Kun san miyagun makaman da China ta yi baje-koli a faretin Beijing?

Asalin hoton, Getty Images
Titunan birnin Beijing na China sun sauya yayin da Shugaban Ƙasa Xi Jinping ya jagoranci katafaren faretin soja, inda shugaannin ƙasashen dunya aƙalla 26 suka sha kallo.
Taron wanda aka shirya ranar Laraba domin murnar cika shekara 80 da nasarar da China ta yi a kan Japan yayin Yaƙin Duniya na Biyu, wata dama ce da ta yi amfani da ita wajen nuna wa duniya irin miyagun makamai kuma na zaman da ta mallaka.
Bayan gaishe da shugabannin duniya, ciki har da Putin na Rasha, da Kim Kim Jong Un na Koriya ta Arewa, Shugaba Xi ya gaishe da tsofaffin dakarun ƙasar kafin ya samu wurin zama.

Asalin hoton, AFP via Getty Images
Da yake jawabi, Shugaba Xi ya yi magana kan "nasarar daƙile harin Japan", inda ya gode wa shugabannin duniya da suka taimaka wa ƙasarsa. Sai dai bai ambaci Amurka ba wadda ta taimaka sosai wajen kawo ƙarshen yaƙin.
"Al'ummar China za ta ci gaba da kasancewa a ɓangaren mutanen kirki da neman cigaban ɗan'adam, da zaman lafiya, da kuma haɗa hannu da sauran ƙasashen duniya wajen gina al'umma mai makoma ɗaya," a cewarsa.
Mutum 50,000 ne suka zazzauna a kujeru domin gane wa idanunsu wannan ƙasaitaccen biki da aka gudanar a Chang'an Avenue da ke birnin na Beijing.
Ɗaya daga cikin abubuwan da suka fi jan hankalin masana harkokin soji shi ne irin tarin sababbi da kuma makaman da aka yi wa kwaskwarima, waɗanda suka dinga gilamawa ɗaya bayan ɗaya yayin faretin.
Makaman nukiliya masu linzami

Asalin hoton, Reuters
Robot wolves: Yana nufin "mutum-mutumin kerkeci" a Turance. Gungun mutum-mutumi ne masu ƙafa huɗu da aka ƙaddamar a wurin faretin, waɗanda ake iya amfani da su a filin yaƙi domin kai hari, ko kayan aiki, ko tattara bayanai, a cewar kafar yaɗa labarai ta gwamnatin China.

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A shekarar da ta gabata aka ƙaddamar da su da sunan "Robot Dogs" (mutum-mutumin karnuka), amma yanzu aka inganta su da kyamarori a jikinsu tare da sauya musu suna.
Dongfeng-5: Makami ne mai linzami mai cin dogon zango kuma ɗaya daga cikin mafiya girma da China ta gabatar, wanda ke da ƙarfin harba makamin nukiliya kuma zuwa dogon zango.
Ana iya harba makamin daga tashoshin da ke arewacin China waɗanda za ta iya kai wa Amurka hari da su, a cewar Alexander Neill wani masanin harkokin soji.
Yana cin dogon zangon da zai iya kaiwa baki ɗayan Amurka, da yammacin Turai, in ji cibiyar nazarin harkokin soji ta Center for Strategic and International Studies.
Dongfeng-61: Shi ma makami ne mai linzami da ka iya fita daga sararin samaniyar duniya ciki gudu irin na walƙiya kafin ya harba makamin da yake ɗauke da shi.
Ana iya harba shi daga kan babbar mota, abin da ya sa yake da sauri da kuma sauƙin sarrafawa. Haka nan, za a iya harba shi daga wurare da dama, wanda zai sa abokan gaba su kasa gane daga inda yake.
Dongfeng (DF)-26D: Wanda ake yi wa laƙabi da "Guam Killer", shi ma makami ne mai linzami amma mai cin matsakaicin zango. An ce zai iya ragargaza rukunin jiragen sama - ko kuma sansanin sojin sama na Amurka - a yankin Pacific.
An kira shi da Guam ne saboda sunan wani yanki ne da ke ɗauke da sansanonin sojin Amurka masu muhimmanci a Pacific, waɗanda za ta yi amfani da su idan yaƙi ya ɓarke tsakaninta da China.
AJX002: Shi kuma jirgin ƙarƙashin ruwa ne maras matuƙi da aka ƙaddamar. Yana da tsawon mita 20, kuma za a iya amfani da shi wajen kai harin bam na nukiliya.
Kazalika, za a iya amfani da shi wajen tattara bayanai yayin kai wa abokin gaba hari a cikin ruwa.
LY-1: Aikinsa shi ne katse layin intanet ko na tauraron ɗan'adam da wani makami ko jirgin yaƙi na abokin gaba ke amfani da shi. Ana goya shi ne kan babbar mota mai taya takwas.

Asalin hoton, Getty Images
Me ya sa makamai masu linzami?

Asalin hoton, Getty Images
Da ma tun kafin yanzu, China ce kan gaba a fasahar makamai masu linzami da ake kira missile a Turance. Sai Rasha da ke biye mata, da kuma a can baya. Akasarin ƙasashen Turai sai yanzu ne suke neman haɗa irin waɗannan makaman masu cin dogon zango.
Akasarin makaman da China ta gabatar a yanzu masu linzami ne, waɗanda ake harbawa daga nesa kuma ba tare da buƙatar wani jirgi ba - na sama ko na ruwa.
Daga cikinsu akwai waɗanda ka iya tsallaka nahiya guda kuma su kai harin nukiliya. Sai dai akwai babban dalili kan hakan.
China ta sha zuba kuɗaɗe a fannin makamai masu linzami ne saboda ta kare kanta wajen mayar da martani ga ƙwarewar sojin ruwan Amurka, a cewar Alexander Neil wani mai sharhi a cibiyar Pacific Forum.
Rundunar sojin ruwan Amurka ce mafi girma a dunya saboda yawan jiragen ruwa masu ɗauke da jiragen sama, yayin da China ke can baya.
Amma yanzu ana muhawara a ƙasashen Yamma kan ƙarfin da irin waɗannan jirage ke da su, da kuma rauninsu saboda yadda makami mai linzami zai iya ragargaza su lokaci guda yayin da suke zaune a cikin ruwa.
"An ce China na son kyautata tsaronta ta hanyar kariya, da kuma kyautata hanyoyin kai hari," a cewar Mista Neil.
"Wannan dalilin ya sa take faɗaɗa hanyoyin samar da makamai masu linzami."

Asalin hoton, Reuters

Asalin hoton, Reuters

Asalin hoton, Reuters
Sojoji masu fareti cikin burgewa

Asalin hoton, Getty Images

Asalin hoton, Getty Images

Asalin hoton, Getty Images










