Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Da gaske ne tattalin arziƙin Najeriya na bunƙasa?
Arziƙin Najeriya ya ƙaru a tsakanin watan Yuli da kuma Satumba da kashi 3.46 cikin ɗari kamar yadda alƙamun hukumar ƙididdiga ta ƙasar, NBS, da aka fitar ranar Litinin suka nuna.
Alƙaluman sun nuna yadda arziƙin cikin gida na ƙasar ya bunƙasa a rubu'i na uku na gwamnatin Bola Tinubu.
To shin mene ne arziƙin cikin gida kuma me yake nufi ga tattalin arziƙin Najeriya?
Waɗannan ne za mu yi muku bayani a nan.
Mene ne arziƙin cikin gida (GDP) ?
Arziƙin cikin gida (GDP) na nufin dukkanin harkokin tattalin arziƙi na kamfanoni da gwamnati da ɗaiɗaikun jama'a na cikin ƙasa.
To hukumar ƙididdiga ta Najeriya, NBS, tana wallafa alƙaluman da ta samu bayan ta tattara bayanai kan waɗannan harkokin tattalin arziƙi a cikin wata uku-uku a shekara, ta fitar da sakamakon da alƙaluman suka nuna mata da abin da suke nufi.
Da wannan ne hukumar ta NBS ta fitar da bayanin cewa arziƙin Najeriyar ya bunƙasa a wannan lokaci da ta bayyana.
Yadda arziƙin ya kasance a tsakanin shekaru
Kamar dai yadda hukumar ta NBS ta ce arziƙin cikin gida na Najeriyar ya ƙaru a rubu'i na uku na wannan shekara ta 2024, wannan na nufin arziƙin ya zarta wanda aka samu a rubu'i na uku na bara, wanda a lokacin aka samu kashi 2.54 cikin ɗari ya kuma wuce wanda aka samu na rubu'i na biyu a wannan shekara ta 2024 inda aka samu 3.19.
Bayanan hukumar sun nuna cewa ɓangaren bankuna da harkokin sadarwa da fasaha da ayyukan lauyoyi da makamantansu ne suka fi haifar da ƙarin da aka samu - inda suka bunƙasa da kashi 5.19, wanda hakan ya tallafa wa arziƙin ƙasar ta wannan bunƙasa da ya yi da kashi 53.58 cikin ɗari.
To shi dai arziƙin cikin gida na Najeriyar ya kai na naira tiriliyan 20.12, wato ke nan ya ƙaru daga Naira tiriliyan 18.29 a rubu'i na biyu na wannan shekara ta 2024, ya kuma ƙaru daga Naira tiriliyan 19.44 a rubu'i na uku na 2023.
Ƙididdiga ta nuna cewa arziƙin na cikin gida ya kai naira tiriliyan71.13 a don haka wannan ya nuna an samu ƙaruwarsa da kashi 17.26 shekara bayan shekara.
Muhimman ɓangarorin da suka taimaka wa bunƙasar arziƙin
Ɓangaren harkokin noma ya bayar da kashi 26.51 cikin ɗari, sai kasuwanci ya samar da kashi 14.78 cikin ɗari da sadarwa, kashi 13.94 cikin ɗari, sai ɗanyen mai wanda ya bayar da kashi 5.57 cikin ɗari da kuma ɓangaren gidaje wanda ya bayar da kashi 5.43 cikin ɗari ta bunƙasar.
A ɓangaren manyan harkokin ayyukan noma sun bunƙasa da kashi 1.14 cikin ɗari, sai masana'antu da ya ƙaru da 2.18 cikin ɗari, sai harkokin bankuna da makamantansu waɗanda suka ƙaru da kashi 53.58 cikin ɗari, inda wannan ɓangare ke nan shi ya fi bunƙasa shekara bayan shekara.
Ɓangaren man fetur ya bunƙasa ne da kashi 5.17 inda ya bayar da kashi 5.57 ga bunƙasar arziƙin na cikin gida - kasancewar ƙasar na haƙar mai ganga miliyan 1.47 a kullum.
Shi kuwa ɓangaren da ba na mai ba ya bayar da gudummawar kashi 94.43, kuma harkokin noma da kasuwanci da sadarwa (waya da itanet da sauransu) da harkokin gidaje ne suka haifar da wannan bunƙasa.
Yawancin masana tattalin arziƙi da 'yansiyasa da masana harkokin kasuwanci suna son ganin bunƙasar arziƙin cikin gida.
A wajensu idan aka samu wannan bunƙasa, hakan na nufin kuɗin da mutane ke kashewa ya ƙaru - ana hada-hada sosai ke nan.
Idan kuma arziƙin na cikin gida ya yi ƙasa hakan na nuna cewa al'ummar ƙasa ba sa jin daɗi, harkokin kasuwanci ba sa gudana, ma'aikata da yawancin jama'a na cikin mawuyacin hali.
Idan alƙaluman arziƙin suka yi ƙasa a rubu'i biyu na shekara a jere to wannan ake cewa tattalin arziƙin ƙasa ya kama hanyar durƙushewa - wannan ne zai kai ga rasa aiki ko rage ma'aikata da sauran matsaloli na tattalin arziƙi.
Nawa kowa zai samu idan aka raba arziƙin?
Saboda kawai alƙaluman arziƙin cikin gida na ƙaruwa hakan ba yana nufin bunƙasar rayuwar jama'a ba.
Idan yawan al'ummar ƙasa na ƙaruwa, wannan zai sa yawan arziƙin ya ƙaru saboda yawan jama'ar da ake da zai sa a samu ƙaruwar kashe kuɗi.
To amma fa zai kuma iya kasancewa ɗaiɗaikun mutane a ƙasar ba sa samun ƙarin kuɗi idan aka yi ƙiyasi.
Idan aka kasa arziƙin da yawan mutanen ƙasar - mutanen za su iya kasancewa cikin talauci duk da cewa arziƙin na ƙaruwa.
Me ke faruwa ga tattalin arziƙin Najeriya?
Lauya kuma masaniya kan harkokin kuɗi a Najeriya, Adebisi Iyaniwura, ta gaya wa BBC cewa akwai shakku a kan sababbin alƙaluman bunƙasar arziƙin ƙasar da hukumar ta NBS ta fitar.
Ta ƙara da cewa ita ba ta farin ciki da abin da aka faɗa.
Masaniyar ta ce abu ne da yake a zahiri cewa tattalin arziƙin Najeriya na cikin mawuyacin hali.
Ta ce idan banda gwamnati da mutanen cikin gwamnatin ba wanda zai yarda da wannan magana ta cewa tattalin arziƙin na bunƙasa.
Iyaniwura ta ce gwamnati na buƙatar matakai na gasken-gaske kafin ta iya shawo kan matsalar tattalin arziƙin ƙassar.
Tsadar rayuwada hauhawar farashi sun ƙaru tun lokacin da Tinubu ya sanar da janye tallafin mai a shekarar da ta wuce.
Ƙwararriyar ta ce ɗaya daga cikin abubuwan da ya kamata gwamnati ta yi shi ne ta ƙara darajar kuɗin ƙasar - Naira - ta yadda ƙarfin kuɗin zai ƙaru - a fannin siyayya wanda hakan zai taimaka gaya a ga tasiri a hada-hada.
Mece ce makomar tattalin arziƙin Najeriya?
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bai wa 'yan ƙasar tabbacin cewa tattalin arziƙin Najeriyar zai bunƙasa, yayin da yake magana kan alƙaluman na hukumar ta NBS, da ke cewa arziƙin ya bunƙasa.
A wata sanarwa da aka fitar daga fadar mulkinsa, Tinubu, ya ce yana matuƙar farin ciki da alƙaluman bunƙasar tattalin arziƙin - na cigaban da ya samu a rubu'i na uku sama da yadda aka samu a rubu'i na baya har ma ya zarta yadda aka yi hasashe.
Ya ce duk da murna da ya yi ta samun wannan cigaba ya ce, alƙaluman sun nuna cewa suna da aiki sosai a gabansu.
Ya ce ba za su sarara ba har sai 'yan Najeriya sun samu sauƙin rayuwa da burunƙasar tattalin arziƙinsu.
To amma lauya kuma masaniyar harkokin kuɗi, Iyaniwura, ta ce ba ta tsammanin tattalin arziƙin Najeriyar zai kyautatu a watannin da ke tafe.
Hasali ma ta ce 2025 za ta kasance mafi tsanani a kan 2024.
Ta yi hasashen cewa darajar Naira za ta ƙara faɗuwa, tsadar rayuwa za ta ƙaru.
Masaniyar ta ce ana ƙara kuɗin harajin kayayyaki na VAT, ɓangaren masana'antu da bankuna da makamantansu na durƙushewa, saboda haka rashin aikin yi zai ƙaru.
Ta ce tafiyar da ƙasa a kan tsarin bayar da tallafi abu ne da ba zai raya tattalin arziƙi ba - ''akwai buƙatar gwamnati ta samar da kyakkyawan yanayi na wanzuwar harkokin tattalin arziƙi.'' In ji ta.