Real Madrid ta bayyana waɗanda za su buga mata Spanish Super Cup

Real Madrid

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 1

Real Madrid ta sanar da ƴan wasan da za su buga mata Spanish Super Cup na bana a birnin Jeddah a Saudi Arabia.

Ƙungiyar Santiago Bernabeu za ta fafata da Real Mallorca a zagayen daf da karshe a filin King Abdullah.

Real Madrid ta tashi 1-1 a gidan Mallorca a gasar La Liga a bana ranar 18 ga watan Agustan 2024.

Ranar Laraba 8 ga watan Janairu za a fara karawar daf da karshe tsakanin Athletic Club da Barcelona.

Daga nan kuma za a fafata tsakanin Real Madrid da Real Mallorca ranar Alhamis 9 ga watan Janairu.

Za a buga wasan karshe a gasar ranar Lahadi 12 ga watan Janairu.

Da zarar an kammala Spanish Super Cup, Real Madrid za ta karɓi bakuncin Las Palmers a La Liga ranar 19 ga watan Janairu.

Daga nan za ta kece raini da RB Salzburg a Champions League ranar Laraba 22 ga watan Janairu.

Ƴan wasan Real Madrid da za su buga Spanish Super Cup:

Masu tsare raga: Courtois, Lunin da kuma Fran González.

Masu tsare baya: Alaba, Lucas Vázquez, Fran García, Rüdiger, Mendy, Asencio, Lorenzo da kuma Diego Aguado.

Masu buga tsakiya: Bellingham, Camavinga, Valverde, Modrić, Tchouameni, Arda Güler da kuma Ceballos.

Masu cin ƙwallaye: Vini Jr, Mbappé, Rodrygo, Endrick, Brahim da kuma Yáñez.