'Sun kashe min ɗana' - Yadda iyaye ke jimamin yaran da suka mutu a ruftawar makarantar Jos

    • Marubuci, Chris Ewokor & Ifiokabasi Ettang
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Jos
  • Lokacin karatu: Minti 4

Wannan rubutun Chidera Onovo ne mai shekara 15 wanda ya rasu a rushewar ginin makaranta a birnin Jos.

Chidera dai yaro ne mai son zane-zane kuma ya kasance wanda mahaifiyarsa ta fi so a cikin ƴaƴanta.

"Ya ajiye kuɗinsa na abincin rana domin sayen biskit su raba da ƴan'uwansa," kamar yadda Blessing Onovo take tunawa. "Kuma shi ne wanda a koyaushe yake ganewa idan raina ya ɓaci sannan sai ya tambaye ni: Mama da fatan komai lafiya?."

Da safiyar Juma'ar da ta gabata ne Chidera ya tafi makarantar sakandare tare da ƙanwarsa Chisom, ashe dai ba zai koma gida ba.

Bayanai daga jami'an gwamnatin Najeriya na cewa ɗalibai 22 suka mutu a rugujewar ginin makarantar Saints Academy, wata makaranta mai zaman kanta da ke birnin na Jos, duk da mazauna yankin sun ce yawan waɗanda suka mutu ya kusa 50.

Iyayen yara dai sun ta yin ƙoƙarin ceton yaran nasu ta hanyar amfani da hannayensu da shebir wajen kawar da ɓaraguzan da suka danne su. "An kwashe kusan awa ɗaya kafin motar kwashe ƙasa ta zo," in ji mahaifin Chidera, Chike Michael Onovo.

"Na ga ana janyo ƴata Chisom daga ɓaraguzai. Sai hankalina ya kwanta, amma na ci gaba da magana da ƙarfi: Ina ɗana Chidera?

Daga baya an samu gawar Chidera, wadda ɓuraguzan kankare suka danne a ajinsu da ke bene hawa na farko.

'Yadda mutane suke ƙin bin dokar gine-gine'

Victor Dennis ma shekaru 43 na ɗaya daga cikin masu neman nasu ƴaƴan.

Abin da yake fargabar faruwa ya faru washe gari bayan yin ido biyu da gawar ɗansan Emmanuel a wata mutuware da ke yankin nasu.

"Ɗana na gari ne," ya shaida wa BBC. "Bai kamata ya mutu ba. Sun kashe min ɗana. Bai yi laifin komai ba. Kawai dai ya je makaranta ne domin ya koyi karatu."

Hawaye na zuba daga idanun mista Dennis waɗanda suka kaɗa suka yi ja zur a daidai lokacin da masu alhinin rashin da aka ke waƙen ban kwana ga gawar ɗan nasa. Sai dai kuma mahaifiyar Emmanuel wato mai ɗakin Dennis ba ta wurin sakamakon halin da take ciki tun bayan mutuwar saboda haka ne ta tsaya a gida.

Mutane a birnin Jos sun yi taimakekeniya a junansu, abin da ya sa aka samu damar ceto rayukan yara da dama ta hanyar bayar da jini a wata cibiyar bayar da jini da ke asibiti a yankin da abin ya faru.

To sai dai an nuna damuwa sosai kan yadda aka sake samun afkuwar rugujewar gini a Najeriya. Mazauna yankin sun yi iƙrarin cewa ɗaliban sun ji ginin yana rawa kwana ɗaya kafin faruwar al'amarin.

"An yi amfani da kayayyakin gini marasa inganci - hakan ka iya zama dalilin rugujewar ginin ," in ji wani mai sa ido kan inganci gine-gine, architect Olusegun Godwin Olukoya, wanda shi ne ke shugaban cibiyar ƙwararrun zayyanar gini a jiahr Plateau. "Bincikenmu na farko na nuna cewa akwai yiwuwar rashin bin ƙa'idar yin gini."

Ya kuma yi kakkausan suka ga masu gini da kuma hukumomi a Najeriya kamar yadda ya shaida wa BBC:

"Sai dai kuma sakamakon irin al'ummar da muke ciki da rashin mayar da hankalin hukumomi wajen yin amfani da shawarwarinmu ne su ka janyo a ka kasa daƙile faruwar rugujewar gine-gine.

"Mutane suna ƙin bin dokar gini kuma idan ka nemi ga fallasa, sai wasu su ji kamar kana ƙokarin ka uzzura musu ne. Suna amfani da mutanensu da ke muƙamai wajen ƙin bin ƙa'idojin gini."

Tun dai bayan rugujewar ginin makarantar ta Saints Academy, gwamnan jihar ya umarci gudanar da bincike kan gine-ginen dukkan makarantun gwamnati da masu zaman kansu a jihar ta Plateau.

Jami'ai na gwamnatin jihar sun ce ba a gano ko mamallakin makarantar wanda tuni dai ya riga ya rasu, yana da izinin gina makarantar ba.

BBC dai ba ta iya samun wani bayani daga hukumomin makarantar ba.

Wasu mutanen sun yi zargin cewa ayyukan hakar ma'adanai da ake yi a kusa da makarantar ne ya lalata ginin, saboda haka gwamna ya umarci da a kama duk wani mai aikin ma'adanan da ke yi ba bisa ƙa'ida ba a yankunan da gidaje suke.

To sai dai jami'an suna zargin cewa babbar matsalar ita ce yadda aka gina makarantar.

Shi ma ministan gidaje na Najeriya, Ahmed Ɗangiwa wanda ya yi kakkausan suka ga mutanen da ayyukansu ke janyo rugujewar gine-gine irin wanda ya faru a birnin na Jos wand akuma ya yi sanadiyyar rasa rayuka.

To sai dai wadancan kalaman na minista na sanyaya wa iyalan da suka rasa ƴaƴansu a ruftawar ginin makarantar kamar Chinecherem Joy Emeka mai shekaru 13 wadda tana ɗaya daga cikin mafi iya rawa a makarantar.

Chinecherem dai na da burin zama likita kamar yadda mahaifiyarta Blessing Nwabuchi ta faɗi.