Ana zargin Fifa da gaza biyan wasu kuɗaɗen 'yan wasa fan miliyan uku

Lokacin karatu: Minti 1

An zargi Fifa da gaza biyan ɓangare na ƙarshe na kuɗin wasu 'yan wasa da aka yi yarjejeniya da ita a faɗin Turai, wadanda ƙungiyoyinsu ba su mutunta yarjeniyoyinsu ba.

Majiyoyi daban-daban daga ƙasashen mabanbanta da suka san matsalar sun ce Hukumar ƙwallon ƙafar ta biya wasu kuɗaɗe da dama, amma ba ta biya ɓangare na ƙarshe ba na kuɗin.

Mafi yawan 'yan wasan da abin ya shafa ba su da abin yi ko kuma sun yi ritaya, wanda kuɗin zai yi musu amfani matuƙa a yanzu.

Za a biya kuɗin ne daga asusun kuɗaɗen 'yan wasan na Fifa, wanda aka kafa a 2020.

Kuma ya kamata Fifa ta biya waɗannan kuɗaɗe a watan Satumbar 2023.

An tura wa BBC wani saƙon email da wata ƙungiya ta tura wa Fifa, wanda aka rubuta sunan 'yan wasa sama da 30 da ke fama da matsalar kuɗi, kuma aka roƙi Fifa ta taimaka ta saki kuɗin.

Fan miliyan 3.09 ne aka riƙe na 'yan wasa ɗari huɗu da ashirin.

A yanzu haka Fifa na rikici da ƙungiyar manyan kwararrun 'yan wasan duniya kan yawan wasanni da ake samu su a mataki na ƙasashe.

Fifpro, wadda ke da goyon bayan ƙungiyar kwararrun 'yan wasa, ta yi amannar wasannin sun yi wa 'yan wasa yawa, wanda hakan ke jefa su cikin haɗarin jin raunuka.

Inda aka gaza samun daidaito shi ne faɗaɗa Club World Cup da aka yi zuwa ƙungiyoyi 32, wanda aka tsara farawa a baɗi a Amurka.