin alama ta kawo karshen aikinsa ga sarakin.

Mai rike da wannan mukami a yanzu shi ne Andrew Parker, tsohon shugaban hukumar leken asiri ta Birtaniya. Ya fara wannan aiki ne a watan Afrilu na 2021.

An fara wannan al'ada ne karni da dama a baya kuma lokaci na karshe da aka yi ta shi ne shekara 70 da ta gabata, lokacin da Earl na Clarendon ya karya sandar tasa a kan kabarin Sarki George na shida, wato mahaifin Sarauniya Elizabeth ta biyu.

Richard Fitzilliams ya ce ''masarautar Birtaniya tana da al'adu irin nata masu ban mamaki.''

''Wannan ne kuma ya sa masarautar ta kasance ta daban'' in ji shi.